KUCHAKAR KISHIYA

Page 30

by @xayyeesherthulhumaerath

Ahlam tayi wata kara tana fadin"wayyo ALLAH kafata,wayyo babatah". gaba daya baba ta birkice takasa magana tana rikwo yarta. Hamlat da,Maamah kuwa me zasuyi banda dariya suna"ai wannan kadan ma kuka gani,indai dani kuku". Baba ta fara ihu tana fadin"DAN ALLAH jama'ah ku taimaka mana". Dasu Hamlat su ka ga anfara nufuwo wajen ai da sauri sukabar gun. Duk matasan layin suka nufo wajen inda wani mutumi yataimaki Baba yadau Ahlam yakai ta wani kemis da ke kusa dasu. Ahlam duk tabi ta fita ahaiyacinta ta ma rasa a ina take tun tana ihu har tayi shiru sai hawaye dake kwaranya daga idaniyan ta. Dakyar likitan yadan yi dara ya wanke mata kafar domin,abin ya chabe da yawa. kafin agama wankewa har Baba ya iso. Haka Baba yadau Ahlam suka koma gida Baba dai ta kasa magana domin ji take kamar abin ajikinta yake. Suna zuwa gida Baba ya kwantar da Ahlam a yar katifarsu, tukun yadawo kan Baba da takasa magana sai zubar hawaye yace"Haba kedai na kukan nan mana ya isa haka, yanzu ki fada min me yafaru,neh ya akayi haka". Baba ta numfasa sannan tace"wasu mata ne suka zo,su biyu suna ta fada mana bakyakyen maganganu tun ina kawar da kai har Ahlam ta fusata tafara magana, suna ta magana akan miji abinda yafi dauremin kai kenan domin ban gane mesuke nufi ba, ban kai ga tambaya,sumin bayani ba kawai naji,Ahlam dita na ihu suka kuma suka yi tafiyarsu". Baba ya numfasa yana fadin"INNALILLAHI-WA"INNA-ILLAIHIR-RAJI'UN wannan wace irin musiba ce me shirin afka mana da duk kan alamu matar Amaan ce". Baba ta rike baki tana fadin"dama yana da mata neh.?. Baba yayi murmushi,yana"eh yana da mata nazabi boye miki ne domin gudun halinku na mata". Baba tace"subhanallah gaskiya da matsala domin yariyar nan idonta abude yake zata iya kome". Baba yayi numfasa yace"kinga irin halin naku kenan , ita dama tayi hakan ne dan mutsorata muce A,a kuma mu ba kana nun mutane bane ai munsa me muke". Baba tacr"Hakane to yanzu dai fatan mu Allah ya bata lafiya". Bba yace"yauwa koke fa ALLAH dai ya miki,Albarka". Baba tayi murmushi tace"AMEEN AMEEN".

,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, Abangaren Hamlat kuwa gidan iyayenta ta huce domin tasan Amaan ma yana chan. tana zuwa ta nufi,shashin mumy sai murmushi take. Mumy na ganinta tace"ya akayine daughter naga kina murna muda muke cikin matsala". Hamlat ta shekye da,dariya sannan tace"yoo,ai munga da yar matsiyatan ". Mumy tayi shewar data fi ta Hamlat sannan tace"yoo yar nan bani nasha mana". Hamlat ta kwashe duk,abinda suka gani da wanda sukayi,ta fadawa Mumy. Bakaramin dadi,Mumy taji ba hakan,yasa sai shewa suke ita da yar ta ba mai wa wani,fada abin nema yasamu. Amaan,ya fito,daga bangaren Dady kenan yazo,zai geshe da Mumy yaji shewa hakan bai hanasa shiga ba domin yasan,inya tafi ma kansa yajawa wata sabuwar masifar. yana shiga suka kara kwashewa da dariya. Hamlat tayi masa wani irin kallo,sannan tace"ango kashe kamshi ",