FA'EEZAH

Destiny Draws Them Closer

by @zeeyluv

Page 4:


Sai bayan la'asr su ka yi  haramar tafiya gida. Zuwa ta yi ta zauna kusa da Hajiya ta ce, "Hajiya zamu tafi, me za ki bani na tafi na yi guzurrin zuwa makaranta? 


Banza haijyar ta yi mata kamar bata ji abin da ta ce ba. Ganin haka ya sa Fa'eezah faɗin, "Hajiya magana fa na ke yi miki kika share ni ko da ya ke ai dama ba sona ki ke yi ba shikenan. Amma ni dai don Allah ko ya ya ne ki ɗan haɗo min wani abu bari na je kitchen ma sha ruwa kafin na dawo kin haɗa. 


Miƙawa Asmy hand bag ɗinta ta yi tare da veil ɗinta tace riƙe min ina zuwa. Asmy ta ce , "Ai kuwa sai dai ki same ni a waje don ba zan iya da wannan ɗan banzan jan jikin na ki ba." Ta na gama faɗin haka tayi waje abinta. Fa'eezah kuwa a ranta ta ce, "Kin sauƙaƙa mini aiki ne yarinya." 


Kitchen ta nufa kai tsaye inda tayi ajiya ɗazu da ta shigo kitchen ɗin ta nufa. Wani ɗan ƙaramin bucket mai murfi ta ɗakko haɗe da farin robar takeaway wanda ya ke cike makil da haɗadɗiyar yajin tafarnuwa da ya ji kayan kamshi. buɗe bucket ɗin ta yi. Cike ya ke da dambun nama a ciki mai rai da lafiya. Saka robar yajin ta yi a cikin bucket ɗin dambun namar, sannan ta nufa parlour ta na faɗin,  


"Hajiya ki bar kuɗinki kawai na yafe. Na sauƙaƙa miki zan yi manage da wannan." 


Ta buɗe robar ta na nuna mata. Dama ta riga ta saita hanyar fitarta ko da ta kwaɓe mata. Zare ido Hajiya ta yi, cikin masifa ta miƙe ta yo kanta ta na faɗin, 


"Zan ci mutuncinki idan ba ki koma kin ajiyemin ba tunda ba uwarki ta kawomin ba. Shegiyar yarinya dangin jarababbu."  


A saba'in Fa'eezah ta kwasa a guje ta yi waje haɗe da faɗin, 


"Danginki kenan ko Hajiya." 


Cikin ɗaga murya yadda Hajiyar za ta ji ta dawo ganin Hajiyar ta koma ciki ta ce, 


"Ai wallahi uwata da ta na raye da ba ƙaramin daɗi za ki ji ba, don na tabbata da mai capacity za ta dinga yi miki ba irin waɗannan jagwalgwalon ba. Ke da za ki gode min ma da kika samu na ɗauka zan rage miki tarikice."


Ta ci gaba da faɗin,


"Nima ba ni zan ci ba, almajirai zan ba wa idan na fita, kar ma ki yi tunanin ni zan ci wannan trash ɗin."


Ƙwafa Hajiya ta yi ta ce , 


"Ba ga irin ta nan ba. Wannan yaro ya je ya auro mana dangin matsiyata, ga shi nan matar ta haifa mana alaƙaƙai ta mutu ta bar mu da ita."


Ɗakin Baban cikin gida ta nufa inda ta iske Asmy na jiranta a wajen. Sallama su ka yi masa a kan jibi za su koma makaranta. Bai bar su haka ba sai da ya sallamesu da kayan makulashe kasancewarsa mutum ne mai yawan kyauta. 


Koda su ka isa unguwarsu gidansu Asmy su ka yaɗa zango. Umma na ta shirin haɗa abincin dare su ka yi sallama. Nan su ka karɓeta su ka ƙarasa. Saboda dukda kasancewar Fa'eezah ƴar gata hakan bai hanata zagewa ta koya girki ba saboda girki ya na ɗaya daga cikin Hobby ɗinta. 


Bayan sun kammala girkin su ka je su ka yi sallah. Su na idarwa su ka hau yin tilawar alqur'ani tq hanyar yin musaffa a tsakaninsu. Sai bayan sallar isha sannan su ka fito cin abinci lokacin kuma yaya Abdallah ya dawo daga wajen aiki (Yayan Asmy).


A dining su ka same shi. Fa'eezah ta fara faɗin, 


"Ya Abdallah barka da dawowa." Kafin ya kai ga amsawa ita ma Asmy ta gaisheshi. Da fara'a a fuskarsa ya amsa musu gaisuwar haɗe da faɗin, 


"Ah'ah shalelen Ummah yau kece a gidan? Yaushe rabon da na ganki a gidan nan?" 


Fa'eezah ta ce, "Kai Ya Abdallah kullum fa sai na shigo, kai ne dai zan ce ba ka zama a gidan. Ganinka yanzu sai an cike form." Murmushi ya yi ya ce, "Yo Fa'eezah ina kuwa za ki ganni a gida bayan ina neman na aure. Sarai kin san halinku dai, mata yanzu ba ku auren mara naira." 


Ta ce,


 "A'a Ya Abdallah ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba." 


Yace, 


"Eh to kuma da wannan gaskiya. Yaushe za ku koma school ne?" 


"Jibi monday In shaa Allah."Ta ba shi amsa. 


"Okay. Allah ya kai mu lafiya." 


"Ameen." Ta ce a taƙaice sannan su ka ci gaba da cin abincin su sai da su ka kamalla tsaf su ka kimtsa wajen sannan su ka nufa ɗakin Ummah saboda yau a gidan Fa'eezah za ta kwana. Dama haka tsarinsu ya ke wani lokaci Fa'eezah ta kwana gidan su Asmy wani lokacin kuma Asmy ce ke kwana gidan su Fa'eezah. 


A zaune su ka sameta gefen gado ta na ta shirin kwanciya. Cikin ɗakin su ka ƙarasa tare da zama gefe da gefenta. Fa'eezah ta kwanto kanta jikin Umman ta ce, "Ummah ba ki yi mini ba." Ta faɗa ta na kwaɓe fuska cikin tsantsar shagwaɓa. 


Murmushi Ummah ta yi saboda fahimtar abin da ta ke nufi da hakan. Shafa kanta ta yi cikin so da ƙauna ta ce, 


"Allah ya yi miki Albarka ɗiyar arziƙi irin albarka."  


Ganin haka ya sa ita ma Asmy ta kwaɓe na ta fuskar ta ce ita ma ba ta yarda ba sai anyi mata, yadda kasan ƴan biyu haka su ke yi idan su ka fara rigima a gaban Ummah. Ita kuwa Ummah sai murmushi ta ke ta yi musu mai sauti. Ganin abin na su ba na ƙarewa bane, ya saka ta rungumesu gaba ɗaya ta na faɗin,


"Allah ya yi muku Albarka autaras ɗina." 


Da "Ameen." Su ka amsa su duka haɗe da yi mata Peck a kumatu. 


Washe Gari.


Da misali ƙarfe sha ɗaya su ɗunguma zuwa gidansu Fa'eezah. Su na shiga compound ɗin gidansu ta ga motar daddy. Wanda ya ba ta tabbacin ya dawo daga tafiyar da ya yi kenan. Da farin ciki ta nufa part ɗinsa. Mara mata baya Asmy ta yi. Sai da su ka fara knocking kafin aka basu izinin shigowa. Tura ƙofar ta yi su ka nufa cikin parlourn.


Zaune su ka same sa kan sofa hannunsa riƙe da  jarida ya na dubawa. Da gudu taƙarasa ta rungumeshi haɗe da faɗin,  


"I miss you Daddy." 

Shafa kanta ya yi ya ce, 


"Wato dai har yanzu babyn daddy ba ta girma ba." 

Ƙara langwaɓe kai ta yi a jikinsa ta ce, 


"Ai daddy har yanzu ni jaririya ce a wajenka."


Sai a lokacin ya ɗaga kai ya ga Asmy a tsaye ya ce, 


"Daughter dama tare kuke shine kika tsaya a nan ƙaraso ciki mana."

 Cikin ladabi ta ƙaraso ciki. Har ƙasa duƙa ta na faɗin,


"Daddy barka da dawowa, ya hanya?" 

Murmushi Daddy ya ce,


"No daughter ni kam ba zan amsa wannan gaisuwar a haka ba. Zo ki zauna kusa dani mu gaisa da kya." 

Ba ta ja da shi ba ta ƙaraso kusa da ƙafarsa ta zauna. Murmushi ya sake yi wato ba za ta zauna a kujera ba kenan. Wannan halin tarbiyyar Asmy ya sa hankalinsa ya ke sake kwanciya ko tafiya ya yi bai da haufin halin da Fa'eezah ke ciki saboda sani tarbiyyar gidansu Asmyn. 

Kanta ya shafa ya na faɗin,


"Daughter ƙarfi da ya ji dai kin mai da ni sirikinki bayan ba ni da ɗa balle na ce zan baki sai a yi surukatan da gaske." Murmushi ta yi mai sauti ta na ƙara yin ƙasa da kanta. Fa'eezah ta ce, "Allah Daddy na munafurci ne." Ta yi maganar ta na dariya. 

Daddy ya ce,


"Babu ruwanki karki shiga tsakanina da ɗiyata, ba na son sharri. Ya ɗaura da faɗin, 

"Ya karatun? Ko da ya ke ya hutu zance  ko tun da har yanzu ba ku koma ba." 


Murmushi ta yi ta ce, 


"Alhamdulillah, ai gobe ma zamu koma in sha Allah." 

Ya ce,


"Masha Allah, hutun ma ya ƙare kenan ashe." 


 Ta ɗaga mishi alamar, "Eh."  Ya ce, 

"To madallah, Allah ya yi muku Albarka." Da "Ameen." su ka amsa su duka. 


"Ku tashi ku je ku huta zuwa bayan la'asar sai ku je ku yi shopping ɗin komawa school, tunda yanzu za'a baku tsayayyen hostel." Cewar Daddyn. 


Da, "To." suka amsa mishi haɗe da yi mishi godiya, sannan su ka miƙe su ka nufa dakin Fa'eezah, Fa'eezah ta fara shiga toilet tayi wanka kafin Asmy ita ma ta tashi ta shiga. Bayan sun fito su ka bi lafiyar gado, ko wannen su ya jawo waya ya na hidimarsa. Daga bisani kuma bacci ya yi awon gaba da su.


Sai wajajen 3pm su ka farka. Asmy ta riga Fa'eezah tashi. Toilet ta faɗa ta ɗauro alwala a gaggauce ganin lokaci ya shige. Sannan ta tashi Fa'eezah ta ta shi ta yi sallah ita ma. 



Tsaf su fito cikin shiga iri ɗaya tamƙar ƴan biyu . A parlour su ka samu mommy zaune ta na kallon Tv. Sama sama Asmy ta gaisheta babu sake fuska, don ita Mommyn ba ta game ta ba, haka nan jininta bai haɗu da na ta ba. Fa'eezah ta ce,


"Mom za mu je shoping ɗin komawa school."


Cikin kulawa ta ce, "To, daughter a dawo lafiya." Ta ce, "Ameen." Sannan su ka nufa ɓangaren daddy. 


Da sallama su ka shiga ciki. Yana nan zaune a parlour hankalinsa na kan Tv ya na kallon wani labaren da aka yi highlighting ɗin su akan tashar aljazira. Cikin sanɗa ta ƙaraso bayansa ta ɗaura kanta a bayansa. Ko ba'a faɗa masa ya san ita ce sarai, sai ya yi murmushi ya saka hannu ya juyo da ita zuwa gabansa ya dungure mata kai haɗe da faɗin, 


"Wai yaushe na koma kakanki ni kam, ba za ki dinga bari na ina hutawa ba?"


Dariya ta yi har dimple ɗinta na lobawa ta ce,


"Daddy kewarka na yi da yawa ne fa."


Dogon hanci ta ya ja ya na faɗin, 


Tafiyar just a week da na yi shine kike complain? Alright then next time idan na tafi sai na yi months kafin na dawo, kinga sai ki yi complain mai lasisi."


Ƙafa ta shiga bubbugawa har da ƙananan hawaye na shagwaba. Murmushi ya yi ya ce go and get ready I will called when I'm done. Cikin shagwaɓa ta ce, "Daddy mun shirya fa kai kaɗai kawai mu ke jira." Daddy ya ce, 


"Ah bari daddy ya je ya shirya to kar ya ɓata wa ƴan matan shi lokaci." 


"To daddy bari mu leƙa gidan Umma kafin ka gama."


Cewar Fa'eezar ta ja hannun Asmy su ka nufa hanyar fita. "To a ce ina gaishe da Umman ta ku."


"In sha Allah daddy." 


Gidansu Asmy su ka wuce kai tsaye saboda dama a shirye suke. A parlour su ka samu Umma Ummah ta na kallo a Tv. A ladabce su ka gaisheta ta amsa musu cikin kulawa tare da faɗin, "Daddyn ya dawo lafiya?" Fa'eezah ta ce, "Lafiya qalau Ummah ya ce ma a gaisheku." Daga su ka sanar mata fitar da za su yi da daddy. 


Ummah ta ce, "Oh Daddy dai ba ya gajiya da ɗawainiya, to Ubangiji Allah ya saka mishi da Alkhairi ya cire idon maƙiya daga kanshi." Su ka amsa da "Ameen."




************


"Fadeel be fast mana Dan Allah. Ka na wani shiri kamar mace wannan da a mace ka zo ban san me za ka yi ba wallahi." Cewar Sadiq. 


A tsanake ya vi gaba da shirinsa har ya gama ba tare da ya ɗaga kai ya kalle Sadeeq ɗin bama balle ya sa ran samu amsa daga gare shi. 


Fitowa sukayi daga part dinshi suka nufin part ɗin Ammah. Har ƙasa su ka sunkuya su ka gaisheta ta amsa musu cikin fara'a haɗe da faɗin, "Angon irin wannan kyau haka! Toh Allah ya sa dai a samo mini kishiya daga nan."


Ɗan ɓata fuska Fadeel ya yi ya taɓe baki haɗe da kauda kanshi. 

Cikin jimami Ammah ta riƙe haɓa ta na faɗin, "Oh ni Aminatu naga ta kaina, a ce mutum gaba ɗaya bai son zancen aure kamar mara lafiya, ko wanda aljana ta aura?" 


Shi dai Sadeeq dariya ya ke ta musu. Tashi Fadeel ya yi ya ce,  "Ammah sai anjima." Ya juya da kallonshi kan Sadeeq ya na watsa mishi harara ya ce, "Kai kuma magulmaci inka gama sai ka same ni a hanya." 

Ya na gama faɗin haka ya yi ficewarsa. Da kallo Ammah ta bishi ta na faɗin, "Munafurcin banza da wofi ana so ana kai wa kasuwa, yanzu fa da za'a aura maka matar nan da wata 9 sai dai fa a ji ana maganar suna."


Miƙewa Sadeeq ya yi ya na ci gaba da dariya, ya ce, "Toh Ammah ƙila dai sai kin samo masa matar da kanki in dai auran kike so ya yi." Ya ƙarasa maganar ya na barin parlourn. 


A part ɗin Ummie ya samesa zaune kusa da Ummin da ke zaune akan sofa ya ɗora kansa akan kafaɗarta ya na ta zuba shagwaɓa kai kace shine auta manal. Sadiq ya gaida Ummie ya na faɗin, 


"kai Ummie Allah kina shagwaba wannan katon da yawa, ji shi fa wani goɗoɗo da shi, abin da ya kamata a ce manal ce ke yi ya na mata faɗa amma shi ne shi kato dashi ya ke yi ko kunya babu."


Murmushi Ummie ta yi ta na faɗin, "Sadeeq ka na takura wa autana da yawa fa (Dama wani lokacin auta ta ke ce mishi saboda tazarar dake tsakaninshi da manal ba su yi tunanin zasu sake haihuwa ba sai kuma Allah ya kawo manal... Fatan kun gane ta inda ya samu sunan autan?.) 


Sadeeq ya ce, "Allah Ummie kin dai shagwaba Yaron nan da yawa." Jin ya ce mishi yaro yasa ya ɗago yana watsa mishi wani banzan kallo ba tare da ya ce komai ba. Tashi ya yi su ka yi wa Ummie sallama haɗe da fitowa su ka nufi mota.


Su na zuwa parking slot ɗin Sadeeq ya cilla wa Fadeel key ɗin ya na faɗin, 


"Malam ni fah bazan tuƙa ƙato ba yau ehee."

 

Ai kuwa Fadeel ya juya da niyyar komawa ciki Sadeeq ya yi saurin shan gabanshi ya ma faɗin,  "Malam me kake nufi? To Allah ba ka isa ba ka shiga mu tafi karka ɓata mana lokaci."


Wani ƙayataccen murmushi Fadeel ya yi har sautinsa na fitowa kamar mai ciwon baki ya ce,


 "A ka ce ba ka ji."

Ya yi maganar ya na shiga wajen mai zaman banza. Tsaki Sadeeq ya yi ba tare da ya tanka shi ba....


 Hospital su ka fara nufa su ka ɗan duba patients kafin su ka fito su ka nufa inda su ka yi parking ɗin motarsu tare da faɗawa ciki Sadeeq ya yi wa motar key su ka