Page 38
Taji Amaan yace"Kanwa Tah? Ahlam ta dago ta kalleshi Alamar bai fada dai-dai ba hakan yashi yin murmushi sannan yace"Auh sorry Aunty Ahlam ya jikin? Ahlam ta washe baki tare da cewa da sauki. Sun karasa shiga falo suna shiga Ahlam ta fisge hannunta ta nufi inda baba ta ke ta zauna kan cinyarta. Amaan yayi murmshi yana"lallai ma wato guduna kike zaki sani." Baba tace"Hmm ai Wannan sai ahankali dama ta gun tsokana ne ta fi kauri." Amaan yayi murmushi yace"Ina hini baba? Baba ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa mutanen gidan. Bayan sun gama gesawa ne Amaan ke tambayar shin ko su na da wani abun bukata. Annan ne Baba takara masa godiya tare da fadin suna da kome ai . Bai tambayi baba ba domin kuwa yasan Baba baya nan yabude masa shagon sai da atampopi a sabuwar kasu da ke yan tifa. Dan haka yatashi domin tafiya yayiwa Baba sallama har ya kusa fita yaji Ahlam tace"kanina! Sai kuma tayi shiru, Ya juyo tare da murmushin sa yace"kanwa Tah zo ma na." Ita ma da murmushin ta takarsa wajen sa. Amaan yace"yane Aunty? Yana kallon idon ta. Ahlam tace"Dama fa naji sauki ne kuma banje skul nakarbo takardar gama aji uku na ba." Amaan yaji dadi domin ya kara tabbatar da cewa Ahlam yar kirkice me son karatu. Yace"toh shikenan ki ba ri zanje da kai na karbo miki da ga nan sai ma muyi maganar cigaban ki." Ahlam taji dadi sosai hakan ya sa ta ma sa godiya sannan ta ko ma cikin gida. Washe gari da safe kuwa Amaan ya shirya ya nufi gidansu bayan sun gesa da Daddy ne yake sanar masa cewa"ai sunyi zama da Baban Ahlam yace kawai duk sanda suke da bukatar ayi bikin ba matsala." Amaan yaji dadin hakan matuka yanason ya Ma Dady magana Amman yakasa Dady ya fahimci akwai magana abakinsa hakan yasa yace"Ina ga asa bikin nan da wata ko? Dasauri Amaan yadago yana murmushi alamar eh. Dady yace"toh shikenan bakome Allah yama Albarka ." Amaan yace"Ameen." Sannan yatashi ya nufi bangaren babansa. Yana zuwa yasanar da Baba abin da ake ciki . Baba ma yasa masa albarka sannan Dady yakara kiransa akan anjima zasu gidansu Ahlam din. Abangaren su Hamlat kuwa sunshirya tsaf ita da kawarta maama tare da wawiyar mahaifiyarta domin zuwa su gidansu Ahlam sukara ci musu mutunci. Mumy ce taje tasamu Dady akan bara takai Hamlat asibiti domin ciwon ta na kwokarin tashi. Dady yace"Adawo lafiya inda shima yanufi gun motarsa." Basu san Amaan nacikin motar Dadynba shiko ya hangosu domin bai sanma Hamlat bata gun aiki ba azuciyarsa cewa yake"Allah yakyauta da mata irin wannan." Maganar Dady ce dawo dashi yace"Amaan muje mufara dauko mallam sai muje gidan nasu." Amaan yace"toh." Sun zuwa suka tarar da malam ya fito su kawai yake jira hakan yasa basu bata lokacinsu ba Suna isa gidan Amaan ya hango motar Ahlam achan gefe inda suko su Dady ko lura basu yi ba,tuni gaban Amaan ya fara faduwa addu"ah kawai yake azuciya har suka shiga gidan sannan yayi hamdala tunda bai ga su mumy ba. Suna shiga Amaan yaje yakira Baba . Suko su maama sai yanzu suka fito amota domin sun tsaya kitsa irin wulakanci da zasu musu. Mumy ce gaba suna binta abaya. Baba yafito suna gesawa da su Dady sukaji anwani bankado kofa idonta rufe da masifa tashigo tana"Ina matsiyatan marasa zuciyan suke ? Duk kansu kowa ya kame banda Baba wanda yatafi duniyar tunani ko wacece wannan. Hamlat da Maama ma kamewa su kayi ganin Dady Da Amaan na wajen. Mumy ta ci gaba da cewa"wai bazaku fito bane talakawan banza da wofi." Ta ga dai shirun yayi yawa tana bude ido ta cii karo da Dady tuni ta fara rawar murya domin tasan yau ta kawo karshe hakurin Dady. Tana"ba fa ba fa nan mu mu ka zo ba maama meyasa zakusa muzo nan nibance muzo ba ba fa." Dady yace"ku fita agidannan inba kwaso ranku ya baci ." Yana fada tare da nuna musu kofa. Dasauri mumy ta fita inda Hamlat da maama suka bi bayan tah. Dadyne yabawa Baba hakuri. Baba yace"Bakome ai mata sai hakuri haka suke." Anan dai Dady yama Baba bayanin yadda su ke son auren anan kuwa akasa karshen watan satin ban nan . Suka yi sallama da su Baba sannan suka nufo hanyar gida. Mumy kuwa tana nan tarasa ina zata sa kanta domin ita bawai ma ganin Dadyn bane ya fi damunta kar ace maganar aure su ka je yi. Dady na shigowa yanufi bangarenta . Tana ganinsa ta mike tana"...
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_