KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 43

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

_wayyoo yan grp dina kuchakar kishiya fans kuna nishadantar dani da cmmts dinku ina jin dadi wallahi akullum koda banda niyar cmmts inna tuna ku sai inji karfin gwiwa much luv sisters_🥰🥰🥰❤❤❤❤

_wannan shafin sadaukarwa ne agareki sister LAYUZA KABIR ina tayaki murnar kammala book din ki YAN ARABIC Allah yakara basira_

************

Tace,"Toh Hajiya Ahlam Amarya kafin in fara miki gyaran jiki ya ka ma ta muyi wata muhimmiyar magana ki saurare domin naga kinfi kauri ta wajen abin wasa,ki sani cewa Aure zakiyi yanzu kuma ba ke kadai bace kina da abokiyar zama dole sai kin dage da AZKAR safe,rana,da kuma dare sannan ki san yadda zakina tattalin mijinki, karki yarda ki kasance me kazantar kullum cikin tsafta da kuma kamshin ya kasance jikinki nayi dakin ki na yi haka kuma shima mijinki nayi, kullum karki kasance cikin yin shiga daya inya fita da safe ya barki da kananun kaya to fa kafin ya dawo ki tattabatar kinsa masa doguwar riga ko ko atamfa dai inko da safe atamfa ce ajikin ki to kafin yadawo kinci kananun kayanki, yawancin maza suna, son mace me gashi dan haka ko baki da dashi inkika dage da gyarawa kina masa ado dashi zai ji dadi,haka kuma fannin abinci da drinks yakamata ki koyesu kala kala, sannan kullum ki kasance kina wanka da ruwan lalle basai kin kashe kudin ki awasu abubuwan ba ke da kanki zaki iya gyara jikinki kina shan kunnun wanken suya,gyada,aya,alkama,shinka far tuwa koda sau daya ne arana,Ki kasance me kissa da kisisina awajen mijinki karki yarda da wani cewa kina da abokiyar zama alokacin mantawa da ita zakiyi sannan kuma da ma naga alamun ki na da shagwaba tanan fannin bamu da matsala."

Ahlam da Amrin su nutsu kawai sauraren Aunty Aisha suke.

Aunty Aisha ta kara da cewa, "Fatan dai kin fahimta."

Ahlam tace, "eh jiki asanyaye."

Aunty Aisha tace, "Yauwa haka akeso Amman fa kisaki jiki dani domin ni yayarku ce dukanku kuma ma zan baki wani hausa novel da zAi tai makeki duk akan abubuwan dana fada miki da wanda ban ma fada ba."

Ahlam tace, "Toh nagode Auntynmu."

Amrin tace, "Aunty adai rage kar ahauka tamin yayanqh."

Aunty tace, "Ai sai dai kuyi hakuri kawai domin yayanki sai yaji chanji na mussamman."

Dukansu suka sa dariya sannan Aunty Ta tashi tana, "Kunga lokaci na kurewa bara muyi mu fara."

Batare da bata lokaci ba Aunty ta fara dilke Ahlam suna yi tana kara mata wasu bayanin .

Abangaren Amaan da Salim kuwa ba inda suka huce sai wajen telen da yakaiwa dinkunan Ahlam suka karbo .

Dagq nan kuma suka huce kasuwa anan ne suke hira Salim yace, "Amaan gaskiya nima fa yanzu auren nan zanyi dan nasamo mata."

Amaan yace, "Haba ai wallahi ko dana ji dadi tun tuni anata fama dakai."

Salim yace, "Ba kowa bace illa kanwar mu Amrin."

Amaam yayi murmushi yace, "seriouse?" Salim yace, "Eh mana ko baza abanin bane?"

Amaan yace, "wane ni ai wallahi naji dadin lamarin nan yau mq zan sanar da dady."

Salim yace, "woo amman gaskiya nagode wallahi ."

Da wannqn hirar suka gama siyayyarsu.

Ahlam kuwa tanan ta fito asak amarya "ko ayau adaura." cewar Amrin.

Aunty tace"ai ba zama ki gane ta sai mun dau wankan dina."

Ahlam dai tayi shiru baki ya mutu duk rawar kannan da surutu babu .

Da kyar Aunty tasa tadan saki jikinta aiko ta fara zuba.

Misalin karfe 5 dai dai su Amaan suka dawo daukan dai-dai da fitowa Ahlam daga wanka.

Tana jin su afolo tuni tafara sa kaya kamar wadda suke ganinta.

Auntyce tazo ta bata wasu kayan tace, "tasa ."

Bayan ta gama sawa ne ta fito falo tana fitowa kamshinta yakarade dakin Amaan kawai zuba mata ido yayi azuciyarsa yana cewa, "Aminci da karamci su kara tabbata agun sarauniyar kyawawa."

Salim ne yace " Dalla mallam kwanq nawa ne wai anan dinma sai kq nuna halinka."

Amaan yaji kunya sose domin ya manta ma a inda yke murmushi kawai yayi.

Aunty tace, "Ango kenan."

Amman yayi murmushi sannan yatashi yna fadin, "Toh Aisha sai anjima mun gode sose sai kuma in mun dawo gobe."

Aunty tace, "Bakome ai Allah ya kai mu."

Aunty ta rakasu har wajen get tace, "Ahlam karfa ki manta ki karanta littafin nan."

Ahlam tace, "Insha Allah Aunty."

Amrin tace, "umm nima dai asamin nakaranta."

Aunty tace, "Anki din kema ki fito da miji."

Dukansu sukayi dariya sannan sukayi sallqma.

_Urs Preety Xayeesherth_

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_