KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 44

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

_Ina kuke yan team 🅰 dangin uwar gida Hamlat fatan kun karbo ankon ku domin gobe fa akwai💃💃ba daku nke ba yan team 🅱 dangin amarya Ahlam abamu waje🤪_

*Yake Yar uwa musulma;*

_1.Ki kiyaye daga yin surutu da yawan magana,Allah madaukakin sarki yace;_

_"Babu wani alheri acikin masu yawa daga ganawarsu,face wanda yayi umarni da wata sadaka ko kuwa gyara tsakanin mutane."_

*Kuma ki sanu cewar akwai mala'iku masu rubutawa kuma su dididge duk abinda kike fada.*

_"Alokacin da masu haduwa (mala'iku) biyu suke haduwa daga dama,kuma daga hagu akwai mazauni,baya lafazi da wata maganq face a like da shi akwai mai tsoron halartacce."_

*Kiyi kokari wajen magana takaitacciya mai ma'ana*

Anan ne fa Salim ya fara nema wa zuciyarsa wajen zama agun Amrin Shiko Amaan sai tsokanarsa yake yana, "wato ma ko kunya ko? yanzu dai ka fara girmama ni nazama siriki."

Ko kulasa bai yi ba yana ta wa Amrin magana .

Ita kuwa Ahlam sai dariya take Amaan najin dadi.

Ahlam suka fara saukewa agida sannan suka je suka sauke Amrin.

WASHE GARI Da sassafe Hamlat ta tashi Maamah ta zo ta dauke to adole suma an bazana gyaran jiki anje LALLE,WANKE KAI,DAKUMA DILKA.

Amaaan da ya tashi bai ganta ba baiyi mamaki ba domin yasa ba dama da hakan ba yau tafara ba hasali ma bata taba tambayarsa fita anguwa bA.

Ashiryensa ya fito inka gansa kace yau ne daurin Auren, Yana fita suka hadu da salim domin sun riga sun gama magana tun jiya basu nufi ko ina ba sai gidan su Amaan domin daukan Amrin ashirye suka sameta hakan yasa basu bata lokaci ba suku nufi gidan su Ahlam,

Ahlam na nan da kawaye ancika gida adole anfara sha anin biki barin ma su Amrah uwar gaiya.

Amrin ce tashiga domin kiran Ahlam su Amaan sun tsaya awaje sabida gidan acike yake da baki.

Ahlam da Amrah ne suka biyo bayan Amrin, Suna fitowa Amaan yace, "Toh matata ta fito mallam sai akoma baya ko."

Salim yayi murmushi yanq, "kai ma ai kasan nafison bayan domin anan sahibata take."

Aiko Ahlam na zuwa ta shige gaba abinta su Amrah da Amrin tare da Salim ne abaya.

Suna tafiya anata wasa da dariya musamman ma uncle Salim da yake ta tsokanar Ahlam Da Amrah Har suka isa gidan Aunty Aisha.

Suna zuwa batare da bata lokaci ba Aka fara gyara Amarya Aisha takirawo me jan lalle domin ta wa Ahlam kafa da tafin hannu har ma da bayan hannun domin ita tace batason bakin lalle.

Da sauri sauri suke abin domin sukoma da huri kar azo sa lalle.

Su Amaan kuwa gida suka koma domin Daddy da Baba suna nemansa.

Bayan sun gesa ba Dadyne yake sanar masa cewa, "Ga Akwatunan nan nasa anmin order daga DUBAI Guda sabin fitowa ne me seti TAKWAS ka duba ko kayan sunyi."

Amaan yayi murmushi sannan yace, "Ah Dady ai nasan kome ma yayi ba abinda zance sai dai godiya Allah yasaka da Alkairi."

Salim ma ya taya Amaan godiya sannan Dady yace, "bakome ai son kome namq naka ne yanzu dai anjima za akai kafin sa lallen danaji su khadija na fada anayi daman dan basu zo bane ba akai tun huri ba Amman tunda sunzo nace su shirya bara su karasa sai akai kayan."

Amaan yace, "Toh shikenan Dady."

Shidai Baba ba abinda yakewa Amaan sai nasiha akan yq rike matan shi da Amana kar ya nuna musu banbanci.

Ba tare da bacin lokaci ba duk su Aunty khadeeja sun shirya da hike yar itace babbar yar abokin Dady wanda suka zama dangi guda.

Alokacin suka nufi gidansu Ahlam batare da sannin yau za akawo kaya ba.

Gaba daya yan gidan sunyi mamakin irin kayan da ake shigowa dashi domin kaf acikin su ba wanda yataba ganin irin wannan akwanti GOLDEN me adon gyali gyali kaman huta kuma gashi har guda takwas da jaka zuwa unguwa sannan da karama ta rikewa ahannun, Ga kayan sa lalle bokiti biyu ta burma hudu.

Gaba daya yan gidan su rasa ina zasu sa kansu dan farin ciki mussaman baba da ta rasa me zata basu Khadeeja ce tace mata, "karki damu wallahi mu kam akwoshe muke daga gida yanzu zamu koma domin aiki ya mana yawa."

Har bakin kwofa Baba da yayarta suka rakosu suna godiya sai da suka shga mota sannan suka koma.

Ahlam ana nan ansha kyau ko ayau adaura ga LECTURES da Aunty Aisha ke kara mata .

Suna cikin hira Ahlam tace ,"Aunty Aisha Dan Allah ki tambayi Dadynson Hanan yabarki yau muje gidan mu ki kwana kinga ni ban cika kwalliya ba ban iya ba wallahi."

Aunty Aisha tayi murmushi tace, "Ah yaushe zan bar mijina shi kadai na dai miki Alkawari zan zo da huri kuma har dina ma sai munje."

Ahlam tace,' yauwA har naji dadi wallahi."

Ahaka suka ta hirarsu har aka kammala har akama Amrin da Amrah ma lalle, misalin karfe 4 su Amaan suka zo suka daukesu.

Ita kuwa uwargida ana chan ana hauka.

Aranar da kyar Ahlam suka rabu da Amaan domin yanzu ta fara sanin me ne ne so.

Washe gari🤪🤪

Urs preety xayeeesherth

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_