PAGE* 39
------------------------------------------------------------------------------------------
~AuntyNah AuntyNah banji zafin mutuwarki ba sai yau danazo gida naga yaranki hmm Allah ya jikanki AuntyNah Dukanmu muna kewarki~
_Wannan shafin sadaukarwa ne agareka Amsard dina Yayana Abin Alfahari nah_
Tana, "Haba Alhaji ya za ka min haka wai harda kai za'a hada baki domin a wulakan tah yar ka?
Dady ya mata alamu da hannu yana fadin ,"Da ka ta! Yanzu duk abinda ki ka je kika aika ta bai yi ba sai kinzo gida ma kinyi wani?, toh wallahi ya isheki na gaji da irin wannan mummunan halin , gashi har kin fa ra ko ya wa yar ki Ko ince har ma ta ko ya."
Mumy tayi rau da ido domin tunda take Dady bai taba fita mata agiya ba irin na yau.
Dady ya kara da ce wa, "Kuma wallahi indai kikayi sanadiyar fasuwan auren nan to abakin naki auren." Ya na gama fada ya yi ficewarsa abinsa mumy kuwa ta zube agefen gado azuciyar ta ce wa ta ke, "Ah lallai akwai aiki agaba na har abin ya kai ga anamin bara za na da aure na hmmm zan bari ayi auren nan amman wallahi yar matsiyata sai kin gwanmace kidi da karatu."
Bayan ta gama tunanin ta ne ta kira Hamlat awaya ta sanar da ita kome sannan yanzu zasu fara shirin biki.
Hamlat ba ta so hakan ba amman ya ta iya duk jarabar mahaifiyarta ma ta kasa bare ita kuma ita awa."
Washe gari Da sassafe mumy ta nufi bangaren Dady bayan ta geshe sa ne ta neman Afwan akan abinda tayi jiya .
Shiko Dady yaji dadin hakan inda ita kuwa azuciyarta ba haka bane.
Mumy tace, "Tou yaushe akasa bikin?,kasan mu mata akwai mu shirye-shirye gwara afada tun huri."
Dady ya gyara zama yana, "Haka ne fa toh ance dai karshen watan nan inaga asabar din da za to akarshen watan nan shine ranar d'aurin auren."
Mumy tayi murmushin dole tare da fadin, "Toh Allah ya kai mu."
Dady ya Amsa da, "Ameen."
Mumy na barin falon Dady ta kira Hamlat awaya bayan ta gama bayyana mata yadda suka yi da dadyne take cewa, "ki barni dasu wallahi Allah yakai mu ayi Auren da kafar ta zata fita wallahi."
Hamlat tace, "Hmm mumy ki barni da ita wallahi indai wannan mitsitsiyar yarinyar ce ai kaman nagama da ita."
Mumy tace, "Hmm ina nan ina kara mana wani babban shiri."
Ahaka hirar tasu ta kare ba abin arziki sai yadda za ashuka tsiya ake tsarawa.
Amaan ya fito zai tafi office , Hamlat nazaune afalo ,ya kalleta yakau da kai alamar bai ma ganta ba.
Har yaje kwofar fita , Hamlat tace , "........
Urs preety xayeesherth
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_