Page 37
Yana zuwa sai Amai tun abinda yaci jiya shine yake dawowa . Hamlat ta biyoshi ta tsaya abayansa Hannu rike da k'ugu tana fadin"lallai ma rainin wayon yayi yawa tsabar bakason cin abincin da nayi shine za ka tsiri amai? Shi dai Amaan bai kulata ba ya na ta k'ak'a tun amansa . Ta ci gaba da cewa"lallai ma gaskiya da sa ke." Da k'yar Amaan yasamu amannan ya tsaya ya kurkure bakinsa ya juya kenan zai fita yaga Hamlat ta tare hanya . Araunane yace"Hamlat dan matsa banajin dadin jiki nah." Ta kallesa ta galla masa harara tare da tsake sannan tayi gaba. Da k'yar Amaan yake tafiya Amman wannan bawair Allahn ko tausayinsa ba ta yi sai ma bala"i da ta ke ta faman surfawa haka yadau jakarsa ya barmata gidan . Da ya je motar ma da k'yar yake tukin haka yadaure har ya isa office dinsa anan ne ya kira likitansa domin yazo ya dubasa. Hamlat kuwa tunda yafita ta kira mumy da maama tasanar musu abinda yafaru anan ne maama take sanar da ita cewa"ai Amaan yabawa su Ahlam gida." Hamlat tace"lallai matsiyatan nan basu daddara ba ko? Hmmmm Anan suka yi sak'e sak'ensu Kafin ta shirya ta nufi office yadda dai aka saba waje tsaf ciki tsami. Bayan an idar da sallar azahar Amaan yasamu karfin jikinsa sose ya nufi gidan su Ahlam. Yana bud'e k'ofar gidan Ahlam ya gani zaune tana ta karatun ta yanzu tunda tayi ciwon nan ba magana ta cika son yi ba ko tsokanarta bakamar da ba. Tana hangoshi tayi murmushi ta tashi kenan zata zura da gudu ai tuni ta tuna fa tana da ciwo hakan yasa ta fara jan kafar. Amaan yace"Ke Ahlam miye haka tsaya mutafi tare." Batasan lokacin da ta tsinci kanta da tsayawa da sai ji tayi anriko hannunta ana cewa"Muje mana." Ta bude baki kenan za ta yi magana.....