BARRISTER SUHAIL

59

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----59


labarin dawowar Amina ya cika kauyen cikin karamin lokaci

mutanen da abaya suke nuna masu tsangama suna cewa ta kashe mijin ta a yanzu sune mutanen da suka cika kofar gidan mahaifin ta

wasu suna murna wasu kuma kunya ce fal a cikin su tare da nadamar Abinda suka aikata masu 

wata tsohuwa ladi ta matso kusa da Amina ita ce mace ta Farko data soma ƴada zargi cikin gari 

ta kama hannun ta 

ta ce"Amina ki yafe min mun zalun ceki mun dora maki Abinda baki aikata ba"

baba ladi na ɗaya daga cikin munafukan Garin tsauni idan kanaso zance ya tashi kaje ka sameta a ranar hatta jariri sai yasan abinda garin yake ciki duk wani zance yana kunnen ta duk da tsufan da tayi hakan bai hanata shiga Abinda babu ruwan ta ba


Amina ta ce"baba ladi na tafe wa kowa"

kalaman suka sa wasu daga cikin matan Kuka ciko hadda baba ladi

suka tun kari cikin gidan 

mahaifin Amina malam na zaune ƙarƙashin bishiyar mangoro dake shuke a tsakar gidan suka shiga 

wata irin kunya ta lulleɓe sa ganin Amina a gabansa duk da tun kafin isowar su ya samu labarin cewa kotu ta wanke Amina daga zargi

ya kasa haɗa ido da kowa a cikin su 
Amina ta ƙarasa gaban sa cike da ladabi ta ce"baba ina wuni"

da kyar ya iya amsawa da"lafiya qlau" wani irin nauyi da kunya suka cika Zuciyar sa 

mahaifiyar ta kallesa sama sa ƙasa ta ce"Musa wajen ka nazo"

sai lokaci ya daga ido ya kalleta karin farko tun bayan auren su sama da shekara Ashirin ta kirasa da sunan sa irin haka.

"Saude ina jinki"

"inaso ka sake ni"

ba malan musa ba hatta Amina sai da ta kalleta cike da mamakin jin Abinda yake fitowa daga bakin mahaifiyar ta 

Malan musa ya ce"saki kuma saude gaskiya ni bazan sake ki ba"

kuka ta fashe dashi ta ce"wallahi musa sai ka sake ni na gaji da zaman da babu daraja a cikin sa tun dana aure ka ban samu kwanciyar hankali kai kamin matar ka tamin to ina so ka sani an zo gaɓar da ban iya cigaba da zama da kai ba"

"duk kaine sillar ciga Amina wannan halin amman lokacin da aka kama Amina baka je ba"

"haka zaman kotu ko sau Daya baka taka ba"

"ka barni ina yawo,ni ƙadai ina neman taimako tamkar Ni kadai na haife ta"

Malan musa ya rasa abin fadi

"nayi shekaru ina yi maka biyyayya a matsayin ka na miji"

"Amman a lokacin da nafi buƙatar ka sai ka juya min baya"

"Saboda haka,ka sakeni"

matarsa uwani ta fito daga dagi sai ya tsina fuskar take ta ƙaraso wajen su baban jamilu wato babban danta kenan lafiya nake ta jiyo hayaniyar ku a ɗaki 

kallon ta yayi ya ce"wai saude ce tazo wai sai na sake ta"

"to sai ki badai haƙuri ka tsaya bata ba ai ko bata faɗa ba hukunci saki ne a kan ta ko ka manta kimanin sati biyu kenan bata cikin gidan nan"

murmushi saude tayi ta ce"ki kwantar da hankali uwani,nima daga nan babu inda zan matsa sai musa ya ce ya sake ni"

musa yayi shiru yana dogon nazari

“Saude… ki ba ni dama na gyara Na san na yi babban kuskure Wallahi na yi nadama"

Saude ta girgiza kai

“Nadama ta zo ne bayan komai ya lalace, Musa Zuciyata ta gaji taso bukatar yanci"

daga karshe ya ce"saude kije na sake ki saki ɗaya,ki tafi"

saude ta runtse ido yayin da kalmar saki ke fita daga bakin malan musa zuciya ta karye,bata so sakin ba har ranta amman bata da wani zabi daya wuce hakan dan bazata iya zama da malan musa ba idan ta tuno Abinda yayi wa Amina zuciyar ta na cigaba da tsanar sa har lokacin hawaye basu daina zuba daga idanun ta ba 


ta juya zata tafi Amina tabi bayan ta Malan musa ya ce"ke Amina ina kuma zaki je"

a raunane saude ta kalleta ta ce"Amina ki zauna a wajen mahaifinki nima zan koma wajen nawa dangin"

kuka ta fashe masu ta shi ta ce"haba Mama ki duba halin da nake ciki ina cikin halin rayuwa ko mutuwa dan haka bazan iya zama babu ke ba"

ta juya ta kalli mahaifinta ta ce
Na kasance ’yarka, kuma zan ci gaba da girmama ka a Matsayin uba gare ni"

“Amma bayan Allah Mama ita ce ta tsaya min lokacin da kowa ya juya mini baya tafi kowa shiga tashin hankali ,bata samu natsuwa har sai da ta tabbatar da na shaƙi iskan ƴanci"

“Ba zan bar ta ita kaɗai ba"


“Inda take zan kasance tare da ita koda kuwa zamu rayu a cikin daji"


Mutumin ya sunkuyar da kansa

Ya gane cewa yau ya rasa abin da kuɗi ba za su iya dawo masa da shi ba

A hankali Amina ta kama hannun mahaifiyarta

Su biyun suka juya suka fita daga gidan

Ya tsaya yana kallonsu

Har suka ɓace daga ganinsa
A zuciyarsa kuwa

Nadama ce kawai ta rage masa

uwani ma ta juya ta koma daki

Da suka ɓace daga ganinsa

Malam Musa ya durƙusa a ƙarƙashin mangwaron

Hawaye suka zubo masa ba tare da ya iya tsayar da su ba

Ya ɗaga hannayensa sama ya ce,

“Ya Allah na tuba Ka gafarta mini"

“Na zalunci matata"

“Na zalunci ɗiyata"

“Allah Kada Ka hukunta ni da kuskuren da na aikata"

Ya rushe da kuka, amma babu wanda ya rage a gidan da zai share masa hawaye

Bishiyar mangwaron da shekaru da dama ta shaida farin cikin gidan…

A yau ita ce kaɗai ta rage tana shaida rushewar wannan iyali.

Iska mai sanyi ta kaɗa ganyayenta a hankali, tamkar ita ma tana jimamin abin da ya faru

Malam Musa kuwa ya ci gaba da kuka…

Amma kukan nasa ya zo ne bayan ya rasa komai

ya rasa mata ta Gari da kuma Amina yarinya mai hankali da sanin ya kamata

takaitacciyar nasiha 

Ba kowace uwa ce take samun damar rayuwa cikin farin ciki ba Wasu iyayen mata suna binne burinsu, suna haɗiye hawayensu, suna ɗaukar nauyin zafi da wahala domin kawai su ceci rayuwar ‘ya’yansa Uwa ta gaskiya tana iya rasa komai, amma ba ta son ta ga ɗanta ya rasa komai. Wannan sadaukarwa ce da ba za a taɓa biyanta ba sai da kyakkyawan ɗabi’a, biyayya, da addu’a Allah Ya jiƙan iyayenmu, Ya saka wa masu rai da alkhairi, Ya ba mu ikon kyautata musu tun kafin lokaci ya ƙure 🤲💙

ku duba irin wahalar da mahaifiyar Amina tasha daga karshe ma ta kashe auren badan ranta yaso amman wani lokacin bawai muna rubutu bane dan nishadantarwa kadai akwai saƙo na masu mahimmanci da ko wani marubuci kesan isarwa

like 
share 
comment 

sai mun hade a page 60 ya kamata fa naje hutu ko