22
Chapter 22
Tafe suke a gaje liƙis sun ɗebo zafin rana, dawowar su kenan daga duba wani gida da aka kwatanta ma Ammie suka je duba sa sai dai tsaran gidan bai yi dai dai da ra'ayinsu ba, area bata da tsaro haka zalika a na wahalar samun ruwa amma yanaye da tsaruwan gidan ya yi babu laif, kawai matsalar ruwa da rashin tsaron ne.
A gaje Nazli ta ɗago fuska a ɗan yamutse saboda zafin rana ta ce. "Ammie bari na karɓo mana ruwa a wajen mai kantin can." Ba ta jira me Ammie za ta ce ta tsallaka titi, Ammie ta ja gauron numfashi ta sauke ta waiwayo baya ganin baƙar motar da ke bibiyarsu a baya tun fitarsu. Ta lura da hakan ne tun safe da suka bar gida da su aka yi yawon neman gidan duk juyawar da za ta yi sai ta gansu.
sai dai bata gaskata zargin na ta ba sai yanzu da suka tsaya ta ga motar ma ta tsaya. Gaban ta ne ya faɗi ta soma jero adduo'i da neman tsari ga dukkan wanda ke bibiyar su da sharri, bata raba ɗayan biyu kodai ɓarayi masu bibiyar mutane su san muhallin su su kai masu farmaki da dare ko kuma yan garkuwa da mutane ne a yadda duniyar nan ta zama babu yadda.
Gaban ta sai faɗuwa ya ke tana ta anbatan sunan Allah a ƙasan zuciyarta, tana nan tsaye a wurin har Nazli ta siya ruwan ta zo tsallaka titi dukkanin su ba su ankara ba sai gani suka yi motar ta yi reverse ta yi kanta da mugun gudu, a matuƙar zafin nama Ammie ta finciko hannunta ta yi baya da ita ta yi taga taga kamar za ta fadi cikin kwata dan har kafarta ta gwauce ledan ruwan hannunta ya fadi pure water da cingam da da siya duk ya watse a wurin. Take kuwa mutanen wurin suka yo caa a na a tsaida me mota amma ina ya riga da ya yi masu nisa bai ko tsaya ba ya ƙara karfin gudun sa ya bar wajen.
Hannu biyu Ammie ta saka ta riƙo Nazli tare da tambayar ta ko ta ji ciwo ta ce a'a, amma idanunta a kan motar har ta ɓacewa ganin ta zuciyarta sai tsananta faɗuwa take, ta tuna yadda kwananki ma haka a ka kusan bige ta ta faɗa a cikin kwalbati ta sha ruwan ƙazanta, bata raba ɗayan biyu mutanen nan da ke bibiyar raywarta ne, wanda ta rasa me ta tsare masu ita ba sanin su ta yi ba bare ta san me suke sonta da shi.
Jin muryar Ammie ta yi tana faɗin. "Ni wallahi tun ɗazu hankalina bai kwanta da motar nan ba, a jikina na ke jin ba alkhairi bane tunda muka fita na lura da a ita baya." Ita dai ba bakin magana gaba ɗaya hankalin ta ya lula kan abubuwan da ke faruwa da ita a wannan tseku, duk nazari da tunanin ta bata san me ta tarewa kowa da abubuwan nan da ke ta faruwa duk da bata son yarda hakan amma zuciyarta na tabbatar mata da saka hannu cikin lamarin sai da bata su wa?
Ƴan samarin wajen suka taya su haɗa kayan su da ya watse da ban bakin haƙuri suka kama hanya yayin da kowa ke allah wadai da wasu matunen, na yadda ya kusa kaɗe mutum amma ko a jikinsa sai ma ƙara motarsa wuta da ya yi ba tunanin ya tsaya ya ga ko ya ji ma wani ciwo.
Gaba ɗaya sukuku suka dawo gida kowa rai ba daɗi, ga abin da suka je nema basu samu ba ban da zafin rana da suka ɗeboo ga kuma abin da ya so afkuwa Allah ya tsare.
========
Da dare suna zaune a tsakar gidan na su sun yi shinfiɗa a nan waje kasancewar garin da zafi zaman ɗaki bai zaunuwa, Nazli ta ɗan nisa ta ce. "Ammie na ce me zai hana na yi wa Hajiyar da na ke wa aiki magana kan batun wajen zama kafin lokacin da Allah zai yi?" Kin ga dai har yanzu shiru kuma wa'adin da suka bada ya kusa cika amma har yanzu babu tsayayyan gida muka samu idan har za su amince mu koma can ɗin da zama na ɗan wani lokaci, tunda dama ita hajiyar ta so haka daga gare ni tun baya amma ban bada fuskar haka ba"
Ammie ta yi shiru tana nazari. "Kina ganin hakan zai yu ba za'a samu matsala ba?" "In sha Allah Ammie, dama tuntuni ta buƙaci hakan ni din ce ban amince ba kuma ma zaman na mu na dan lokaci ne ai da mun samu gida zamu koma can."
======
Kamar yadda Nazli ta ƙudirta washe gari da ta je aiki ta samu Hajiya Binta da ƙudirinta inda ta aminci nan take dan dama ta so hakan bayan gindaya da kuma jaddada mata dokokin ta tamkar na wancan karon.
A ranar ta sanar da Ammie suka fara haɗa kayan su, a yadda suka tsara da basu wani haɗa tarkace ba daga kayan sawarsu sai ƴan abubuwan da ba za'a rasa ba, sauran kuma a gidan Ture za'a su barshi har zuwa ranar da za su samu gidan haya su kama kana su kwashe. Cikin kwana biyu suka gama hada komai na su a ka saka cikin baro a ka kai gidan Turai, ya rage daga su sai katifa da kayan sawan su wanda da shi za su koma gidan Alhaji Badamsi.
A ranar ne kuma Maman Kadija suka bar gidan suka koma bayan layi inda suka samu gida, Maman Sadiq kuma a washe garin ranar za su tashi Amarya kuwa tun satin da ya gabata suka tashi ta bi mijinta wurin aikainsa, sai ya saura daga su Ammie sai Maman Sadiq ya rage a gidan.
A na washe garin ranar da za su koma gidan Alhaji Badamsi da zama Nazli ta yi sallama da Ammie kan zuwa aiki, tana fita ta tsaida adaidaita ta yi masa kwatancen ya ja suka yi gaba. Tafiya suka yi mai nisan zango, tun suna tafiya tana kallon hanya har ta soma gangaɗi.
Kasancewar shata ta ɗauke mai napep din ya sa ko tsayawa bai ba har suka isa anguwar da ta sauke tare da buɗe jakar hannunta ta irga kuɗi ta basa, ta tsaye a gaban estate ɗin wurin tana tariyo abubuwa da dama da suka shude.
Hannu ta sa ta gyara zaman nikab din ta da kyau ta yadda ba wanda zai waye ta kana ta nufi estate, a bakin gate security suka tsaida ita amma koda ta fada masu wanda ta zo nema sai suka bata hanya ta wuce.
Tun daga nesa ta ke kallon gate din na su take jin emotions da dama na tasu mata, sai take jin kamar ta nufi wurin ta kwankwasa mai gadi ya buɗe gate ta shiga ba tare shamaki ko wani ko tuhuma. Sai dai kash! Ta sani a yanzu gidan ya fi karfin ta, sai dai gani daga nesa sun mata nesan da duk gudun ta da kokarin ta ba za ta cimma masu. Ta zame musu bare, sun kuma zamo kallo daga nesa, sun rufe babin ta tare da rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kamar ba'a taɓa yin mai kama da it ba a cikin su. Sun daura rayuwar su daga inda suka tsaya yayin da ita ke cikin kewa da begen su a kullum, sun zame mata tamkar taurari a sararin samaniya bata isa ta zo gare su ba.
Hawaye masu ɗumi ne suka sukar mata a fuska, bata saka hannu ta goge ba sai ma neman wuri da ta yi a kasan bishiyar da dan nesa da gidan ta zauna ta cigaba da kallon gate din tana jiran ganin wani daga ciki ya fito ta gani ko hakan zai sanyaya mata zuciya kadan musamman Daddy ta da take kwana take tashi da shi a ranta.
Shin ya za su ji idan suka ganta? Shin za su yi farin cikin ganinta? Ko kuwa sun riga da sun rufe babin ta kamar yadda Daddy ya furta, nade kanta ta yi ta hada kai da guiwa tare da lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya, ga fuskar nan da ta yi shabe shabe nikab da ke fuskar ta kuwa ya jiƙe sharkab da ruwan hawaye. tana cikin kewa, kewan Abban ta, kewar da ta fi ko wacce. So take ta ji duminsa, ya lallashi ta ya fada mata mafarki take ba, ya fada komai zai daidata ya share mata hawaye.
Murya a shake saboda kuka ta furta. "Me ya sa?" Why Daddy, you of all people ka gasa fahimta ta ka ka san abin da zan yi da wanda ba zan aikata ba, me ya sa ka biyewa dokin fushi har ka iya korar yarka ta fice maka da gida." Ta ja numfashi tare da kai duban ta kan gate din gidan. "Na dauka ko da kashe mutum na yi a ka zo hukunta ni to kai me kare ni ne da dukan karfin ka Daddy. Ta yi murmushi mai ciwo da ya ke bayyana irin hargitsin da zuciyarta ke ciki.
Me ya sa ka kasa fahimtar ta a wannan karon kan laifin da bata san hawan sa ba? Laifin da ko wuka za'a daura mata bata san ya hakan ta faru ba, ita kan ta har yanzu tana cikin rudun da tunanin abin da ya faru a wannan daren amma duk yadda ta yi tunani da nazari ta kasa tuna komai abin da za ta iya tunowa shi ne ta shi kawai ta ganta cikin daki tsirara da kuma alamun kasamcewa da wani namaji ba mijin auren ta ba.
*Zaid." Ta furta sunan a hanakli yayin da take jin yadda sunan ya yi mata ɗaci a baki, gabaki daya sai kuma ta soma tariyo komai da ya faru a rayuwarta tun tasowarta da girmanta ta har zuwa yau da take cikin wannan halin, sai kifa kanta ta soma rere wani sabon kukun.
Cikin fitan hayyaci ta ke furta "Ban aikata ba, ku yarda da ni ban aikata ba ban aikata abun da kuke zargina da shi ba." Tun tana kukan a hankali har ya soma fitowa fili, kasancewar anguwar estate ce ya sa ba mutane sosai babu wanda ya lura da zaman ta a wurin bare wani ya tanka ta.
Idan har da zuciyar imani a kirjin ka to a wannan lokacin sai ka tausayawa Nazli, sosai take kuka tana tuna maraicinta. Tana tuna da ace mahaiffiyar ta na raye da ba ta gayyara har haka ba, da duk abin da zai faru ta sani ita din ba za ta guje ta ba. Uwa mai dadi, a duk tsawon rayuwarta bata taba jin ta ji kewar mahaifiyyarta daidai da second daya ba, Mommy ta maye mata gurbin Uwa da komai da uwa za ta baiwa danta a yau sai ta ji duk duniya bata muradi da ta ganta a jikin mahaifiyyarta. Dama masu iya magana suka ce gurbin ido ba ido bane, to ita ta tabbatar da wannan hausar.
Ba za ta iya irga iya adadin lokuta da ta dauka a wurin ba sai da rana ta fadi yamma ta yi kan ta farga, kuma har zuwa lokacin bata ga koda inuwar yan gidan bata san suna can kasar Switzerland sun lula duniyar bude ido tare Neesah da angon ta Zaidu.
======
Ita dai bata san ya a ka yi ba, tsintar kanta ta yi a bakin titi, bata bi ta kan yan machina da ke mata tayin tafiya ce? a wannan lokacin da za ka tsare ta ka tambaye ta inda ta za ta to bata sani ba.
Kawai burin ta a wannan lokacin ta samu lokaci, ta kaɗaici daga ita sai tunanin ta. A wannan halin aka zuk'e da ruwan sama kamar da bakin kwarya.
A yayin da kowa ke gudu da neman mafaka, ita sai hakan ya yi mata dadi ta yadda za ta sharɓi kuka ba tare da kowa ya gane ko fahimta ba, yadda take kukun sai ya sanyaya mata zuciya, ta amayar da dukkan ƙunci dake zuciyarta.
Duk yawan ruwan nan a kanta ya ƙare, jikin ta sai karma ya ke ga sanyi da take ji na shigarta har ƙasusuwan ta, jin ta take a sama kanta na juya mata. Sai a lokaci ta nemi abun hawa ta nufi gida, koda suka zo sauka ta yi ta nufi cikin gida mai adaidaita ya tsaida ita. "Ke ya haka kudin nawa fa?" Sai a lokacin ta tuna da wai fa za ta basa kuɗi, hannu ta kai Jakarta da ke rataye a kafaɗarta ta ga wayam jaka ta ce dauke ni inda kika rataye ni. Cikin dishashshiyar muryata dake mayyana kalan kuka da sha ta ce. "Ka yi haƙuri bari na shiga na dauko maka." Daga haka ta yi ciki yayin da mai adaidaita sahun na guna guni kan cewa an tsaida shi za'a ɓata masa lokaci.
Ammie ce tsaye a farfajiyar gida da Maman Sadiq cikin tashin hankalin rashin ganin Nazli har wannan lokaci bayan sun yi da ita mata ba daɗewa za ta yi ba kakari bayan azahar za ta dawo, amma gashi ana neman isha'i shiru babu ita ba labarin ta, hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba jin layinta ma bai shiga. Gaba ɗaya ta rasa abin da ke yi mata daɗi fatan ta ba wa su mugayen ne suka tsaida ita da niyyar cutarwa, da tuna abin da ya faru ranar sai hankalinta ya ƙara tashi.
Shi ya sa ta fito waje inda su ke sake maimaita lamarin da Maman Sadiq inda Ammie ke faɗa mata za ta je nemo ta idan ta kama za ta je wurin Turai ta kai ta har shi gidan Alhaji Badamasi ta ji ko shi ya hana ta z
dawowa. "Ko mu ɗan jira kaɗan mu gani ne kar kuma da fitar mu ta dawo a yi saɓanin hanya?" Faɗin Maman Sadiq yayin da take saɓa ɗanta ɗan wata shida a baya. "Ke dai bari Hafsah ke ɗin ki zauna ko dan yaran nan ba zai yu duk mu fita a bar yara su kaɗai ba, ni ɗin ce da ya zamar min dole zan je na dubo." Cewar Ammie, Maman Sadiq za ta yi magana sai ga Nazli.
Salati Ammie ta suma tana tafa hanayen ta yi matuƙar kaɗuwa da ganin Nazli a wannan yanaye. "Nazli! Hafsa gane min wannan lamari Nazli ce ko ko idanuna ke gani mini?" "Ita ɗin ce ba ba gizo take miki ba." Maman Sadiq ta fada itama cike da mamaki da ya gaza bayyana a fuskar ta itama.....