Page 28
WASHE GARI
Kamar yadda su Amaan basu da Aiki haka ma Ahlam basu da skul sai islamiyar yammah. Dassafe Maamah tuni fo gidan Hamlat Inda Ko tashi daga barci,Amaan bai yi ba. Tana zuwa,kamar munafuka ta shiga dakin Hamlat da hike kwofar abude take tun sallar asuba. Hamlat naganin Maamah Ta fara kuka. Maamah tace"haba kawata miye na kuka mufa mata ne munada hanyoyi da ban-da ban,dan haka share hawayenki kimin bayani". Hamlat ta share hawayen ta sannan tazauna tama Maamah bayanin duk abinda yafaru tsakanin ta da Amaan jiya. Maamah tayi murmushi mugunta azuciyar ta tace"ai kadan ma kika fara gani". afili kuma tace"aikin banza ni nazata ma cewa yayi zai sake ki,kar kiji kome yanzu akafara ,tunda dai kinsa moma gidan su yarinyar ai kome ya huce". Hamlat tayi"murmushin dole tace"yauwa kawata shiyasa nake alfahari dake". Maamah tace"umm yanzu dai naga alama ko,wanka ma baki yi ba je kiyi wanka kafin wancen matsiyacin ya fita sai muje muyi aika-aika". Hamlat tace"nikam ba sai nayi wani wanka ba shekaran jiya fa nayi zan shafa turare kawai". Maamah ta rike baki tace"haba dan ALLAH karki bani kunya mana tashi kiyi wanka aganmu zam-zam ba raini". Hamlat bata so ba haka ta tashi tashiga wanka. tana shiga wanka Maamah tafara mata bincike tadau abin dauka ta bar na bari domin,ita kanta kyamar Hamlat take dan dai tanason abin hannunta neh yasa take tare da ita. Hamlat batafi minti biyar ba ta fito duk wanda yaganta yasan jika-jika tayi. Maamah tace"nashige yanzu har kin gama wankan". Hamlat tace"hmm kema sanin kanki ne banason wahala arayuwata agidama dan mumy nake wanka wallahi yanzu ko sai naga daman yi". Maamah tace"ah kam naga alama turare na aiki,yanzu dai ba wannan ba jeki sa kaya mutafi". Hamlat tashirya cikin hanzari aka mulka turare ajiki waje yayi kyau amman ciki tsami. suna fita suka ga ba motar Amaan awaje Hamlat tayi,tsaki,tace"yanzu haka yatafi gun wa innan matsiyatan,iyayen nasa ne. Maamah tace"umm ba nan ba muyi abinda ke gabanmu". suka nufi gidan su Ahlam da Maaamah taga Hamlat ta tsaya kusa da wani dan gajeren gida,ai tuni ta tun tsire da dariya tana cewa"kar kice min nan ne gidan su kishiyar tamu". Hamlat tayi tsaki sannan tace"yo ehmana ai dai-dai su yanemo kamar yadda suke". Maamah ta bude baki zatayi magana sai ko hango Amaan ai tuni ta kame kam. Hamlat ma zatayi magana sai taga inda Maamah take kallo sai da tayi suman tsaye.