KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 40

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

~Life without you will be like going to sleep and never having sweet dreams~❤❤❤

Haba ango ba magana? ai dai yaci ka tsaya mu gesa .

Amaan ya juyo da murmushin nasa wanda bai kai zuci ba yace, "Au uwargida ai ban lura kina wajen ba."

Wannan kalma sai da ta taba zuciyar Hamlat Amman ta daure domin ba tason nuna masa tsarinsu ya baci tace, "Hmm Ango kenan To Ina kwana?"

Amaan yace"lafiyalau fatan kin tashi lafiya?"

Tace, "lafiyalau, ya kanwar tawa?"

Amaan yace ,"Wace kanwa kuma? Daman kina da Kanwa ne? ko Amrin kike nufi?"

Hamlat tayi murmushin dole tare da fadin, "Wace kanwa kuma nake da ita bayan Amarya ?"

Amaan yace, "Oh ai sai kice min Ahlam dinah toh tana lafiya kuma tana geshe ki."

Hamlat ta kasa magana tsabar takaici sai Hmm.

Amaan yace, "Toh nikam natafi sai nadawo uwar gida."

Hamlat ta so yin magana sai kuma ta tuna da abinda mumy ta fada mata awaya ai ko tuni tace, "Adawo lafiya."

Amaan ya ji mamakin jin hakan kawai cewa ya yi, "Ameen." sannan ya fita office.

Yana fita kuwa ita ma ta tashi ta nufi gidan su Maamah sai ta je sun gama tseguminsu sannan ta nufi office itama.

Amaan kuwa yana zuwa yakirawo uncle Salim awaya yazo ya sa me shi a office .

Ba bata lokaci uncle Salim yazo .

Yana zuwa bayan sun gesa Amaan yake sanar masa cewa ,"biki fa ya karato ya kamata mufara shirye-shirye."

Uncle Salim yace, "Haba dai Har abun ya matso kusa haka?"

Amaan ya ce, "kwarai ma kuwa karshen watan nan."

Salim yace, "Ah dole musan abin yi ."

Da ganan suka tattauna yadda abin zai kasance .

Sun dade sose suna hira sannan suka rabu akan Anjima zasu hadu suje gidan su Ahlam tare.

***************

Misalin karfe hudu da minti arba"in Amaan ya bar office yaje domin su hadu da Salim.

Suna haduwa Salim yace, "Kaga kamata yayi muje shagon babanta yanzu musanar masa tsarinmu."

Amaan yace ,"To shikenan muje."

Suna zuwa gun Baba suka gesa cikin girmamq juna bayan nan ne Salim yake sanar da Baba ce wa, "Suna so in anyi auren Ahlam ta tafi kano karatu sai ta karasa zata dawo kafin ta kara girma."

Ba karamin Dadi Baba Yaji ba Domin yana so Ahlam tayi karatu.

Baba yace, "Masha Allah ai hakan ma yayi."

Ahaka suka rabu cikin girmama juna.

Suna barin gun Baba Suka Nufi filin sukuwa gidan su Ahlam.

Suna isa suka shiga ciki Baba ce zau ne atsakar gida tana yanka *latas*.

Da sallamarsu suka shiga ta amsa cikin fara'ah.

Ba ta musu iso ga su shiga cikin daki bayan sun shiga ne suka gesa Anan ne Baba take cewa, "Oh Ahlam fa yau narasa meke damunta taki walwala sai zaman daki tun safe."

Salim yace, "To anya kuwa lafiya?

Baba tace, "Toh wayasan mata bara nakiro muku ita ko ku ta fada muku."

Baba ta tashi ta nufi dakin Ahlam ta sa me ta akwance tace, " to Ahlam kinyi baki kizo ana jira."

Ahlam tace, "umm Baba tah ni fa bana son fita."

Baba tace, "Kiyi hakuri kinji auta tah."

Dakyar Baba ta shawo hankalin Ahlam ta taso Ta nufi falo Baba kuma ta nufi kichin.

Tana zuwa....

Urs preety xayeesherth.

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_