PAGE* 69,70
------------------------------------------------------------------------------------------
Amaan yaga Matukar tashin hankali awannan ranar domin ita kanta Ahlam sai dare aka samu kanta.
Tunda ta farka kuwa ta kankame Little Amaan ahannunta taki ba kowa ko sallah zatayi sai da ta goyasa.
Akullum Ahlam na cikin kuka Amaan ne yake dauriya har ya mata nasiha akan cewa yanzu ba abinda Hamlat ke bukata agun mu illa Addu'ah .
Yau Hamlat tacika kwana uku da rasuwa dan haka duk mutane sun tafi Ahlam da Amaan ma sun koma gida.
Ba karamar kulawa little Amaan yake samu ba awajen Ahlam baya fin mintuna sai anbasa madarasa da kuma ruwan dume tare da gulukos.
Yau Hamlat ta cika kwana bakwai da rasuwa kuma sunan little Amaan ba ayi taron suna ba anma anyi sadakawa mutane sose Dadyne ya radawa little Amaan suna.
Ahlam dai ta fara sakewa Amman ta kasa sabo da rashin hamlat kwata-kwata.
Little Amaan sai girma yake duk wanda yagansa kaman yaga Hamlat domin kamansu daya sak.
Yaron yakasance me gwarjini a idon mutane gashi ko yaushe cikin murmushi yake hakan yake karasa shi shiga zukatan mutane da dama.
Soyayya ta kara karfafa atsakanin Amaan da Ahlam.
Litte Amaan nada shekara biyu Ahlam tasamu ciki,duk da cewa tana shan wahalar cikin amman hakan bai hanata dawainiya da Little Amaan ba kullum burinta taga die heart dinta kusa da ita sunnan da take kiransa dashi kenan hakan yasa kowa ma yake ce masa die heart.
Ahlam ta haifi yarta mace wacce taci sunan Hamlat Wato Amina Amman Da Hamlat dinta ake kiranta.
Dady da mumy kuwa suna nunawa takwarar yar su so sose mara misaltuwa domin acewarsu ita hamlat dinsu ce.
************ Bayan shekara biyar Muka kara lekawa gidan Amaan .
Ahlam ta kammala karatun ta har tayi bautar kasa amman bata aiki ita tace kula da ya'yanta zatayi hakan kuwa Yama Amaan dadi.
Little Amaan na primary one hamlat kuwa na nusery 1.
Hamlat ce ta tawo da gudu tana," Ammi nah kinga Yaya Ko ?"
Ahlam tace, "Me ya faru neh die heart ya kasa kanwarka kuka."
die heart ya ce, "Umm Ammi wai fa take cewa me kumatun cincin shine nikuma nace ita kumatun alale ne da ita."
Ahlam ta kalli Amaan,Amaan ya kalle ta aiko sai sukq sa dariya dukansu.
Amaan yace, "yan Albarka sunyi Halin Ammin su kunga kuzo na kai ku skul karku yi letti."
*ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH NAGODEWA ALLAH DAYA BANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA ALLAH YASA ANDAU DARASIN DAKE CIKI NA ALKAIRI WANDA NAYI BA DAIDAI BA ALLAH KA YAFEMIN DUK WANDA NABATAWA RAI SANADIN WANNAN LITTAFI YA YAFEMIN DOMIN DAN ADAM AJIZI NE*
FATAN MASOYA NA ZASU TSIMAYI SABON LITTAFINA WANDA YKE KAN HANYA.
Shin wani darasi kika dauka akan littafin nan?
dame kika karu?
Me yafi baki dariya?
Wace shawara kikeson bani?
shin me yafi baki tausayi?
Me yafi baki haushi?
Ina bukatar wannan amsoshin daga gareku masoyana
Wtsp me or call me Wit dis nO ***
Urs preety xayyesherth.