Page33
Sun isa dai-dai asibitin OLA dake cikin garin JOS suna zuwa Amaan ya bude mota ya fito Amrin ma ta bi yoshi abaya. Da har Hamlat ta fuske tana jiransu sai kawai wata zuciyar tace ta dai shiga taga ko su waye. Amaan nashiga yasamu Ahlam ta farka sai kuka take yayi saurin karasawa yanq"ayya Ahlam di ta kidai na kuka mana ai kin kusa warkewa ". Ahlam ko kallon sa bata yi ba bare kulasa. Amriin ta shigo ita sai da ta geda su baba sannan ta karasa wajen su Ahlam. Tana zuwa tace"ya jiki auntynah?. Ahlam ta kakulo murmushin dole tama Amrin. Amaan yace"Amriin zuba mata a......... bai karasa ba Hamlat ta ban kado kwofa. Dukan su sai da suka razana domin shi kan shi Amaan ya manta ma da ita suka zo. Tana shigowa ta nufin inda ta hango Amaaan Ta karewa Ahlam kallo sannan tace"Oh anyi asararrun matsiyata dai wato bara dai arabu dashi ba ko?. Amaan yace"wai miye haka ne Hamlat ke baki da hankali ne?. Hamlat tace"ai dole kayi tunanin banda hankali tunda anbaka kasha". Su baba dai sun tsaya kallon ikon Allah. Amaan yace"tunda abinda yakowo ki kenan to ki fita ya isa haka inba kinaso na batq miki rai ba". Hamlat tayi murmushi sannan tace"Yoo ai ko baka fada bq bazan iya zama cikin kazantar nan ba" . Ta fice abinta. Amaan yacewa su baba"Dan Allah kuyi hakuri zan dau mataki". Baba yayi murmushi yace"bakome Amaan ai banga laifinta ba kishi ne yaja hakan nidai fatana kana hakuri kar kadau hukunci cikin zafin rai". Amaaan yama baba godiya sannan ya tashi suka koma gida shida Amriin Ita kuwa Hamlat daman tayi gaba. Hamlat ba inda tq nufa sai gidansu ta sanarwa da mumy duk abin da ta gani da kuma abin da yafaru su ka kintsa sabon makircin da aikata wa iyayen Ahlam bayan sun gama Hamlat takoma gida cikin farin ciki domin ita aganinta insuka aiwatar da abinda suka shirya sun gama da su Ahlam. Kullum sai Amaan yaje yaduba Ahlam a asibiti sau biyu arana safe dq dare hakan yasa Amaan da Ahlam suka kara shakuwa wanda inhar bai zo ba Ahlam kan iya shiga damuwa domin sun shaku . Hamlat na ankare da hakan domin kullum sai ta bincika ko ansallame su. Satinsu biyu aka sallamesu domin kuwa kafar Ahlam tq warke sose har ta fara takawa sai sauran tabo shima da dukkan alamu zai bace. Da Hamlat taji labarin ansallamesu ba karamin dadi taji ba domin kuwa yau zasu kawo karshen soyayyar Amaan da Ahlam.