KUCHAKAR KISHIYA

Page 31

by @xayyeesherthulhumaerath

Amaan ko kallon Hamlat bai yi ba yace"mumy ina kwana?. mumy ta masa wani mummunan kallo tana"na kwana agida na ko baka ga alamun hakan bane?. Amaan yayi shiru domin in bawai Dady na wajen ba yasan daman bakar magana ce zata hada sa da Mumy. Ya juya kenan zai fita mumy tace"dan matsiya ta ansamu waje to wallahi baki isa ka dauko ko yar waye ka hada ta da diyata ba bare yar matsiya ta irin ka, kaje chan suna jiranka dan nasan iyanzu sun shiga halin dana sani". Amaan najin Mumy ta fada haka gabansa ya fadi domin yasan da wata kullalliya. da sauri ya fita adakin su ko su Mumy suka cigaba da shewar su dan su aganin su sunyi nasara akan matsiyata. Amaan na fita ya nufi gidan su Ahlam tuki yake cikin hanzari domin ya riga yagama tsorata,da su,Mumy. Tunda yake bai taba shiga cikin gidan ba amman yau,afusace ya shige ciki. Aiko yana shiga ya hango Baba da Baaba sun zubawa Ahlam ido kallon ta kawai suke. Yana zuwa ya durkusa gaban su baba yana kuka cewa yake"Baba dan ALLAH karku,ce zaku rabani da Ahlam wallahi inason ta bazan iya rayuwa ba ita ba". Baba yayi murmushi ya rikwo Amaan na fadin"kar ka damu ai insha ALLAH Ahlam matar kace, baka ji ance matar mutum kabarinsa ba? to karka damu inda rai da rabo zaka auri Ahlam. sai alokacin Amaan yaji sanyi aransa . yace"toh Baaba ya jikin nata". Baaba tayi murmushi tace"jiki da sauki yanzu ta samu barci ne". Amaan yace"wani asibiti kuka kai ta?. Baba yace"oh ban da abinka ina zuwa wani asibiti ai kemis din dake anguwar,nan ma ya wadatar". Amaan yace"subhanallah kemis! ai Baba gaskiya ku tashi mu tafi asibiti domin ba awasa da maganar kuna". Baba zai yi magana Amaan ya katse sa da cewa"DAN ALLAH Baba". Haka suka tashi ba da niya ba aka nufi asibitin *OLA* Dake cikin garin jos. Suna zuwa aka bawa Ahlam gado domin acewar likitan bakaramin kwonewa tayi ba amman ga dukkan alamu tana da kyan jiki zai iya warkewa da wuri indai ka,kiyaye shi yarda yakamata. Sai da Amaan ya gama biyan kudin kome sannan yacewa su Baba bara yaje yadawo su Baba sai godiya suke. Amaan na fita ya nufi gidan Dady amman bai je bangarensa ba ya nufi bangaren babansa. yana zuwa ya geshesu sannan yasansar dasu duk abinda yafaru . basuyi mamakin jin hakan ba domin su kansu basu sha agun uwar ta ba bare shi mijin yarta. Alokacin Amrin ta tashi ta daura abinci da shike taliyace bata bata lokaci ba ta kammala. suka fita ita da Amaaan . Suna fita kenan sai ga Hamlat sun fito ita Mumy. Hamlat tana hango basket din kayan abinci . ta wage ido sannan tace"........