KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 42

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

~Everything in your life is a reflection of a choice you have made. If you want a different result, make a different choice.~❤

```MATAR KAWU ZAINAB ADAMU SAKO DAGA HAMLAT KIN KUSA KAI TA MAKURA FA WATO KE YAR ZUMUNI HARDA ANKO KO? TO AYI AUREN MUGANI🤪 ```

Bayan Baba ya dawo gida ne yake sanar da Baba yadda su ka yi da su Amaan Baba taji dadi sose tace, "Ai kaga ta kara girma ma kan lokacin hakan zai fi."

Baba yace, "wallahi kuwa ai ni naji dadin shawarar nan ko ayanzu nakara sanin cewa yaron nan nada hankali."

Tace, "Sai dai kawai muce Allah yasaka da Alkairi".

Baba yace"Ameeen summa Ameen."

********Washe gari*********

Yau ya rage saura kwana uku biki.

Da sassafe Amaan yatashi dOmin yanzu sun fara hidimar biki duk da wani programs zasu yi ba da yahuce daya zuwa biyu, Yana tashi yaje yayi wanka sannan yashirya cikin manyan kaya da kagansa kasan yana cikin farin ciki ba kaMar kwanakin baya ba.

Su uwar gayya Hamlat ko tashi daga barci ba ayi ba.

Shiko Amaan yana fita ba inda ya nufa sai gidan su,yaje ya samin Amrin domin zasuje tadau Ahlam akai ta wajen gyaran jiki da sauransu.

Amrin taji dadi sose domin zata ganin masoyiyarta barin ma tanaso taga Ahlam ta dau wanka domin tasan anan kyanta zai kara baiyana.

Tace masa, "Yaya Ango ai ba matsala tunda ma ta iya karatun hausa ai zama zamuyi tayi karatu sose domin sanin ita wacece."

Amaan yace, "Ah lallai Amrin ni kike fadawa hakan ma ko?"

Amrin ta kyalkyale da dariya sannan tace, "Yo ai wannan kaza miyar matar ta ka ce sai antashi tsaye anuna mata cewa ita ba kome ba ce."

Amaan yayi murmushi yace, "kidai na fadan haka Amrin."

Amrin tace, "Umm nidai bara nadauko hijabi na muje kar lokaci ya kure,domin gun aunty Aisha nakeso muje."

Amaan yace, "yauwa yar kanwata maza ki zo mu tafi yakarasa maganar yana fita."

Amrin tayi sauri tasako hijabinta har kasa sannan ta fito.

Suna cikin tafiya Amman yakirowo Salim awaya akan cewar,"Su hadu abakin titin yan TIFA."

ai kowa ba jimawa sai ga Salim nan,Amrin ta bude kwofa zata dawo baya yace, "Aa wallahi ba matsala ki zauna abinki."

Amaan yace, "Aa dai da kabari ".

Yace, "Aa kabari kawai." yashige baya ya zauna.

Bayan ya shiga ne suka gesa da Amrin.

Yace, "Amaan daman muna da kanwa haka baka taba fada min ba."

Amaan yace, "Hmm ai gashi yau ka gan ta ma."

Suna ta hira har suka isa gidan su Ahlam .

Amrin ce ta fara shiga da sallamar ta inda Ahlam ta tawo da gudu tana, "Oyoyo Amman fa ni na yi fushi dake."

Amrin tace, "Umm Auntyna kinsan fa ina skul ne ai da tuni nazo."

Ahlam tace, "kinci sa,ah kince min Aunty da bazan yarda ba."

Amaan da Salim suka shigo da sallamar su Ahlam ta musu iso ga su shiga daki.

Ahlam kam ta manta dasu ma sai zuba takewa Amrin ita ko tana ta dariya .

Baba ce tazo suka gesa sannan tace, "Toh uwar yan surutu ko ruwa ma ba abasu ba?"

Salim yace, "Aa Baba karki damu wallahi daga gIda muke."

Amaan ya ma Baba bayani akan zasu gurin gyaran jiki dA Ahlam .

Baba tace, "Ai ba kome Adawo lafiya."

, "Toh Babata Tashi ki shirya zaku fita anguwa ." cewar Baba.

Ahlam ta tashi tashiga daki batare da bata lokaci ba ta fito tana, "Aunty Baba tah kimin Dan sululu na kafin nadawo."

Dukan su sai da sukayi dariya. Baba tace, "kunga halin nata ko? kai da kam Amaan kana da aiki agaba."

Dukansu suka kara dariya sannan suka fitA.

Ahlam tashige gaba abinta Amrin da Salim abaya.

Ba inda suka nufa sai gidan Aunty Aisha, suna isa kuwa Aunty Aisha ta karbesu da karamci da hike damqn me son mutanece ga bar kwanci.

Bayan sun gama zaiyana mata abinda yakawo su Amaan ya ce, "su zasu tafi sai yamma zasu zo su daukeso."

Bayan sun tafi ne Aunty Aisha tace,"..........

Urs preety xayeesherth

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_

NASIHA

*Yake Yar uwa musulma;*

_1.Ki kiyaye daga yin surutu da yawan magana,Allah madaukakin sarki yace;_

_"Babu wani alheri acikin masu yawa daga ganawarsu,face wanda yayi umarni da wata sadaka ko kuwa gyara tsakanin mutane."_

*Kuma ki sanu cewar akwai mala'iku masu rubutawa kuma su dididge duk abinda kike fada.*

_"Alokacin da masu haduwa (mala'iku) biyu suke haduwa daga dama,kuma daga hagu akwai mazauni,baya lafazi da wata maganq face a like da shi akwai mai tsoron halartacce."_

*Kiyi kokari wajen magana takaitacciya mai ma'ana*