KUCHAKAR KISHIYA

Page34

by @xayyeesherthulhumaerath

Amaaan ne ya dauko su amota domin ko mawa gida . Suna isa su ka ga wani abu me firgitarwa wanda yasa kaf acikinsu ba wanda ya iya magana sai babba ne yayi dauriyar cewa" *Innalillahi-wa'inna-illaihir-raji'un*". Baba kuwa da Ahlam ba abinda suke sai kuka. Bama su kadai ba ni kai na wannan abu ya rikita ni domin kuwa anrushe gidan su Ahlam ko alamar gini ma babu inba wai wanda yama wajen kyakkyawan sani ba bazai ce da da gida agun ba. Amaaan yayi shiru kawai yana kallon ikon Allah . Baba ne yakara dauriyar cewa"haba kuyi dan gana ga Allah mana domin kuwa da abinda yatare mana". Amaan yace"baba kuyi hakuri domin kuwa nasan wannan aikin Hamlat ne babu shakka domin ya tuna lokacin dana ji tana waya cewa"take sun rushe kuwa?. Adai dai lokacin nashiga gida kuma ni wallahi ban kawo tunanin hakan ba. Baba yace"ba kome Amaan ai nasan ba yinka bane". Baba tace"to yanzu ina kake so mu zauna muyi rayuwa ba mu da kome ba mu da kowa akusa" . Amaan yace"indai wannan ne karku damu dama ina da niyar chanja muku gida nafiso ne agama kafin na muku magana toh kuma angama kuna asibity shiyasa nabar maganar ". Baba yace"ba ayi haka ba dannan kabari kawai ai wahalar sai tama yawa kuma kaga dama rikici ake akan ka" . Amaan yace"indai wannan ne karka sa mu damuwa baba ko me zai da wo dai dai". Baba yace"aa kadai sauke mu kawai". Baba tace"haba mai gida yanzu ina kake tunanin zamu je daga nan ka bari kawai tunda Allah yakawo shi ya taimaka mana". Baba yace"toh shikenan Allah ya mana jagora". Baba da Amaan su ka ce amin banda Ahlam wadda har yanzu kuka take. Baba tace"haba Ahlam dina kidai na kuka mana kinga yanzu munyi sabon gida". Amaan naji zafin kukanta har cikin ransa yadaure ne dai kawai dan kar ace yayi rashin kunya". Da kyar akasamu Ahlam tayi shiru sannan su ka dau hanya. Ba inda suka nufa sai filin sukuwa inda anan Amaaan yatsaya Abangaren su Hamlat kuwa sun hadu ita da mumy da maama sun sake kida sai rawa suke ba me wa wani fada acikin su adole suna murna sun samu nasara domin aganinsu tunda suka rusa gidansu Ahlam sun riga sun gama raza na su. Koda Daddy yashigo ma basu fasa abinda suke ba shiko da hike yasan halinsu girgiza kai kawai. Amaaan ya yi paking dai-dai wani kata faren gida wanda ni kai na yaban sha'awa domin dan dai-dai na mata daya ne. Suna shiga......