62
by @nanadiso10
ZUCIYA DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook
PAGE 62.
Nawaf ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce cikin damuwa sosai,“Ina son ka saurare ni, wallahi na canza daga Nawaf ɗin da ka sani. Kuma ba zan sake bin turbar da mahaifina ke kai ba. Na riga na gane kuskurena. Na fahimci Nayla tamkar ƙanwata ce. Bai kamata da kaina na cutar da ita ba, ko kuma na bari a cutar da ita. Shi ya sa nake son gyara kuskurena, kuma in tabbatar maka cewa ko da mahaifina zai zamo abokin gaba gare ku, ni zan kasance a tsagin ku.” Rayyan ya ci gaba da kallonsa ba tare da ya motsa ba. Fuskar Nawaf ta nuna gaskiya da nadama irin wacce ba za a iya ɓoye ta ba. “Me ya sa ka zo yanzu?” Rayyan ya tambaya Nawaf ya haɗiye yawu. “Saboda na samu wani labari akan sajid zai aure nayla wanda kuma hakan kuskure ne babba ni nasansa sosai.. shiyasa zan gayamaka gaskiya akansa. Rayyan ya ɗan haɗe fuska. “Wace gaskiya?”Nawaf ya sauke numfashi kafin ya ce, “Maganar Sajid ce.” Rayyan ya mike zaune sosai. Nawaf ya ci gaba. “Na ji mahaifina yana magana da shi a waya kwanaki uku da suka wuce. Sun yi magana ne game da Nayla. Kuma daga abin da na ji, Sajid ba ya son Nayla. Yana son auren ne saboda kusancin kuɗi da matsayin gidanku.” Rayyan ya zuba wa Nawaf ido sosai, idanunsa sun ƙanƙance kamar yana ƙoƙarin karanta abin da ke ɓoye a zuciyarsa.
“Are you sure of what you are saying?” ya tambayai, wacce ke nuna cewa ba zai yarda da kowace magana ba sai an tabbatar da ita da hujja. Nawaf ya gyara zamansa, ya haɗiye yawu kafin ya ce da cikakkiyar tabbaci.
“One hundred percent sure.” Ya ɗan yi shiru, sannan ya ci gaba. “Wallahi. Kuma ba wannan kaɗai ba ne. Sajid yana hulɗa da wasu mata daban-daban. Yana kuma Bashida komai wallahi cikakken talaka ne. Mahaifina ne ke ƙoƙarin rufe masa baya saboda wasu anfani da yake son samu idan auren ya tabbata.” Wani irin fushi ya bayyana a fuskar Rayyan. “Na san ka riga ka gano wani abu game da shi,” Nawaf ya ƙara da cewa. “Amma abin da nake so ka sani shi ne, binciken da ka yi gaskiya ne. Sajid ba mutumin da ya dace da Nayla ba.” Office ɗin ya yi shiru na wasu daƙiƙu. Daga ƙarshe Rayyan ya tashi tsaye ya nufi taga, hannuwansa cikin aljihun wando. Ya tsaya yana kallon manyan gine-ginen birnin, zuciyarsa cike da tunani. Bayan ɗan lokaci ya juya ya kalli Nawaf. “Na gode da ka zo ka faɗi gaskiya.” Nawaf ya sauke ajiyar zuciya, kamar an sauke masa wani babban dutse daga zuciya. “Ka yafe min?” ya tambaya cikin rauni.
Rayyan ya yi shiru kafin ya ce, “Abin da ya wuce ya wuce. Idan har da gaske ka canza, Allah Ya shiryar da mu gaba ɗaya.” Idanun Nawaf suka cika da hawaye. “Na gode, Rayyan. Wallahi ba zan sake bari wani ya cutar da Nayla ba.” Rayyan ya gyada kai. “Ka je. Zan kula da sauran.” Da Nawaf ya fita daga office ɗin, Rayyan ya koma ya zauna a kujerarsa. Ya dafe goshinsa da hannu, yana jin cewa al’amura sun fara ƙara bayyana fiye da yadda ya zata.
A lokaci guda kuwa, a can cikin luxury resort ɗin da ke bakin teku, Hanan tana zaune a barandar ɗakinta tana kallon teku. Wayarta na hannunta, amma tunaninta yana yawo tsakanin tsohuwar rayuwarta da sabon farin cikin da take ciki. Ba ta san cewa karɓar lambar Faisal zai buɗe ƙofar wasu sabbin abubuwa da za su iya sauya komai ba.
Kuma a lokaci guda, Rayyan bai san cewa yayin da yake ƙoƙarin kare ƙanwarsa daga hatsari ba, wata sabuwar jarabawa na fara tasowa a rayuwar aurensa.
****
Nayla na kwance a kan gadonta, fuskarta cike da damuwa da tashin hankali. Idanunta sun kumbura ƙwarai saboda yawan kukan da ta sha tun daga daren jiya. A yau tana da wasu muhimman abubuwa da ya kamata ta je ta yi a makaranta, amma gaba ɗaya ta kasa fita. Zuciyarta ta yi mata nauyi, kuma ba ta jin ƙarfin yin komai.
Wayarta na a gefenta ta kunna wata waƙar soyayya mai cike da kalamai masu motsa zuciya. Ta lumshe idanunta tana bin waƙar a hankali, kamar tana neman mafita a cikin baitocin da ke tunasar da ita Sajid.
A daidai wannan lokacin ne Momy ta yi knocking sannan ta turo ƙofar ta shigo.
Nayla na kwance babu dankwali, gashinta a warwatse a pillow, idanuwanta jajir. Sai dai ko shigowar Momy bai sa ta daina sauraron waƙar ba. Momy ta tsaya cak tana kallonta. A zuciyarta ta ji zafi ƙwarai ba wai saboda kuka kaɗai ba, har ma saboda yadda ‘yarta ke yawan shagaltuwa da waƙoƙi fiye da ibada a wasu lokutan. Ta ƙarasa kusa da ita, sannan ta kashe waƙar. Nayla ta buɗe idanunta da sauri, ta miƙe zaune tana kallon Momy Momy ta ɗaure fuska sosai. “Wannan wani irin sakaci ne, Nayla?” ta faɗa cikin tsauri. “Ke ba ƙaramar yaro ba ce. Kullum sai na yi miki faɗa a kan ki daina kunna waƙoƙi a gida.” Ta nuna wayar da hannu. “Menene amfanin waƙar soyayyar da kike sauraro? Ita ce za ta magance matsalarki? Ko kina son ki maida kanki baya?” Hawayen da Nayla ke ƙoƙarin dannewa suka fara zubo. Momy ta ci gaba.
“Wanene Sajid? Tunda yayanki ya yi bincike ya ce bai dace da ke ba, ki ci gaba da addu’a mana. Maza da yawa suna sonki. Allah zai ba ki wanda ya fi alheri.” Da jin haka, Nayla ta fashe da kuka sosai. “Ni wallahi Sajid nake so” ta faɗa cikin kuka. “Ba na son kowa Kuma ko yaya yake, ina sonsa. Saboda kawai Yaya ya ga ba shi da kuɗi ne ya ce ba mu dace ba.”
Nan take Momy ta bugi bakinta cikin mamaki.
“Au, kenan haka kike tunani?” ta faɗa cikin ɓacin rai. “To ai sai ki aure shi da kanki” Da waɗannan kalmomi, ta juya ta fice daga ɗakin.
Da ƙofar ta rufe, Nayla ta saki wani irin ihu mai cike da ɓacin rai da raunin zuciya. Ta faɗa kan gadonta tana kuka kamar zuciyarta za ta tsage. Sa’o’i da dama ta shafe tana kuka ba tare da ta san lokacin da gajiyar kuka da damuwa suka yi nasara a kanta ba. Daga ƙarshe, bacci ya ɗauke ta. Sai wajen ƙarfe huɗu na yamma ta farka.
Bayan ta farka wajen ƙarfe huɗu na yamma, Nayla ta zauna a bakin gadonta na wasu mintuna tana share hawayen da suka bushe a kumatunta. Duk da ɗan baccin da ta yi, zuciyarta ba ta samu sauƙi ba. Akasin haka ma, tunanin Sajid ya ƙara mamaye dukkan tunaninta. Soyayyarsa ta riga ta yi mata katutu a zuciya, har ta kai ga tana jin kamar rayuwarta ba za ta daɗi ba idan ba tare da shi ba. Ta miƙa hannu ta ɗauki wayarta dake gefenta. Hannunta na rawa yayin da ta danna lambarsa. A lokacin Sajid yana cikin sabon office ɗinsa a ɗaya daga cikin companies na Dady, inda aka ɗauke shi aiki kwanan nan. Yana duba wasu takardu ne lokacin da wayar Nayla ta shigo. Da ya ga sunanta, murmushi ya suɓuce masa. Nan take ya ɗaga wayar.
“Princess…” Da zarar Nayla ta ji muryarsa, ta sake fashewa da kuka. “Sajid…” ta kira sunansa cikin shasheƙa. “Idan suka raba mu… yaya za ka yi?” Sajid ya gyara zamansa, ya sauke murya cikin salon da ya san yana kwantar mata da hankali. “Princess, babu wanda zai raba mu. Ki ji ni da kyau ina sonki fiye da komai. Kuma na rantse da Allah, kece matar da nake son aura.” Nayla ta ƙara matse wayar a kunnenta. “ Yaya ya ce ba zai taɓa yarda na aureka ba .” Sajid ya yi shiru na ɗan lokaci kamar yana tattara kalmomin da zai ƙara ɗaure mata zuciya da su.
“Ki saurare ni, Nayla. Wani lokaci mutane ba sa fahimtar irin soyayyar da ke tsakanin mutane biyu. Amma idan ƙauna ta gaskiya ce, dole ne a tsaya a kanta.” Kalaman nasa suka sa zuciyarta ƙara narkewa. “Ni idan ma suna ganin ba ka da kuɗi,” ta faɗa cikin kuka, “zan ba ka komai daga cikin kadarorina. Ka yi kasuwa ka zama mai kuɗi.” Sajid ya yi murmushi a ɓoye, amma a fili ya yi magana cikin taushin murya. “Wanda kika ba ni a baya ma ninkuwa suke yi. Yanzu boutique ɗina na tafiya sosai, kuma alhamdulillah na fara samun rufin asiri. Amma ki sani, ba dukiya nake so ba. Ke nake so.” Sai ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara da wata magana da ta ƙara ƙarfafa zuciyarta. “Idan da gaske kina sona, kada ki yarda wani ya sa ki hakura da ni. Ki nuna musu cewa soyayyarmu ba ta wasa ba ce.” Nayla ta share hawaye, zuciyarta na cika da wani sabon ƙuduri. “Wallahi ba zan bari su raba mu ba.” “That’s my girl,” Sajid ya faɗa cikin murmushi. “Ki tsaya tsayin daka. Ki roƙi Dady. Ki nuna masa cewa ba za ki taɓa farin ciki da wani ba sai ni.” Ya ci gaba da lallashinta da kalamai masu daɗi har sai da kukanta ya lafa, ta fara murmushi. Bayan ta gama waya da Sajid, Nayla ta zauna na wasu mintuna tana rungume da wayarta a ƙirji. Kalaman da Sajid ya gaya mata sun sake kunna wata sabuwar wuta a cikin zuciyarta. A karo na farko tun bayan da aka fara nuna adawa da soyayyarsu, ta ji kamar tana da ƙarfin da zai sa ta tsaya ta kare mutumin da take so, ko da kuwa za ta fuskanci fushin kowa a gidan. Ta share hawayen da suka jike mata fuska, sannan ta dubi kanta a madubi. Idanunta sun yi ja saboda kuka, amma a cikin zurfinsu akwai wani sabon ƙuduri mai cike da taurin zuciya. Soyayya ta riga ta cire mata kunya da tsoron da ta saba yi wa iyayenta.
Cikin sauri ta sauko ƙasa. Tun kafin ta shiga babban falon, ta hangi ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan yana wucewa. “Dan Allah kawo min smoothie,” ta faɗa a taƙaice.
“Okay, Hajiya,” ya amsa cikin girmamawa.
Nayla ta ci gaba da tafiya har zuwa falon Dady. Kamar yadda ta zata, Dady na zaune shi kaɗai a palour ɗinsa na musamman. A gabansa akwai wasu takardu da laptop, amma tun daga yanayin fuskarsa za a gane cewa hankalinsa yana kan wasu manyan tunani. Da Nayla ta shiga, ta yi sallama cikin sanyin murya. Dady ya ɗaga kai. “Wa alaikis salam.” Ta ƙarasa cikin ladabi ta zauna kusa da shi. Na ɗan lokaci ta kasa magana. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi, hannayenta na rawa. Amma soyayyar Sajid ta fi duk wani tsoro ƙarfi. “Dady…” Ya kalle ta cikin nutsuwa.
“Ni fa… ina son Sajid wallahi.” Dady ya zuba mata ido cikin mamaki, kamar bai yi tsammanin za ta sake dawo da wannan maganar ba. “Nayla,” ya faɗa a hankali, “ni kike gaya wa haka?” Ta gyada kai, hawaye na taruwa a idanunta. “To, ba ki ji abin da Rayyan ya faɗa ba?” Nayla ta haɗiye yawu. “Amma Dady, ka san mutane suna iya yin ƙarya. Ni dai ina sonsa. Duk yadda yake, ina ƙaunarsa.”
Dady ya ɗan yi shiru, sannan ya ce cikin murya mai nuna cewa ya riga ya yanke hukunci. “Tun bayan maganar da Rayyan ya yi, ni ma na sake yin bincike. Saboda haka, maganar Sajid babu ita yanzu. Kin ji ko?”
Nayla ta matsa kusa da shi, kuka na neman ƙwace mata murya. “Amma Dady, don Allah ka saurare ni. Wallahi ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba. Ina sonsa fiye da yadda zan iya bayyana.” Dady ya ɗaga hannu alamar ta tsaya. “Na ce miki, maganar Sajid ta ƙare.”
Nayla ta girgiza kai, hawaye na zubo babu ƙaƙƙautawa. “A’a Dady. Don Allah kada ka raba mu. Idan kuna ganin ba shi da kuɗi, ni zan taimaka masa. Zan ba shi duk abin da nake da shi. Kawai don Allah ka bar ni na aure shi.” Dady ya ƙure ta da ido. “Har wannan maganar ta kai ga kina tunanin ba shi kadararki?” Nayla ba ta ma lura da abin da ta furta ba. Soyayya ta riga ta rinjayi hankali da kunya. “Eh, Dady,” ta faɗa cikin kuka. “Ko me zan rasa, a shirye nake. Abin da kawai nake so shi ne kada ku rabamu.” A daidai wannan lokacin, ma’aikacin da ta aika ya shigo da smoothie. Da ya ga yanayin da ake ciki, ya ajiye kofin a hankali ya fice ba tare da ya ce komai ba. Nayla ta matsa har ta kama hannun Dady da nata biyu. “Dady, don Allah. Ka dubi yadda nake son sa. Wallahi idan ban aure shi ba, ba zan yi farin ciki ba.” Dady ya zare hannunsa a hankali, fuskarsa ta nuna haɗuwar mamaki da ɓacin rai. “Na yi mamakin yadda soyayya ta cire miki kunya har kike magana da ni haka.” Kalaman nasa suka sa Nayla ta rusuna a gabansa. “Dady, ina roƙonka. Ka taimake ni. Ka tausaya min.”
Dady ya miƙe tsaye, alamun haƙurinsa sun fara ƙarewa. “Nayla, ya isa haka.”
Amma ta ci gaba da kuka. “Ina sonsa, Dady. Ina ƙaunarsa sosai.” “Za ki bar min wuri ko sai na ɗauke ki da mari?” Tsawar da ya yi ta girgiza falon gaba ɗaya. Nayla ta tsaya cak, jikinta yana rawa. Dady ya ci gaba cikin murya mai tsauri. “An hana ki mutum saboda soyayya, kina ƙoƙarin bijire wa umarnina? Wannan ba tarbiyyar da muka koya miki ba ce.” Kalaman nasa suka fasa duk wani ƙarfin hali da take da shi. Ta saki kuka mai ƙarfi, ta miƙe tsaye cikin ruɗani. Ba tare da ta sake cewa komai ba, ta juya da gudu ta fice daga falon.
ZK2026
***
***.