KUCHAKAR KISHIYA

Page 35

by @xayyeesherthulhumaerath

Tana haba yayanah ba ka ganni bane?. Amaan yayi murmushi yace"Naganki mana kanwata lafiya dai ko." Hamlat tayi wani murmushin kissa da kisisina tana shafa jikinsa tare da cewa"uhumm bakome yayana daman ina ma barka da dawowa neh." Amaan yayi murmushi sannan yacire hannunta ajikinsa yace"owk nagode sai da safe ko?. Bai jira me za ta ce ba yayi tafiyarsa yana murmushin mugunta. Ita kuwa ta kame kam ta rasa abin cewa. Tafi minti goma atsaye sannan ta shige bangarenta tana kuka batare da bata lokaci ba ta dau waya ta kira mumy ta sanar da ita abinda yafaru Su ka kara kintsi wani Abun da ba mu san menene ba ji nayi kawai Hamlat na dariyar mugunta tana"Shiyasa nake kara sonki uwa ta gari." Da haka sukayi sallama

WASHE GARI

Da sassafe Hamlat ta tashi ko sallah ba ta yi ba domin ba sa ba yi kullum tayi ba inbawai Amaan ya tashe ta ba kuma shima din da kyar take yi ba don son ranta ba. Ba inda ta nufa sai dakin girki ta ciro wayar ta sannan ta bude data domin shiga whatsApp group din da take na girke girke mesuna *ZAINAB SPECIAL KITCHEN* bata taba magana aciki ba domin ita aganinta bata da damuwarsu sai yau tayi sallama tayi sa'a kuwa Aunty *Shaxee* na online ta amsa mata Bayan ta amsa ne ta sanar da ita cewa girki takeso tayi kuma bata iya ba adan koya mata me sauki. Anan ne Shaxee ta mata bayanin yadda zatayi saukakkakiyar jallop din taliya. Aiko tana koya ma ta ko godiya babu ta sauka ta daura tukunya akan gass sannan ta soya mangyada ko soyuwa bai yi ba ta zuba wata katuwar albasa da kayan miya tukun ta dibo su karas da koren wake ta raba su bibbiyu suma ta zuba,ta dibo ruwa ta maka akai ko zafi bai fara ba ta dauko taliya leda daya ta juyo,sannan tasa magi guda ashirin. Sai murna take adole yau tayi girki hakan yasa ta daura ruwan zafi adaya bangaren. Taliyar bata kai minti goma ba aka sauke akasa a flas din abinci sannan aka juyo ruwan da ko ta fasa bai yi ba aflas din tea. Da sauri ta koma daki tayi kwaskwarima ta feshe jiki da turare sannan tadawo ta jera abincin akan dinning table tukun ta nufi bangaren Amaan domin ta sanar dashi yazo suci abinci . Sai wani tafiyar kasai ta take kamar wadda kashi ya taru mata aciki. Tana zuwa....