PAGE* 62
------------------------------------------------------------------------------------------
Tace, "Toh fah anbar tuwon dawa agida yanzu an samu na semo sai rawar kai ake."
Duk acikinsu ba wanda yadago ya kalleta bare ma ya kullata.
Data ga haka ta nufi hanyar fita.
Amaan yace, "Ina zaki da safiyar nan?"
Tajuyo sannan tace, "Gun uwata wadda tafi kowa sona domin ta ban abinci nacI."
Tana kara fada tayi ficewarta abinta.
Amaan ya kalli Ahlam ya girgiza kai kawai.
Ahlam ta rikwo hannunsa tare da fadin, "Haba nasan fa sahib dina gwarzon na mijine da ma ka iya hakuri da ita bare yanzu,please ka cire damuwar nan aranka."
Amaan yace, "Hmm Sahibty bazaki gane bane wllahi kullum halin hamlat fa kara gaba yake ba baya na rasa ya zanyi da ita ta gyara wannan muguwar dabi"ar da Mumy ke koya mata ta gane gaskiya."
Ahlam tace, "Hmm indai wannan Kama cire aranka domin ta kusa gano gaskiya indai tanasonka toh zata fara nuna kishi akanka daga nan kuma zataga ba abinda yakamata da tayi illa tama biyayya,shiyasa wani lokacin ma sai naga alamun zuwanta nake kara ma wasu abubuwan ba wai dan taji haushi bane sai dan taji kishi tayi tunanin yi maka abinda yafi hakaN.
Amaan yace, "Wooo er karama me kwakwalwar manya anya kuwa bana nemi su Auntynan naki ba daki bane labari Aunty Aisha,Aunty Ambeby,Aunty Walida dama sauransu domin nasan wannan duk darasun sune."
Ahlam ta galla masa harara tare da fadin, "Auntinane ni kadai bara kamin kwace ba eheee."
Amaan yace, "umm shine wato harda harara ta ko zan kamaki ne."
Ahlam ta tashi tana masa gwalo sannan ta shige daki da gudu tana dariya.
Amaan yataso yabita yana zaki sani inna kamaki yau ko zakamin indiancin yan rugarku.
*********************
Hamlat nazuwa bata bari dady yaganta ba ta nufi dakin Mumy ta zaiyanewA Mumy kome aiko mumy tafara surfa bala"i tana, "Ni Wallahi hamlat har kin fara bani kunya,bazakiyi kasa kasa da er matsiyantan nan ba iyee? ai wlh da kin kwara mata ruwan zafinnan ma ba iyaka yanka kadai ba maza maza kije ki kira maamah kuje gidan tare da kuma dukan tsiya bana son raini fa."
Hamlat tace, "mumy ba wani zancen duka yamzu fa ni burina kawai ta bar min gida ."
Mumy tace, "ok ga wata shawara in bata yi aiki ba ma gwada na dukan kawo kunnnenki kiji."
Hamlat tace, "Wooo mumyna shiyasa nke kara sonki wallahi kin iya kissa da kisisi na Amman kinsan miye ba yau ba sai randa kwananshi adakinta ma yakare abin zai fi sugar."
Mumy tace, "Yoo ai bakome hakan ma dabarace."
sai misalin karfe 6 takoma gida inda tA tarar da Ahlam da Amaan suna wasAn buya.
Amaan ido rufe ya fito yana , "sahibty wallahi nagaji ki fito fa inkikasa na fadi kukq zanyi wallau."
Ahlam tana ta dariya abinta.
Sai ga hamlat ta banko kwofa.
Amaan yace, "yess ysn sai nakamaki."
Juyowan da zaiyi ya chafko Hamlat....
*Urs preety xayeesheerth*
***
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
*BANCE KOME BA DOMIN NIMA SAI DA NAYI 😭*