PAGE* 46
------------------------------------------------------------------------------------------
_gaskiya ina fushi da masoyana kuma masoyan book dinnan basai na fada ba kunsan abinda kukayi_
Banda yan daurin Aure da basu san dawar da ake ciki ba.
Aunty Aisha ce ta kirawo Amaan awaya sannan ta dauki Ahlam suka je dakin da ba kowa .
Anan Amaan ya shigo yasame su gaba daya ya birkice suka fara mata Addu"o"i sun kusa Awa daya Ahaka sannan ta farka .
Tana farkawa kuwa Amaan ya miki godiyarsa ga Allah alokacin Aunty Tace , "Yauwa sannu Ahlam tashi kiyi wanka ko?'
Ahlam ta kalli Amaan tace, "Dan Allah karka rabani da gidanmu wallahi inason Baba tah."
Amaan yayi murmushi yana, "karki damu ai kina tare da babarki yanzu tashi kiyi wanka,ni barin je ana jira na awaje."
Alokacin Ahlam tayi wanka takara sa wani kayan Aunty ta gyara ta kamar ba ita ba.
Doguwar rigace fara sol me jibin kayan sarauta ko ina ston ne da bit sai kyalli take kome fari ga tashin kamshi.
Sai da tagama kintsawa tsab sannan ta fito yan gidan sunji dadin ganinta haka ai tuni kowa yakomq sabgarsa.
Abangaren Amaan kuwa suna chan Anata hotuna da hira da abokai salim kuwa ana chan an nanikewa Amrin.
Misalin karfe biyar aka zo daukan Ahlam domin zasuje ayi shirin tafiya dina.
Baba ta kasa zuwa wajen yar tata bare ta mata nasiha , Baba ne yayi dauriyar mata nasiha me ratsa jiki wanda gaba daya ya tafi da Hankalin Ahlam..
Haka Aka rike ta domin sata amota ai tuni ta bincike ta je wajen Baba tana, "Babata kizo kisamin Albarka banaso na rabu dake wallahi inasonki ni na fasa auren ki fada musu wallahi nafasa, nace miki na sake shi,na sake shi fa." Ta zube akasa tana kuka.
Baba ma sai kuka take takasa magana yan gurun kowa jiki yayi sanyi sai Baba ne yazo yadauketa chak yasata amota.
Ahlam tayi kuka ba iyaka wanda duk wanda ya gantq sai ya tausaya mata .
Gidan su Dady aka huce da ita.
Suna zuwa mama ta rungumeta tana, "Haba yata kidai na kuka ai dani da Mamanki duk daya ne kinji."
Mama ce ta rarrashi Ahlam har tayi shiru.
Su Hamlat da Mumy kuwa suna daka anata abinda aka saba basu ma san ankawo Ahlam ba sai suka ji Anata guda.
Ai tuni suka leko da suka abin ke faruwa Hamlat tayi wani tsaki tana, "Ashe kuchakar yarinyar nan aka kawo."
Mumy da Maamah suka hada baki tare da fadin, "kayan takaicI." Suka koma ciki abinsu.
Mangariba nayi duk suka yi sallah Aunty Aisha da Amrin nata dibewa Ahlam kewa har ta sake jikinta .
Amaan ya kira Amrin yabata kayan da Ahlam zata sa anjima su Amrah da zainab kuwa anata faman rawar kai kawayen Amarya.
Sai da akayi sallar isha sanan Aunty tafarawa Ahlam kwalliya.
Andau lokaci awajen yin kwalliyar nan domin ta nutsuwa ake bayan sun gamq ne Ahlam tasa kayanta pitch din doguwar riga wadda tayi ado da golden tare da dankwalinta golden takalmin ta golden da pitch karamar jakar ta ma pitch kayan ya mata dai dai kaman ajikinta aka dinka ga sarka da dankunnenta tare dq warwaraye golden da ka gani kasan Ahlam taci kudi ba karamin kyau tayi ba mara misaltuwa.
Amaan ma yashirya cikin shaddar sa pitch me dizen din golden hula ma hka tare da takalmi ya fito sak ango.
Yayin da Ahlam ta fito shima Amaan ya fito sun hadu dukan su sai dai ace masha Allah.
Ga kawaye da Abokai dasukaci ankon golden din kaya .
Gaskiya abin nasu yakayatu bazan iya ceWa kome sai dai MASHA ALLAH
Urs preety xayeesher
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
*WANNAN SHAFIN NAKUNE YAYANA DA KAWUNA HASSAN ATK,HUSAINI ATK KUYI YADDA KUKE SO DASHI INA YINKU KAMAR YADDA KUKE YINA IRIN TOTALLYN NAN*🥰
*Khaleesat haiydar agaskiya inajin dadin cmmts dinku*🥰