PAGE* 66,67&68
------------------------------------------------------------------------------------------
*SADAUKARWA GA DUK MASOYAN HAMLAT*
Amaan yayi mamakin ganin Hamlat awannan yanayi hakan yasa kawai ya tsaya yana kallon ta,bai san cewa Hamlat kyakkyawa bace sai yau.
Hamlat tayi murmushi tare da kara sowa garesa da murmushinta ta ce, "Ayyah yayanah nasan dole zakaji wani iri yanayin da baka saba gani na ashi ba amman inaso kasancewa da , da yanzu ba daya bane."
Ta durkusa agabansa tare da riko hannunsa ta ci gaba da ce wa, "Dan Allah kayafemin ina me maka alkawarin cewa bazan taba komawa Hamlat din da ba yanzu A Amina ta nake Insha Allah baraka kara kuka dani ba ko na second daya."
Ta matukar ba Amaan tausayi mussaman da yaga hawayen da take zubarwa har yaji yamanta da rayuwarsu ada.
Hakan yasa yadago ta tare da share mata hawa ya rungumeta yana fadin, "Ai koda ace ke ba matata bace ke jininace bazan taba kinki ba Hamlat."
Ahaka suka kasance asabuwar rayuwa adaren ranar.
Ahlam tasha kukanta har ta gaji hakan yasa ta tashi ta dauro alwala tayi sallah sannan ta karanta Alqur'ani agurin barci yadauke.
Da asuba kuwa Amaan yazo ya kwankwsa mata kwofa ta tashi tayi sallah bayan ta idar bata koma barci ba ta gyara dakinta tsaf sannan ta nufi kichin.
Breakfast taje hada musu soyayyar doya tare da miyar kwai sannan ta musu farfesun kifi.
Tana gamawa ta shirya su tsaf akan dainin aiko ta gama shiryawa kenan sai kasu sun fito da murmushinsu.
Ahlam ta kasa hada ido da Amaan kawai murmushin dole take tace, "morning sahib and Auntyna."
Hamlat tace, "morning sister."
Amaan ya ce, "wai me gimbiyar ta shirya mana ne naji gidan duk ya dume da kamshi."
Ahlam tayi murmushi tare da fadin, "Umm kuzo muyi karya nidai inason nasha tea."
Tuni Amaan da Hamlat suka zo na.
Hamlat tace, "toh sister tunda ke kika girka ai kya bari ni yi saving din kinga anraba ladan."
Ahlam tace, "As u wish Auntynah."
Haka suka kasance cikin farinciki da begen juna hakan ya hana Amaan fita ko kwofar gida bare yaje office hamlat kuwa tadau hutun wata guda daman domin ta zauna Ahlam ta koya mata girki da gyaran jiki.
Ya kasance akullum yana cikin farin ciki da iyalansa har in yana office kullum burinsa kawai yadawo yatarar da gimbiyarsa Ahlam, Duk da cewa Hamlat ma tafara shiga ransa Amaan ba kamar Sahibtynsa ba.
Yau yakasance ranar asabar Amaan bai je aiki ba kuma adakin Ahlam yake hakan yasa Hamlat ta nemi alfarmar fita. Amaan ko ya yarje mata domin kuwa intana gidan baya iya bajewa sahibtynsa asalin so da kaunar da yake mata domin gudun kar ta shiga damuwa.
Ba inda Hamlat ta nufa sai gidan su Maamah tana zuwa bata karasa shiga ba taji Mumyn Maamah na cewa, "Wai niko kwana biyu ina Hamlat neh."
Ai tuni hamlat ta tsaya chak.
Maamah tace, "Mumy ina zaki ga wannan matsiyaciyar ta nan ta kusa kisa,ai ni wallahi kawai ina daga mata kafa ne amman sai na auri Amaan domin tun randa nafara ganinsa nakamu da sonsa fatana kawai boko jum yadawo daga nema min maganin da yaje na aure abi nah."
Mumyn Maama tace, "Subhannallah wannan lamarin abun kunyan tare da shirka ba agidannan ba wallahi."
Hamlat ta rasa ta cewa sai yanzu abubuwa suke dawo mata daman ashe Maamah bason tsakani da Allah take mata ba?.
Ba ma bari tagama jin me suke fada ba tashige dakin tare da cewa, "Nagode da hallacin da kikamin Maamah kuma wallahi indai Amaan ne yafi karfinki sanin kanki neh."
Mamah tace, "mtswww aikin banza to se me?"
Hamlat ta yi murmushi sannan ta cewa mumy"mumy nagode da irin nasihar da kikemin da kuma nagyara hali Allah ya saka da Alkairi."
Tayi ficewar tah.
Bakaramin mamaki Hamlat taji bq hakan nr ma yasa ta kira mumy ta fada matA.
Mumy tace, "hmm Hamlat kenan ai gwada kema kingane da huri niko ina tare da makiyata kuma er uwata taji kusan shekara talatin da wani abu tana sani yin mummunan aiki ai kawai sai dai muce Allah ya yafe mana."
Hamlat tace, "Amin kam".
Suna gama wayar kuwa tayi gida.
Rayuwa ta cigaba da dadi agidan Amaan domin kuwa dukansu sunq bawa junansu kulawa yanzu har kwatance ake dasu domin hadin kansu tare da zaman lafiyansu.
Har yakasance duk inda zasu tare suke zuwa sai kuma an nemawa Ahlam admission a universty of jos tana digirin ta afannin computer science Hamlat kuma ta cigaba da zuwa gun aikinta.
Yau yakasance ranar monday kuma Amaan yanq dakin Ahlam tunda ya bugawa Hamlat daki da asuba bai koma ba dan hakq bai sani bsma ko ta tashi.
Har sungama shiri bata fito ba hakan yaSa Amaan yakara bugawa yaji shiru da karshe dai sai keyn gunsa yadauko yq bude dakin .
Hamlat kwance zazzabi ya riketa rawar sanyi kawai take.
Tuni Amaan ya kira doctor ba jimawa yazo.
Ya ma Hamlat gwaje gwaje alamu suka nuna cewa tana dauke da ciki wata biyu.
Ai ba wanda yakai Ahlam murna kin tafiya skul tayi ita zata kula da unborn babynsu .
Amaan ma yayi farinciki sose amman azuciya ynq fatan ganin jininsama daga bangaren Ahlam.
Hamlat kawai murmushi take.
Daga ranar kuwa kullum Hamlat sai sunyi fada Da Ahlam akan aikin gida . Hamlat tace ai sai tayi , Ita ko Ahlam tq ce wallahi bazaki wahalar mana da baby ba kije ki hutA.
Amman duk da hakA Hamlat ba yarda sai tayi aikinnan bata bari ma Ahlam tazo ta tarar da aiki domin tasan farincikin Ahlam shine na Amaan shiyasa kullum koda bata jin dadin jikinta ta gwammace ta ta aiki dan kawai tasa mijintq farinciki.
Akullum in suna zaune ana hira sai Ahlam tace, "Auntynah karfa kizo kina min rowar babynmu domin aguna zai na huni sai barci da shan nono zai na kawoshi gunki."
Hamlat tayi murmushi sannan tace, "Ai babyn ma naki ne Ahlam bansan ran zan rani da ko yar da zan hafe ba."
Amaan ko yakance kullum dai maganar ku kenan.
Watan haihuwar Hamlat yakama kullum karatun Alqur'ani take tare da addu"o"in samu rahama .
Inko ana hira bata da abin fadan da yahuce yayana ka yafemin kanwata kema ki yafe min domin bansan ko zan tashi .
Tun Amaan da Ahlam suna maida abin wasa har sai yafara basu haushi.
Amaan yace, "indai ba so kike ki tarwaatsa mana farin ciki ba kidai na kawo mana zancen kina ganin zaki barmu."
Hamlat tayi murmushi sannan tace, "nabari insha Allah yayanah."
Ahlam tace, "yauwa auntyna me kumatun cincin."
Dukamsu sai da suka yi dariya mussaman hamlat.
yau hamlat ta tashi da ciwon nakuda Amaan taki fadawa kowa agidan har Amaan yatafi office Ahlam ma ta tafi skul.
Har ta dafa ruwan zafi. nakuda tazo gadan dagan aiko ba bata lokaci ta haihu alokacin haka ta daure ta yankewa dan ta cibiya ta masa wanka da ruwan da ta dafa sannan ita ma tama kanta.
Ta kwanta tana hutuwa kennan ciwo yadawo mata sabo Jini yabarke.
Da kyar tasamu damar janyo waya ta kira Amaan awaya.
Tama kasa magana duk jikinta ya mutu cewa take, "Kazo gida zan mutu kazo yaYa."
Da sauri Amaan ya katse wayar ya tawo gida .
Yana zuwa yatarar da yaro sai kuka yake ita ko Hamlat asume.
Da sauri yakira me gadi yarike masa yaron ita kuma yasa ta amota suna zuwa aka karbeta emergency.
Amaan ya kira gida yasanar musu duk sun hallara a asibitn Ahlam ma ta iso.
Hamlat na farfadowa ta sa akira mata Ahlam da Amaan da gudun su suka shiga .
Suna Zuwa Hamlat tace, "Sister,Yayanah kuyi hakuri nasan bazan rayu ba amman ina so kafin nabar duniya kace kana so na ban taba jin wannan kalmar ta ka gareni ba."
Amaan na kuKa Ahlam na kuka Amaan, "Ina sonki Hamlat wallahi ina sonki dan Allah karki tafi ki barmu wallahi duk muna sonki."
Hamlat ta rikye hannunsa da na Ahl am tace, "Umm yayana na gode amman ina neman alfarmar karshe kasawa yarona sunanka domin inaso yayo hali irin naka indai yayi nasan bazai taba shan wahala ba arayuwarsa ke kuma Sister ga danki nan nasan zaki rike shi kaman danki na cikinki,ina Alfahari daku Amine na kuma yan uwa na duka ina sonku."
Amaan yakasa magana Ahlam ce tadaure tace , "Dan Allah Aunty kibar fadan haka karki barmu plssssss."
Hamlat ba abinda yake futuwa daga bakinta sai kalmar shahada.
Atake Allah yadau Abinsa.
*INNALILLAHI-WA"INNA-ILLAIHIR-RAJI"UN* Abinda Amaan yake firtawa kenan.
Ita ko Ahlam itama atake ta suma awajen.
Gaba daya dangi sun shigo sai kuka kawai ake.
Urs preety xayeesherth
***
π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬ *KUCHAKAR KISHIYA* π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬π₯¬
*ZAMANI WRITERS ASSOCATIONπ€π»* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story and Writing* *by*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_
ππππππππππππππππππ