KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 41

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------ ~Your love warms my heart like the glow of a candle light in a midsummer night's dream.~

```WANNAN SHAFIN NAKUNE KU KADAI YAN GRP DINA KUCHKAR KISHIYA FANS MY AMBEBY ZAINAB ADAMU MATAR KAWU MY SISTER MY WALIDA MY MOMIN YASMIN MY HAFSAT MY MMN SHAHEEDA MY HUSAINA KAI KUNA DA YAWA FA DUKANKU INA JIN DADIN COMMENTS DINKU KUMA INA ALFAHARI DAKU AMATSAYIN MASOYANA GA PAGE DINNAN KUYI YADDA KUKESO DASHI SAI WA INNDA KUKA ZABA ZASU KARANTA🥰🥰 XaYeesherth luvs u oll❤❤```

Ta ga Uncle Salim ne da Amaan Ta washe baki sai kuma ta tuna da wani abu tuni ta bata rai.

Uncle salim yace, "Haba yar kanwata ya yau ku murmushin ma babu."

Ahlam ta turbune baki kamar za ta yi kuka tace, "Uhum bayan Wannan kanin nawa ne yaki zuwa ya duba ni yau fa kusan kwana uku?"

Amaan da Uncle Salim suka yi murmushi .

Amaan ya durkusa kasa ya kama kunnensa sannan yace, "Afwan ranki yadade."

Ahlam ta washe baki tace, "Uhum to ba ka ce min Aunty ba."

Amaan yace, "Au to aunty nah."

Tace, "Toh tashi kazauna."

Shiko Salim gaba daya hankalinsa ma yatafi wata duniyar azuciyarsa cewa ya ke, "Dama ni ne da Ahlam mana da na nuna mata cikakkiyar soyayya amman abota tafi kome dole nabarwa Amininah."

Sai da Amaan yatabo sa tukun hankalinsa yadawo jikinsa.

Amaan yace, "ya dai mutumi nah?"

Salim yace, "bakome naga ai kuna ta soyayya neh."

Ahlam tace, "Uncle ya maganar sakamakon jarabawar mu neh ."

Salim yace, "Ai sai dai mugodewa Allah tunda duk kun haye sai sarai da cigaba."

Amaan yace, "kunga hirar nan taku baza ta kare ba gashi ana kiran sallah, Ahlam bamu buta muyi alwala."

Ahlam ta tashi taje tadauko musu buta ta basu .

Suka fita tsakar gida sukayi alwalarsu bayan sun idar ne Amaan ya kira Ahlam ta karba sannan suka yi sallama .

Har yaje kwofa zai fita tace , "saura gobe ma karka zo sai nasaka tsallen kwado yasin."

Uncle Salim ya kyal-kyale da dariya yana cewa, "Ahlam wato dai har yanzu halin na nan ko?"

Amaan yace, "Ai sai ma wanda yakaru kuma fa innazo ba bari na take na tafi ba yau ma dan ta ganka neh."

Ahlam ta galla musu harar sannan tace, "Eh din Nayi." Ta musu gwalo sannan ta shiga gida da gudu.

Suka fita suna ta dariya Salim yace, "Wallahi yarinyar nan na birgeni kullum kara girma take amman intama wani abu kamar yarinya in taso kuwa tafi babbar ma hankali da basira."

Amaan ya numfasa sannan yace, "Salim bazan bo ye ma ba wallahi ina matukar kaunar Ahlam fiye da yadda ake tsammani tun tanq yar karama inaga ma batafi shekaru hudu ba lokacin tafara zuwa makaranta nake zuwa kwofar gidansu domin kawai inganta Kuma ahakan ban taba bari taganni ba sai da ta fara girmab nan domin tsoro nake ji kar ta ce bata so na ko kuma iyayenta su hanani, haka kuma duk randa bangan ta ba kuwa wallahi bana iya barci, shiyasa yanzu inna tuna wai zan aure ta sai abin ya ban mamaki."

Salim ya ce, "Tab Ah lallai kai neh *Majnon* wannan irin soyayya haka akalla fa kun fi shekara goma kuna tare."

Da wannan hira suka rabu Amaan ya huce gida shima uncle yayi gidan su.

Urs preety xayeesherth

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_