60
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
🅿️—–60
A ranar, Saude ta samu mai mota ya kwashe musu kayansu gaba ɗaya daga Garin Tsauni zuwa Garin Gabas, inda yayarta suke uba daya data ke zaune.
Da misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa
Duk sun yi likis da gajiya.
Musamman Amina, wadda gajiyar tafiya ta fi ratsawa saboda cikin da take ɗauke da shi
Turai na tsakar gida tana tukin tuwo lokacin da suka shigo da sallama
Ta ɗago kai
Da idonta ya sauka kan Saude
Ta saki muciyar da ke hannunta ta nufi wajen ta
“Saude!”
Ta faɗa da mamaki tana kallon ta
Da sauri ta ƙaraso gabansu
“Lafiya kuwa? daga ina kuke da yammar nan"
Tun kafin Saude ta ba da amsa Turai ta rungume ta
Sai a lokacin ne ta lura da jajayen idanunta da alamun kuka a fuskarta
Hankalinta ya ƙara tashi
“Subhanallah… me ya faru?”
Amina ta sunkuyar da kai
Hawayen da ta shaƙe tun daga hanya suka sake cika mata ido
Saude ta sauke numfashi
“Yar uwa dogon labari ne"
Turai ta kama hannunta
“To ku fara shiga ciki tukuna da alama Kun gaji"
Ta ɗaga murya tana kiran cikin gida"
“Maryam! Zo ki taimaka a sauken saude"
Nan take wata budurwa mai kimanin shekara ashirin da biyu ta fito da sauri jin an kira sunan saude
Da fara’a ta ce
“La baba saude kune a garin namu sannu ku da zuwa"
Ta gaishe da Saude cikin ladabi, sannan ta rungumi Amina
“Sannu da zuwa Amina.”
Amina ta yi murmushi mai ciwo
“Yauwa Maryam"
Da taimakon wasu yaran unguwa suka sauke kayan daga mota saude ta biya su kudin motar
Turai ta shigar da su ɗaki
Ta kawo musu ruwa mai sanyi suka sha
Bayan sun ɗan huta kaɗan
Turai ta sake kallon Saude
“Yanzu fa ki faɗa min miya same ki me ya faru"
Saude ta yi shiru na wasu daƙiƙu.
Sai hawaye suka gangaro mata ta ce"
“yaya turai Auren Musa ya mutu"
Turai ta zaro ido “Me kika ce"
“Ya sake ni"
Shiru ya mamaye ɗakin Ko motsi babu wanda yayi
Maryam ma ta kasa cewa komai
Turai ta dafe ƙirji ta ce
“Subhanallah!Har abin ya kai haka?"
Saude ta gyada kai ta ce"
“yaya turai bazan iya cigaba da zama dashi ba,Lokacin da Amina take cikin bala’i, ya juya mana baya Na yi ta fama ni kaɗai,kwata kwata na daina ganin musa da mutunci"
Turai ta matso kusa da ita
Ta kamo hannunta cikin tausayi ta ce "Ki kwantar da hankalinki nan ma gida ne keda Amina ba baƙi ba ne duk da saude ke ki ja baya dani ko halin da Amina ta shiga sai a gari naji"
"kuyi zaman ku anan har zuwa muga yadda Allah zaiyi nasan baban Maryam ma baida matsala"
Da jin wannan kalaman
Saude ta fashe da kuka
Ba kukan nadamar sakin da Musa yayi mata take ba
Kuka ne na samun wurin da za ta sauke nauyin da ta daɗe tana ɗauke da shi
Ta ji tamkar ta dawo jikin mahaifiyarta
Tun suna ƙanana, Turai ba ta taɓa ɗaukarta a matsayin ƙanwar uba ɗaya kaɗai ba
A gare ta, uwa ce, abokiya ce, kuma mafaka ce a duk lokacin da duniya ta ƙuntata mata
Shi ya sa tun da ta rasa mahaifiyarsu, duk wani ciwo ko damuwa da ta same ta, Turai ce mutum na farko da take neman ta
Turai ta rungume ta tana shafa bayanta cikin tausayi
Ta ce
“Ki yi haƙuri Saude wata rana sai labari"
Abuja
suhail ne zaune a falo yana jiran iman da zeenah zasu je gidan gidan Aunty Zarah suyi mata sannun da zuwa sun dawo daga Umrah
iman ta fara saukowa sanye take wata white Abaya tayi rolling da gyalen Abaya
tun da ta fara saukowa Suhail duk da ba wani kwaliya tayi ba
Sai dai hasken fuskarta da nutsuwar murmushinta sun ƙara fito da kyawunta fuskar ta
har ta ƙaraso wajen bai dauke idanun sa daga kanta ba
Turo baki tayi ta ce"yaya Suhail nidaii ka daina kallo na sai kace baka sani ba"
murmushi yayi ya ce"ba dole in kalleki ba kullum ƙara kyau kike da alama da yaya Suhail ya iya reno"
murmushi tayi tare da yi masa hararar wasa
agogon dake hannun sa ya kallah ganin lokaci na tafiya ya ce"bari na kira zeenah ta fito mu tafi"
zama tayi kan kujerar
suhail ya nufi Dakin zeenah da mamaki yake kallon ta ganin ta kwance akan gado
bayan ta karasa ciki ya ce"zeenah kinsan zamu fita fa You kept us waiting for you"
"Suhail ni fa na fasa zuwa"
"zeenah kamar yaya kin fasa gidan aunty Zarah fa nace zamu je"
"Suhail koma ina ne ni nace banzan ke ba ai bani kadai bace matar ka sai ka dauki iman ku tafi tare tunda nace bazan je ba"
Suhail ya daɗe yana kallonta na wasu sakanni
Ya sauke numfashi a hankali
“Shikenan"
Kalma ɗaya kawai ya faɗa
Ya juya ya fita daga ɗakin
Zeenah ta tashi zaune tana dariyar mugunta
“Aƙalla yau itama ta ɓata masa rai" Ta faɗa a hankali
Amma ko kaɗan ba ta san cewa
sai dai bata sani ba Suhail ko a kansa shi zai iya cewa ma yaji daɗin hakan
yana fita ya koma falon
Iman ta ɗago kai da ganin Suhail ya dawo shi kaɗai
Ta tambaya cikin mamaki
“Yaya Suhail, ina Zeenah din?”
ya ɗaukar key ɗin motarsa
“Ta ce ba za ta je ba"
Iman ta yi shiru
Iman ta ɗan haɗe gira.
“Amma Yaya Suhail… me ya sa ta ƙi zuwa?”
Ya ɗan yi murmushi mai sanyi
“Ban sani ba Wataƙila tana son ta huta"
Iman ta buɗe baki za ta sake magana
Ya girgiza kai a hankali
“Please, Iman… mu bar maganar mu tafi"
Kai ta jinjina
“To"
fita sukayi zuwa parking space suka shiga motar ya tada sukayi gaba.
tafiyar mintuna Ashirin sukayi suka tsaya a katafaren gate din gidan aunty Zarah
share
like
and comment
Please