Page 27
amaan nazuwa ya tarar da ahlam sun fito kenan ta tsaya tana tsokanar zainab, zainab ce tace"ahlam wallahi kifita aharkata ni bazanyi fada dake ba kiyi hakuri", ahlam tashekye da dariya sannan tace"ashe dai ni din boss ce", bata gama rufe baki,ba har amaan yakaraso yana"a'a nidai aunty tah jarumace ba boss,ba", ahlam tayi murmushi sannan tace"a'a fa kanina basawa sunfi jarume karfi", zainab suna tsaye suna kallon ikon allah, wai da gaske kanin ahlam ne wannan babban kuma kyakkyawa?, amaan yace"toh auntynah yanzu dai karki kara fada da kawarki ku shirya kunji". ahlam ta shagwabe fuska sannan tace"uhumm bayan itace take hantara tah wai mune talakawa", amaan yarike baki sannan yace"ah toh ke kuma karki kara kinji ko?' zainab tace"nida man mumyna tamin fada nadai na so nake ma tazama kawatah"', amaan yace"yauwa daga yau kun zama kawaye ba fada", ahlam tayi murmushi , zainab tace"kin yafemin ko", ahlam tace"eh", amaan yace"toh shikenan dai yanzu bara mutafi kema kije ga kannanki cen anzo daukan ku", ahlam da amaan suka nufi mota har amaan yashiga mota yazauna ya lura ahlam fa bata shigo,ba, ya fito yace"haba auntyna ya baki shiga ba? ahlam tayi kaman zatayi kuka tace"uhum bayan naga masu kudi bude ma auntynansu kwofa suke nikuma kaki budemin", amaan yayi murmushi yace"afwan ranki shidade na bude", ahlam tace"yauwa kanina allah yama albarka amaan ya kalleta azuciyarsa yace"masha allah", afili,kuma yace"amin aunty", ahlam ta rufe fuskarta dasauri amaan yace......