PAGE* 65
------------------------------------------------------------------------------------------
*WANNAN SHAFIN NAKINE AMARYA KHADEEJAERTH AHMED MUHAMMAD DEBERSH MARUBUCIYAR BADON SHI BA ALLAH YASANYA ALKAIRY YASA ZA AYI ASA"A TARE ZURI"AH DIYYIBA😍*
Dakyar likitan yasa Amaan yadan nutsu sannnan likitan yakirawo dadyn da hike likitan familynsu ne.
Ba jimawa sai ga dady,baba,dasu mama harda ma mumy.
Ita ko Hamlat tana gida ba abinda take sai kuka tayi nadamar rayuwarta gaba daya ta rasa meke mata dadi.
Da kyar likita yasamu ceto rayuwar Ahlam amman duk da haka bata farfado ba.
Dadyne yake tambayar Amaan , "wai meya faru ne."
Amaan yace, "Dady wallahi nima bansani ba kawai hamlat ce ta kirani ta fadamin amman ga dukkan alamu dukanta tayi."
Mumy najin hakan gabanta yafadi ras aiko suka hada ido da Dady.
Mama da baba dai basa cewa kome sai Allah yakyauta.
Hamlat ce tashigo cikin asibitin tana kuka."Amaan da Ahlqm dan ALLAH kuya femin wallahi mumyce tace mu ma ma ta duka ba kasheta mukuje yi ba." Ta durkusa gabansa tana kuka mumy kuwa ta kasa sukuni.
Dady yajuyo ya kalli mumy rai abace yace, "Burinki yacika kin bata yarki da duk mugayan halayanki har ma tanaso ta fiki ke baki barni ba,baki bar yan uwa na ba Naga alama kinaso hakuri na yagaza ko toh wallahi kibarmin gida nasake ki saki daya."
Yana fada ya ficewarsa a asibityn baba nakiransa ko juyowa bai ba.
Mumy kuwa tuni itama ta zube tana, "Dan Allah ku yafemin wallahi sharrin zuciyane daga yau nabar mugun hali ku basa hakuri dan Allah."
Mamace ta dagota tare da fadin,"karki damu yanzu afusace yake shiyasa kije gidan insha Allah zamu zo mu dauke ke."
Mumy tace,"toh nagode Amman dan Allah kuzo."ta tafi tana dan kukanta.
Hamlat ma haka mama da baba suka nuna mata cewa ai bakome amman duk da haka ta kasa sakewa jikinta na dar-dar.
Sai chan anjima dady yadawo inda yayi dai-dai da farfadowar Ahlam.
Hamlat sai kuka take tana Ahlam ta yafe mata.
Ahlam tace, "Aunty ki daina kuka ai ba wanda ya huce kuskure da tsautsayi kaddara tace dole sai hakan ya faru Allah ya yafe mana duka."
Gaba daya yan gurin Ahlam kara shiga ransu sai albarka suke sa mata.
Ba jimawa aka sallamesu tare da magunguna hamlat sai rawar kai take wa Ahlam shidai Amaan bayaso kawai kawaici yake dan da iyayensa agun.
Gidan Dady suka huce duka wanda kuwa baba ne ya bukaci hakan.
Salim ma sunji dan haka suka tawo tare da amarya Amrin.
Suna zuwa gida hamlat ce me hadawa Ahlam ruwan wanka harda taimaka matA taje toilet.
Kowa abin yabasa mamaki mussaman Amrin da Amaan suda suka fi sanin rashin mutuncin Hamlat.
Aha suka kasance har safiyar ranar.
Washe gari da safe.
Baba ya hada kowa da kowa a falo yayinda ya nemi da dady yadawo da Mumy domin bai ga amfanin hakan ba halinta dai inda sabo ansaba bare yanzu da tanuna alamum nadama.
Sannan yakoma ga Amaan,Hamlat,tare da Ahlam.
Yace, "banda abince wa gareka da yahuce kanunawa matanka adalci kar ka yadda ka fifita wata awajen watq nuna musu cewa duk kaunarsu kake,Hamlat kece Babba kamata yayi ki rike girman ki kinga abaya kinbarwa Ahlam girman ke kindau kankantar wamda bai kamata ba agareki yanzu inaso ki jajirce ki fito amatsayinki ta babba agidan miji tare da masa ladabi da biyayyah,kinga ita Ahlam banda abinda zance mata sai dai Allah yayi albarka sannan in muku fatam alkairy duka,domin tana da duk abin bukata ga mata ta gari sai sai dai ince ta kara,nadawo gareka Amaan kasani cewa yanzu matanka tarbiyarsu tana hannunka duk yadda ka tafi da su haka zasu tashi fan za akiyaye."
Bakaramin jin Dadi dady yayi game da maganar baba dan haka anjima mama da shi zasu je sudawo da mumy.
Hamlat ba abinda take sai kuka domin tasan ada tayi kucha kanci.
Hamlat tace, "Nagode sose ba sai yanzu nakara sanin cewa ni ce *KUCHAKAR KISHIYA* Ba Ahlam ba."
MAma tace, "aa ya'ta karki kara kiran kanki da wannan mummunan sunan domin ada ne kike haka amman ayanzu ke kamar kowace."
Tuni Hamlat ta rumgume mama tana mama nagode da ace ke nasamu amatsayin uwa tun farko da banyi kukan yau ba.
Baba yayi murmushi yace, "toh dai isa kome ma ya huce yanZu."
Ana gama tattaunawa dady da kanshi yamaida su Amaan gida .
Sannan yazo yadau mama domin adauko mumy.
Suna zuwa gidansu mumy iyayenta suka dunga basu hakuri itama ta kara basu tare da alkawarin ta chanja hali sannan suka nufo gida.
Su Amaan kuwa baki yakasa rufuwa sai washewa yakw wai yau shine da mata biyu kuma cikin farinciki.
Ahlam taki hutu suna zuwa tashiga kichin ai tuni Hamlat ta biyota tana nima gaskiya sai kin koyamin girki.
Ahlam tayi murmushi tace, "yoo ai aunty sai ma kinfini iyawa domin kinsam tsohon hannu yafi sabO."
Hamlat tace, "Ummm nice me tsohon hannun ko zaki sani."
Aha sulayi girkinnan cike da zolayar juna Amaan najinsu sai murmushi yake.
Bayan sun gama abincin rana sunci Ahlam ta nufi bangaren hamlat ta gyarasa tsaf sannan tace to aunty aje ayi wanka kinsan fa yau oga adakin ki yake."
Hamlat tace, "umm anya kuwa nifa kunya nke ji gaskiya kawai nabar miki shi yakara sati."
Ahlam ta rike baki tarw da fadin rufamun asiri ai sai yau oga yakaini kotu wlh bawani shima so yke yazo fa."
Hamlat tace, "haba dai?"
Ahlam ta girgiZa kai.
Hamlat tace, "bara nayi bani hanya kiga har ta shiga tace karki fita fa ki jira na fito kimin kwalliya."
Ahlam tayi murmushi ta jirata ta fito sannam ta dauko mata sabuwar abaya tasa ta mata daurin chakwai tare da simple make up dinta .
Hamlat ita kanta tasan tayi kyau sose kawai godiya tkewa Ahlam.
Ahlam tace, "yauwa toh aunty zauna yqnzu oga zai iso bara na fada masa munshirya."
Hamlat kawai murmushi tke domin ko ran aurensu batayi farinciki irin na yau ba.
Ahlam na fita taje ta durkusa gaban Amaan tana, "Kayi hakuri bansan ko na aikata abinda bai kamata ba agunka amman aguna dai dai-dai ne yau zaka koma dakN Auntyna Na fada matq kuma ta shirya kawai kai take jira."
Amaan yayi shiru yarasa mema zai cewa Ahlam .
kaji yaya plsss dan ni zakayi .
Amaan yace, "shikenan naji kuma nagode Allah yamiki albarka sahibty er aljannah."
Ahlam tayi murmushi ta riko hannuna tashi muje.
Amaan yatashi suna zuwa kwofar daki tasake shi ta kwankwasa sannan ta juyo da gudu domin tafiya dakinta hawaye ne fal a idonta kuma bataso Amaan yagani bare yadamu.
Dn Haka tana shiga ta fada kan gado tana kuka.
Shiko Amaan yashiga da sallamarsa...
*Preety xayeesherth*
***
***
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬 *KUCHAKAR KISHIYA* 🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_