PAGE* 64
------------------------------------------------------------------------------------------
Ahlam tace, "umm nidai ba ruwana."
Anan suka manta da zancen Hamlat suka fara hirarsu.
Wunin ranar zubur Hamlat ta kasa fitowa waje kwata-kwata.
Yau Ahlam da Amaan sun cika sati chif dan haka yau zai fara zuwa office kuma in ya dawo kwanan hamlat neh.
Amaan ya shirya zai tafi office Ahlam sai shagwaba take ita fa bataso yatafi yabarta da kyar yasamu ta hakuri ya tafi harda kukanta.
Hamlat na kallonsu tana cizan yatsa.
Amaan na fita tadau waya ta kirawo mamah . Aiko ba ayi minti talatin ba sai ga maamah ta iso .
Tana isowo Hamlat tace su shiga bangaren Ahlam.
Ahlam na ganinsu gabantA yafadi mussaman ma irin kallon da taga Maamah take yi mata hakan yakarasa mata tsoronsu ba abinda yafado mata arai sai lokacin da suka kwonata da mangyada.
Hamlat ta ce, "Ahlam wai bakiga nakawo miki bakuwa bane?"
Ahlam ta daure tadanyi murmushi sannan ta ce, "sannanku da zuwa aunty bara nakawo muku ruwa."
Hamlat ta ce, "A a ba ruwa mu ka Zo sha kinsan ba shi muka saba sha ba ruwa sai irinku."
Maamah kawai kallewa dakin kallo take azuciyarta tana, "Hmm Insha Allah ina dap da shigowa gidannan nima na mori arziki tare da samun gwarzon miji."
Hamlat ta ce, "Kawata tunanin me kike neh yakamata fa mu fara ai watar da aiki."
Maamah tuni ta mike ta nufi Ahlam tana," ke yar matsiyata kin samu guri ko , sai yadda kika yi da mijin kawata toh wallahi ina fada miki tun huri ki fita a idonmu inba haka ba zaki sha mamaki."
Ahlam sai baya baya take Hamlat na bayanta Maama na gaba .
Ahlam ta ce, "Innalillahi-wa'inna-illaihir-raji'un Dan Allah kuyi hakur.......
Bata karasa ba taji mari tassssss hamlat ma ta kara mata taaasssssss.
Gaba daya Ahlam ta gigice ta ko ina dukanta suke.
Hamlat nadukanta tana fadin"wai har er nan zata nama gwalo kuma na fada magana ta mayar min hmm yau maga bakin maganar da harshen gwalo."
Tun tana iya basu hakuri har ta daina sai numfashi kawai da take, Daga karshe ta daina numfashin.
Hamlat ta ce, "Ke Maamah ta mutu fa".
Maamah ta kara tabata taga dai ba alamun motsi.
Maamah tace kinga wallahi kuwa ta mutu toh nidai ba ruwqna sai natafi sai anjima.
Hamlat ta fara kuka tana fadin, "Maamah Dan Allah ki tsaya karki tafi ki barni."
Ko kallonta batayi ba tayi ficewarta da sauri.
Hamlat ta rasa me zatayi kawai sai kuka take.
Chan dai kawai ta dau waya ta kira Amaan awaya da dai har bazai dauka ba sai ya dauka.
Yna dauka tafara cewa, "Ahlam ta mutu wallahi bani na kashetq ba maamah ce kazo ka gani."
Amaan bai gama jin me take fada ba kawai yq katse ya hawo mota sai gida tuki kawai yake hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga ko ta kan Hamlat bai yi ba yadau Ahlam yana kuka ya nufi mota.
Cewa, "yake Ahlam dan Allah karki tafi ki barni inkika barni bazan iya rayuwa ba."
Ahaka har yakai asibiti.
suna isa likitoci suka karbeta .
Sai cewa, "yake wallahi bata mutu ba karku bare ta mutu inta mutu sai nqkashe kowa aduniyar nan."sai yasa kuka kawai
😰😰wannan page din ni kaina ya girgiza ni ba kai kadai ba Amaan.
URs preety xayyesherth
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
*Remain 5 pages to finish insha Allah*💃