KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 51

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------ *WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NEH AGAREKI SARATU TA GRP DINA KUCHAKAR KISHIYA FANS KIYI YADDA KIKESO DASH😍I*

Taga Amaan sai murmushi yake sakar mata batasan lokacin data rungumeshi ba sun fi minti biyar suna shakar numfashin juna sai da Nisher da faty suka zo Nisher tayi gyaran murya alama dai basu ji ta ba sai da ta tabo Ahlam .

Amaan yaji kunya ita ko Ahlam sai dariya take tana fadin, "Yaushe kuka zo haka ai ni na manta daku ma agidan."

Nisher tace, "Ah lallai ma bara yatafi ysn zaki sha mamaki."

Amaan dai yna tsaye yana kallon ikon Allah.

Ahlam tace, "Umm kyaji dashi nikam kinbarmin miji atsaye." taja hannun Amaan suka shige Nisher da Faty kuwa sai dariya suke suka bita abaya.

Ba inda suka nufa sai daining table ta ajiye mijinta sannan tafara zuba masa abinci .

Amaan tsabar farin ciki yakasa magana yadda yaga ana tarerayarsa.

Suko su Nisher sun koma dakin mumy suna ta hira da Mumy kafin Amaan ya gama cin abinci su fito su gesa.

Tana zuba masa tace, "Toh Yayan Ahlam inbaka ko zakaci da kanka?"

Amaan ya shagwabe fuska sannan yace, "Aa nidai Auntyn Amaan tabani abaki."

Ahlam tayi murmushi sannan tace, "Toh bude bakin."

Ahaka su ka ci abincin nan cike da soyayya da nishadi duk wanda yagansu yasan suna cikin shaukin so.

Bayan Ahlam tagama ba Amaan abinci taje ta sanar da su Mumy da Nisher .

Mumy ta fito da fara"arta tana Ah kucemin angon ne yazo shine akaki fadamin.

Amaan yanata murmushi suka gesa sannan nisher da faty ma suka geshesa daga nan kuwa aka bude fagen hira.

Amaan yaji dadin zuwansa kano sose domin yadauke masa damuwar da Ahlam ke dasa masa agida.

Sunsha luv sose domin duk su nisher basu waje suka yi misalin karfe 5 Amaan yayi shirin komawa jos domin tafiyar dare zai yi .

Ahlam batasan lokacin data fara kuka ba bataso su rabu ko kadan Da kyar ya rarrasheta sannan yabata choculate da turaren da yakawo mata sukayi sallama.

Dare ranar Ahlam takasa barci sai kiran Amaan take burinta kawai ace ya isa gida lafiya aiko sai kusan karfe 2 nadare ya isa sai lokacin tayi Hamdala sannan tasamu damar yin barci harda munshari. *KUNGA MACE TA GARI KENAN ME DAMUWA DA MIJI BA IRIN WACER KUCHAKAR BA*

washe gari

Da safe Amaan ya fito kenan yatarar da Hamlat nashirin zuwa dAkinsa.

Hamlat tace, "kai ji mana......

Urs Preety xayeesherth

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_

*SADAUKARWA GA DUK MASOYANA WA INDA NASANI DA WA INDA BANSANI BA*🥰🥰