PAGE* 57
------------------------------------------------------------------------------------------
*UMMU ABDALLAH TA GRP DINA K$K FANS WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE AGAREKI KIYI YADDA KIKESO DASHI*😍
Ahlam ta ce, "haba dai sahib dina kai fa gwarzo neh karka bada maza."
Amaan yayi murmushi sannan ya ce, "Umm sahibty bakisan yadda kike azuciyata bane aduk sanda naji kewarki zuciyata radadi take narasa gane meke min dadi aduniyar nan."
Ahlam tayi murmushi , "Ummm naga alamun hakan da ido na amman yanzu dai zo mushiga ciki, Kaga ina su inje inga mumynah me anjima."
Suka shiga suna yar hirarsu kadam kadan Amrin na ganin Ahlam ta tawo da gudu tana murmushi ta rungume ta tare da fadin , "Oyoyoooo er uwata ."
Gaba daya gida ya kaure da surutai ta ko ina shiko Amaan idonshi nakan Ahlam ya kasa saukesa azuciyarsa ba abinda yake fadin sai, "Masha Allah na godewa Allah da ya mallaka min wannan diyar amatsayin abokiyar rayuwa."
Ahlam anzama babbar yarinya koda mumyn Hamlat tazo ta ganta sai da ta tsorata tuni ta kira Hamlat awaya tana fadin, "Hamlat dole mutashi tsaye bakiga yadda yarinyar nan ta kara girma fa kwarjini ba hmm sai kinganta kawai kizo ynzu ina jiranki."
Tuni Hamlat ta harzuka ta bar masu aiki suka cigaba da gyaran gidan ba wanka haka ta nufo gida..
Aiko tana zuwa ta tarar da Amaan da Ahlam suna zaune afarandar su mamah .
Basu san ma tazo ba sunata hirarsu sai shekewa da dariya suke Amaan yace, "Oh lallai yanzu Matata angirma rigima ta ragu andai na cewa sai nace Aunty."
Karaf Hamlat tace, "Eh tunda yan matsiyata sun hadu atare ai dole amallake juna gaba gaba mq uwarka zaka fara ce mata."
Ahlam ta kalle ta sama da kasa sannan ta ce, "yoo ai dan hakin da ka raina shike tsole maka ido amman ki san cewa rashin mutunci ga mijinki ba abin alkairy bane zai iya kaiki ga halaka yan matsiyanta da kike gani sunfi wasu masu dukiyar wadatar zuci tare da sanin darajar dan Adam ."
taja hannun Amaan da ya tsaya kawai yana kallon ikon Allah tace, "Sahib hakuri zakayi da jahilcin wasu masu kudin muje ka kai ni gun babata nikam."
Amaan ya bita kaman rakumi da akala ita ko uwar mata ta tsaya kaman dutse awajen.
Ba inda suka Nufa sai gidan Su Ahlam da gudu ta shige tana," Babata me kumatun cincin ina kike neh?"
Baba ta fito tana fadin ,"oh Angirma ba afasa halin ba."
Amaan da Ahlam sukayi dariya atare .
Baba ma yafito yana dariya.
Ahlam ko zama vatayi ba tanufi dakinta tana za bincike agidan Amaan ne ya tsaya suka gesa sannan suka fara hira dasu baba da baaba sai da baaba ta kwallawa Ahlam kira sannan tazo.
Suka fara shan hira halin nan dai na nan na surutu sai labarin su nisher ake ba wa su baba .
Amaan ya tafi akan sai dare zai dawo ya dauki Ahlam. Aiko taji dadin hakan domin ta kara bude sabon fagen hira.
Urs preety xayeesherth.
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
_WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE AGAREKI MY KISHIYAS FATIMA ZAHRAH TARE DA DOTE MEENARLUV KUYI YADDA KUKESO DASHI INAYINKU IRIN TOTALLYN NAN😍_