PAGE* 50
------------------------------------------------------------------------------------------
Da sassafe Ahlam da Nisher suka shirya tsaf domin tafiya skul dukanninsu cikin uniform me kalan blue da fari riga da sket ne sai karamin hijabi yamusu kyau sose kaman ajikinsu aka dinka.
Amaan ma yafito cikin shirinsa dan haka ba inda suka nufa sai makarantar ASIYANDA dake cikin garin kano.
Amaan ne ke tuki yayinda Ahlam take gaba Nisher ko na baya.
Amaan ya ce, "Nisher ga amana nan nabaki karki bari maza su kulata domin nasan Ahlam dina dai ba kulasu za tai ba."
Nisher ta ce, "kai yayah Amaan ba ma me kulata ai ba hade da maza muke ba iyaka mata ne kowa da bangarensu."
Amaan ya ce, "Yauwa toh yar kanwata banda kula kawayen banza dai."
Nisher ta ce, "Insha Allah br."
Ahlam ta ce, "Yayan Ahlam choculate."ta fada tana nuna masa shagon shopping.
Amaan yayi murmushi ya ce, "Daman nasani toh nasa miki ajakarki keda Nisher shiyasa nasiyo katon naba aunty ta ajiye muku."
Ahlam ta ce, "wooo Yayan Ahlam nagode."
Amaan ya ce, "Bayan godiyar kuma sai wace kalmar?"
Ahlam tayi saurin rufe fuskarta da hannu.
Nisher ta ce,"uhum fa ina nan naga kaman anmata dani."
Da sauri Amaan ya ce, "Mu mun isa ma."
Dai dai da ciga get din skul din kenan.
Amaan yasamu waje yayi paking din motar sannan yabudewa uwar sarauta Ahlam kofa. Ita kuwa Nisher tuni ta fita dama.
Ba inda suka nufa sai ofishin shugaban makaranta da hike Dadyn Nisher ya gama kome tun kan suzo basu dau lokaci ba aka kai Ahlam ajinsu Nisher Anan sukayi sallama da Amaan domin yau zai koma jos.
Ahlam taji dadin makarantar sose daga ita sai Nisher agun zamansu basa kula kowa.
Banda malamai da nisher ba wanda yasan Ahlam matar aurece tunda tashiga skul dinnan takara kama kanta domin kullum sai Amaan ya mata nasiha mai ratsa jiki hakan yasa batama laifi bare ace za adaketa duk da cewa tasan ma ba dukkanta za ayi amatsayinta na matar aure ba amman tana kiyayewa.
Akullum suna dawowa daga skul suke hucewa islamiya ba su lokaci sai dare ko ranar weekend .
Soyayya kuwa tsakanin Ahlam da Amaan karuwa ta ke akullum sai sunyi waya kusan sau biyar na safe da ban na rana da ban haka ma nadare bayan sun gama waya sai kuma akoma chart.
Ahlam dai ankara girma anzama babbar yarinya kullum da glass a ido ga kwalliya bata taba yarda tazauna batayi koda simple makeup bane.
***************
Abangaren Hamlat kuwa tana nan ta ma manta da sunan waj an mata kishiya cigaba da wulakantA Amaan sai wanda ya karu shiko baya damuwa domin inda sabo yasaba iyakaci yakira Ahlam dinsa awaya ta faranta masa.
****************** Anyi exams din first term dan haka Ahlam ta nami izinin zuwa gida gun babarta Amaaan sam yaki yarda ya ce mata ai shi yana zuwa dubasu kuma itama suna waya dan haka yace mata karta damu Shi zai zo ya ganta.
Ahlam farinciki har zuci dan haka tunda sassafe suka tashi itq da nisher Da faty me aiki sai girke girke ake ita ko Aunty Sai binsu da kallo take tana oh andai ki fadamin wa nene zai zo gashi an bade min gida da kamshi kuma nasan ba sammin za ai ba.
Nisher ta ce, "Ai ko Aunty ki ma maida yawunki domin kamshin ma kin kusa dai na ji."
Aunty ta ce, "Ahlam yata ai ke dai nasan bazakimin haka ba ko?"
Ahlam tace, "Hm Aunty bari dai naje nashirya in bakon ya rage ma sammiki."
Faty da Nisher duk suka sa dariya Aunty ta ce, "Ai duk zanyi maganinku bari mijina yadawo fita ma zamuyi."
Su dai dariyarsu suke.
Ahlam tagama shiri tSaf cikin bakar doguwar rigar tq tayi rolin din gyalen ba karamin kyau tayi ba gashi taci glashi kaman a idonta aka dasa shi .
Ta fito kenan tayi ana kwankwasa kwofa ai da gudu ta karasa .
Tana budewaaaaa.....
Urs preety Xayeesherth
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
*ALHMDLH NAFARA SAMUN SAUKI GDY NKE MASU KIRA DA MASU MSG*