KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 53

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

*HMM ALLAH YARABAMU DA MUGUN HALI IRIN NA HAMLAT*

Ahlam da Nisher sun dawo daga skul sun gaji dan haka suka kara yin wanka sannan su ka yi sallah su ka ci abinci.

Daddare misalin karfe ta kwas bayan sun yi sallar isha Ahlam ta shiga duniyar yaranar gizo inda ta tarar da ana program din ME AUREN YA KUNSA? awani group me suna *TSARABAR MA AURATA* wanda Aunty Aisha take gabatarwa taji Dadin program dan haka ta bada hankalinta agun inda ta hadu da zainab adamu tare real shaxee suke bata shawarwar domin Aunty Aisha ta gabatar da ita akan cewa kanwar ta ce kuma ta na da aure.

Tana jin dadin group din nan sose har Amaan ya hau suka cigaba da soyayyar me ban sha'awa domin yanzu kullum Ahlam kara kilewa take,Amaan kuwa har yafara kosawa matarsa ta dawo garesa ko dan ya huta da halin jarababbiyar nan.

Ayanzu Ahlam da Nisher suna sss3 amadarsa kuma aji biyar dan haka ta kowani fanni shirin zana jarabawa ake .

Kullum suna cikin karatu dan hakq ma yanzu Ahlam bata samu wata damar yin chart domin ga karatu madarasa ga na skul abin ya musu yawa.

Amaan kuwa sai dauki yake matarsa takusa dawowa kullum su ka yi waya sai ya tambaye ta saura kwana nawa ne su fara exams ita ko Ahlam ta ta masa dariya tana wai miyasa ya damu neh.

*******************

Abangaren su uncle salim da Amrin kuwa dankon so karuwa yake domin yanzu ma ansa biki dai dai da gama exams din su Ahlam . Hakan yasa Ahlam ma ta biyewa Amaan sai daukin dawowa take domin asha biki.

Safiyar yau asabar Amaan bai da lafiya yatashi da zazzafi sose dan haka ya kirawo Hamlat domin ta taimaka masa.

Hamlat na zuwa ta kallesa ta na, "kalau neh wai ka kira ni ina barci na katashi?"

Dakyar Amaan ya iya cewa, "ki taimaka min wallahi banda lafiya ne ko Doctor ki kirawo."

Hamlat ta zabga wani uban tsaki sannan ta ce, "Aikin banza mutum sai lalacin tsiya ai da ka kirawo kuchakar matsiyaciyar matar ka ta taimaka maka."

Amaan sai rawar sanyi yake ba damar magana .

Ta kara da ce wa , "kasani zan kira doctor amman wallahi ba abin da zan taimaka maka dashi ka mutu mah mana."

Ta juya zata fita abinta .

Ya daure yace, "Ham.... Hamlat ki ki taimaka mi ru ru ruwa."

Ta yi tsaki tana, " ka mutu mana wallahi ba abin zan baka godema zan kira doctorn."

Ta fita abinta.

Urs Preety xayeesherth.

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_