PAGE* 56
------------------------------------------------------------------------------------------
*Sarauniyar Sharhis my walida ina Alfahari dake tare da gimbiyar Sharhis My Ambeby ko da banyi niya type ba inna tuna kuna jira na fa sai naji karfin gwaiwar fara wa i really luv yhu hoo😍*
Haka soyayya ta cigaba da bunkasa tsakanin zukatan masoyan nan guda biyu wa inda kusan kullum suna tare awaya duk da basa ganin junansu hakan bai hanasu yin abinda ya kamata.
Biki sai karatowa yake yayinda jarabarwa su Ahlam sai kara raguwa take.
Yau ya kasance ranar exam din karshe askul da kuma islamiyyah.
Kamar yadda suka saba kullum kan ta tafi exam sai Amaan ya mata Addu"ah haka yakasance yau ma yq mata doguwar Addu"ah tare da fatan Sa'a.
Ba da son ransu suka rabu awayar ba sai dan kowa yaje ya ai watar da abinda ke gabansa.
Ahlam na dawowa aka fara shirya kayan komawa gida sai dauki take banda nisher waddq duk ta damu domin ta riga ta gama sabo da Ahlam da kyar Ahlam ta nuna mata ai basu rabuba ta dan kwantar mata da hankali sannan itama ta fara himmar shiri domin da ita za a bikin.
Amaan ko ya bazama kasuwa sai siye siye yake wa Ahlam.
Hamlat na gida Hankali yafara tashi domin da ashirmenta ta manta ma tana da wata kishiya sai yau da taga Daddy ya turo mutane ana gyara bangaren Ahlqm ai tuni karamar haukar Hamlat ta motsa, Dan haka tuni ta kira uwar ta suka cigaba da muguyen shirye-shiryensu har maama tazo da wasu maganin mata wai adole Hamlat tasha domin ita zata zamana amaryar ba wata kuchaka ba.
Tuni mumy ta samu Dady akan cewar sai an sauyawa Hamlat kayan Daki.
Ba musu dady ya amsa domin baya neman rigima hakan yasa akayi odar kaya daga dubai aranar ya biyo jirgin yamma aka kawo wa hamlat.
Ba abinda Hamlat take sai washe baki.
Ita ko Amrin ta na nan anata faman shirye-shirye Aunty Aisha da kanwar ta Maryam kawar Amrin din sune agaba dan ko kayan su Ahlam ma Aunty Aisha ce ta tsara kome.
Washe gari
Da sassafe Su Ahlam,Nisher,Aunty Da Dady suka dauko hanyar jos domin yau ne sa lalle kumA Daddyne waliyin Amrin so anq bukatarsa da Huri.
Hamlat kuwa antashi da gyaran gida ko gidan biki ma bata nufa ba kuma ita ba aiki take ba ta tsaya yima masu jeren iyayi tun suna kawaici har sun fara bata rai domin tsurfarta tayi yawa ahakq dai har aka gama jeren.
Amaam kuwa yana tashi ya nufi gida domin bai da burin da ya huce yaga sahibtynsa yau dan haka yayi shigar dq ta fiso wata manyan kaya ya sa glass da agogonsa yayi matukar kyau sose kamar shine angon goben.
Su Ahlam sun iso Amaan na tsaye ya zuba ido yaga fitowar Ahlam Auntyce tafara fitowa sannan daddy sai ga Nisher daga karshe.
Amaan dai yadaure yanata gesawa da mutane ammqn sai leke leke yake ta ina zai ga sahibtynsa amman ba alamarsa daga karshe dai ya ce, "Nisher wai Ahlam din fa?"
Nisher , "Tayi shiru sannan ta ce umm ai bata da lafiya mun barta agida."
Amaan ya ce ,"what?"
kan kace me har yafara zufa.
Nisher ta huce Abinta ta barsa.
Ga zufa ga jiri Amaan ya fara rikicewa har yakusa kaiwa kasa yaji anriko sa.
Urs preety xayyeesherth
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
*Yah hassan atk ysn nagaji kajo muyi type dinnan yau*🤨