KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 59

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------------------------

Misalin karfe 8 Amaan da salim suka zo daukan Ahlam.

Ahlam tuni ta murza ido zatayi kuka tare da kebe baki.

Da kyar Baaba ta shawo kanta tukun ta tashi suka tafI da nufin gobe su baban zasu zo biki ai.

Suna shiga mota Salim yasa Ahlam agaba da tsokana. Tuni Ahlam ta ware ta fara zuba.

Amaan dai sai murmushi kawai yake domin zuciyarsa fal take da farinciki.

Suna isa gida Salim ya nufi gun amaryarsa ita ko Ahlam ta makye amotar masoyinta.

Amaan yace , "Sahibty?" Ahlam tayi wani war da ido sannan tace , "Sahib ."

Sai da Amaan yaji jikinsa ba laka gaba daya ta kashe masa jiki.

ya kara da cewa, "Duk da cewa gobe zamu tare Amman inaso tun yau nabaki Amanar kai nah, Ahlam Dan Allah karki nunamin hali irin na Hamlat nabaki Amanar kai na karki wulakanta ni karki tozartani."

Ahlam, "Ta Juyo gareshi tare da rikwo hannuwansa guda biyu sannan ta sun kuyar da kanta kasa tare da fadin, "Yayanah Ai aganina nice amana agareka duk yadda ka tafiyar dani da haka zan taso kuma ina maka alkawarin cewa insha Allah baraka yi kuka dani ba azamantakewar har abada."

Ba karamin jindadi Amaan yayi da jin wannan kalman daga bakin masoyiyarsa lallai yasan yasamawa ya'yansa uwa ta gari.

Sunyi hira sose har sai da salim yazo tafiya Amrin ta rakosa sannan tace, "Toh Masoya Aunty Ahlam sai aje mama nakira ankawo kayanmu ki gwada kar sai gobe asamu matsala."

Tuni Ahlam ta fito tana, "Byee Bye Sahib inlaw na kira ma hadu awtsp."

Takarasa maganar tana tafiya.

Salim da Amrin suka shekye da dariya .

Amaan ya bata rai yana fadin, "Ina kun koran min ita kunji dadii."

Amrin tace, "Ayyah bldly wlh da gaske nake mama na kiranmu kaga nima natafi."

Tabar Salim Da Amaan.

Amaan yace, "wlh kaa kiyayeni ko gobe nafasa baka kanwata."

Salim yace, "Wane ni Ayi hakuri ai Amrin ta zama jinin jikinah kaga tafiyatq mah."

Amaan ya juya yana dariya ya shige bangaransa na gidan.

********************** Hamlat ta koma gida shiru Bataji shigowar Amaan ba ta zauna tayi shiru kamar abin tausayi haka ta kwana afalo.

WASHE GARI

Yau take ranar daurin Auren salim da Amrin tare da tarewar Ahlam agidan Amaan gaba daya gida yaciki dangi da abokan arziki anata shige da fice .

Yan daurin Aure sun halara tun kan lokaci ya cikA.

Su Aunty Aisha,Aunty Ambeby Aunty Walida,Sister,Ummu Abdallah,Hussaina,Aisha Humaira my Kishiyas fatima zahrah,zainab Adamu, Duk sun hallara musamman aunty Aisha da Ambeby suna gefen Amare sai lectures suke musu.

Ambeby ta fara da cewa bara na fara dake domin kece me babban matsala wanda inkin ssn yadda zaki bi ba wata matsla bace zai zama bakome ba da farko dai karki taba ma er uwar zamanki rashin kunya karki taba shiga harkarta inba ita tashiga taki ba dags gesuwa shikenan yawadatar .sannan abu mafi mahimmanci kinunawa mijinki so da kauna karki taba nuna masa wata damuwa akan abokiyar zamanki, nuna masa kullum ke cikin farinciki kike gyra dakinki fese shi da turare ta ko ina shi ma mjinki kulllum kan ya fita ki feshe shi da turare ,karki bare ya fita batare da kin fadamasa kalaman da ko ina yaje yana tunawa ba ki masa Addu"o"i kullum kan ya fita ,sannan in yafita yabarki da kananun kaya toh kan yadawo ki tabbatar kinsa wani launin irinsu atamfa ,gyaran jikin da na mijinki karki sawa kanki kunya zagewa zakiyi ki gyarashi kema ki gyara kanki,girki kuwa kullum kina masa kala kala mussaman abubuwan da kikasan yafi so,nunawa danginsa so kaman naki ,aganina inkika rike wannan kin gama da kome."

Anan sauran ma suka daura akan na ambeby Amrin da Ahlam sun sha nasihohi wanda dukansu sai da suka fara kuka.

Adai-dai wannan lokacin dumbin jama"ah suka sheda daurin Auren Amrin da Salim.

wayaga Salim sai washe baki yake yau yazama ango Amaan ma yasha kyau sai murmushi ake ana gesawa da mutane.

Misalin karfe 4:00 aka tafi kamu domin anaso akai kowace amarya gidanta kan 8 nadare .

Anje gurin kamu anjagije Anci ansha kowa yaje amman banda hamlat domin ita yanzu ne tafara sanin asalin zafin kishi takasa moruwa tana gida shiru .

Angama kamu lafiya daga nan aka huce da kowace amarya gidanta .

Amaan yana tare da matarsa dan Haka tare aka kaisu Nisher da Ahlam sunyi kukan rabuwa sose shiko Amaan ko ajikinsa so yake ma baki suyi su basu waje.

Hamlat tunda tsji shigowarsu ta rufe kanta adaki taki fitowa munafukar kawarta kuwa maama bata zo shiyads kadaicin ya mata yawa.

Kowa ya watse daga Amrin sai Salim haka ms abangaren Amaan daga shi sai Ahlam.

Amaan yace, "

Urs preety xayeesherth

***

🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story and Writing* *by*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_

_Wannan shafin nakine my eyman marubuciyar wata rayuwa ina tayaki murnar dawowa gida😍_ *Amin afwa a page din baya nayi mistake maimakon nasa 58 sai nasa 59 to gashi na cigaba ahakan kawai*