Page 36
Tana zuwa ta Domin ta sanar da Amaan tagama hada musu abincin karyawa. Da ta je kwofar dakin sai ta kasa budewa domin ita kanta kunya take abinka da basa ban ba. Tafi minti biyar atsaye sai chan da ta ji motsinsa kawai ta daure ta bude kwofar dai-dai da isowar Amaan kwofar kenan. Dukansu su ka tsaya kallon juna domin kuwa Amaan yasan inba neman masifa ba ba abinda yake kawota bangarensa. Amaan ne yadaure yace"Lafiya kuwa Hamlat." Ta gyada kai alamar eh sannan tadaure tace"Dama na ma na abinci karyawa ne nazo na fada ma." Amaan yayi murmushi sannan yace"Kinnsan dai ni bana karyawa sai karfe TARA kuma yanzu bakwai da rabi ne." Hamlat ta shagwabe fuska tana"Haba yayana pls na yau fa kadai." Ba da son ran Amaan ba yace"To muje." Suna tafiya Hamlat na kisisina kamar baza ta tafi shiko Amaan azuciyarsa cewa yake"Koma miye dai na fi karfin ku da ikon Allah." Suna zuwa ta bude flas din taliyar shikan shi kamshin in mutum yaji sai cikinsa ya burga haka Amaan yadaure duk da ya fara jin Amai kafin ma yaci . Ita kuwa oganniyar sai murmushi take tana ta zuba jagwalgwalon ta aflet ta gama zuba mai kafin ta miki masa ta dibo Ruwan tea a cup ta zabga uban suga da madara ta mika masa tare da taliyan. Tuni Amaan yaji numfashin ya fara daukewa yaso yadaure Amman ina ai cikinsa ya fara gurnani da gudu yatashi ya nufi bayan gida.