BARRISTER SUHAIL

61

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----61

tare suka fito zuwa cikin gidan Suhail na gaba iman na biye 
dashi a baya 

knocking yayi mai gadi ya buɗe masu cike da fara'a ya tarbi Suhail dan ya san shi yana yawan zuwa gidan aunty Zarah a kwanakin baya 

bayan sun Gaisa suka nufi cikin gidan bayan ya dan na doorbell Amatullah tazo ta buɗe wani irin ƙara tayi tare da rugume iman cike da so da kauna ta ce

"aunty Iman nayi missing dinki"

murmushi tayi ta ce"miss You to my damsel"

daidai lokacin aunty Zarah na saukowa hannun ta rike da junaid jin karar Amatullah ne ya sauko da ita dan a yadda tayi ihun zaka rantse wani abu akayi mata 

cike da murmushi ta ƙarasa saukowa daga upstair din 

"yau manya baƙi ne a gidan namu"

Suhail yayi murmushi suka karasa cikin falon bayan sun zauna iman ta fara gaishe da Aunty Zarah ta amsa ta ce"iman sai yau nake ganin ki"

murmushi tayi ta ce"Aunty Zarah kullum fa sai nace yaya Suhail ya kawo ni"

baƙi ya buɗe jin maganar iman "ko yaushe akayi hakan"

Suhail ya ce"Aunty Zarah nifa karya tayi min yaushe kika ce na kawo ki"

harararsa tayi ta ce"kullum ma"

dariya aunty zarah tayi ta ce

"ai ba dole sai shi zai kawo ki ba da kinji kina son zuwa kawai ki kirani na turo driver ya dauke ki"


murmushi tayi ta ce"to aunty"

Sadeeq ke saukowa daga uptsair sanye cikin fara shadda gezner sai zuba Kamshi yake 

ya ƙara so cikin dakin da mamakin yake kallon suhail dann har ya manta rabon da gidan idan zai iya tunawa tun satin bikin su da iman

Sadeeq ya ce"Barrister yau kaine a gidan it's her been a while rabon ka da Gidan ko matar ka ta boƴe ka "

"oh na manta ashe fa kai 2 star man ne ko"

murmushi Suhail yayi ya ce"yaya sadeeq ayyuka ne ke min yawa amman yanzu ba gashi nazo ba an dawo lafiya"

murmushi Sadeeq yayi ya ce"haka dai kace, ina dayar matar taka ko wannan ce ta gaban mota"

kowa sai da yayi dariya banda Amatullah da take zaune kan cinyar Iman 

suhail ya ce"ba haka bane,naso mu taho tare to bata jin Dadi ne"

jinjina kai yayi ya ce"Allah ya bata Lafiya"

ya kalli iman ya ce"Amarya ya gida?"

Aunty Zarah ta ce"baban Amatullah ita ce uwar gidan fa"

"oh, i'm sorry kinsan this is our first time to meet"

murmushi kawai iman take ta gaishe shiya amsa 

sadeeq sai kalon ta yake lokaci zuwa lokaci jin cewar ita ce uwar gidan Suhail nada mata kamar wannan mai hankali da natsuwa mi ya kaisa ƙara aure mai yake nema bayan wannan duk yadda Zarah take ƙoda iman a wajen Sadeeq ya ga ta wuce yadda take faɗa the girl is so calm and gentle.

tashi Sadeeq ya yi  ya  dubi Zarah ya ce"zai fita"

Suhail ya ce"ai kawai ya jira sa su fita tare anjima zai dawo daukar iman"

suna tafiya Aunty Zarah ta dubi iman ta ce"muje ciki ko"

tabi bayan Aunty Zarah har zuwa dakin ta a falon sama ta zauna har lokaci Amatullah na manne da ita

koda suka zauna Aunty Zarah ta ajiye junaid ta nufi Kitchen ta hado wa Iman trays mai dauke da snacks irin na makkah sai dabino da bagaruwa tare da ruwan zamzam ta ajiye mata a gaban ta 

ta kalli Amatullah ta ce"ta dauki junaid ta koma dakin su ta bar iman ta huta"

ba'a san ranta ta dauke shi ba tana turo baki ta koma Dakin su

ta dubi iman ta ce"ki ci mana Iman"

a hankali ta sauko ƙasa ta tisa tire din a gaba dabinon kawai ta iya ci 

aunty Zarah ta dube ta ce"iman inaso muyi magana dake amman kimin Alƙawarin zaki fada min gaskiya"

sai da taji faduwar gaba tazo mata amma ta dake ta ce

"nayi miki Alkawari"

aunty Zarah ta gyara zaman ta ta tattaro hankalin gaba ɗaya wajen iman ta ce"iman kina amfani da tsarin iyali ne duk tunanina zan ganki da juna biyu amman" ƙasa karasa Maganar tayi 

idanun iman suka cika da ƙwalla ta Girgiza kai 

aunty Zarah na lura da yadda mood dinta ya chanza sai taji jikin  ta yayi sanyi Amman bawai tayi Maganar don cin fuskar bane 

saukowa tayi ta kama hannayen ta ta ce"Iman i'm sorry,banyi Maganar dan na ɓata maki rai bane na tambayeki idan har baki Amfani da tazarar iyali i can find a way to help you"

hawayen kan fuskar ta soma sharewa ta ce"wallahi ban taɓa shan komai ba"

aunty Zarah ta ce"nagane ki cigaba da cin abinci nasan haihuwa ta Allah ce amman i will take You to gynecology su duba lafiyar ki first"

kai ta jinjina mata ƙarin farko taji ranta yayi mata sauki ko ba komai yau ta samu wanda ya samu da sanin lafiyarta 

duk da Suhail tayi ta jira yayi hakan amman shiru ita kuma ta ƙasa yi masa maganar

don a ganinta ma kamar ta fisa son haihuwa

Aunty Zarah ta lura yadda hawaye suka ci gaba da gangarowa a kumatun Iman

Ta ɗauko tissue ta share mata.'

Cikin murya mai laushi ta ce

“Iman… me ya sa kike ɓoye  damuwarki"

Iman ta yi murmushi ta ce


“Aunty  Zarah Na yi ta jira kullum ina tunanin wata rana Yaya Suhail zai ce mu je asibiti a duba lafiyarmu"

“Amma bai taɓa buɗe maganar ba"

Ta sauke ajiyar zuciya

“Ni kuma ban san ta yaya zan ce masa ba"

“Saboda bana son ya yi tunanin kamar ni ce nake matsa masa matsa tunda bani kadai bace Matarsa"

Aunty Zarah ta dafa kafaɗarta ta ce"kowa damuwar sa ya sani wata ƙila ita Zeenah bata da ra'ayin hakan duk itama ba zamu yanke mata hukunci ba"

“tunda ke kina so You have to talk to him mijinki ne"

Iman ta sunkuyar da kai

ta cigaba da cin dabinon

har dare kafin Suhail ya dawo ɗaukar ta suna zaune a falon ƙasa ya shigo 

sanye yake da ƙananun kaya T-shirt da trouser sai zuba Kamshi turare yake tamkar a lokacin ya saka shi 

iman na zaune kan kujera tare da Amatullah suna game a ipad din ta 

iman najin shigowor ta dago ido ta kallesa ba tare data motsa ba 

bayan ya zauna Aunty Zarah ta ce"Suhail yanzu fa nake ƙoƙarin kiranka ashe ma kana hanya"

"Aunty Zarah lafiya dai ko"

"eh daman zan fada maka kabar Iman ta kwana a nan gobe zamu je Asibiti"

ba Suhail ba hatta Iman sai tayi mamakin jin kalaman Aunty Zarah da ita basu haka da ita ba 

"Aunty Zarah,Iman din bata da lafiya ne"

kai ta girgiza "she is well kawai inaso na kaita ayi mata medical check up kasan yana da kyau lokaci zuwa lokaci ma'aurata suna zuwa asibiti a duba lafiyar su"

bazai iya musu da aunty Zarah ba amman har ga Allah baya son ya bar iman ta kwana a gidan nan babu yadda ya iya haka ya tashi ya ce zai tafi

har ya kai bakin kofa iman na kallon sa ganin kamar ransa ba dadi ta kalli aunty Zarah cikin rauni ta ce"Aunty zan raƙasa gate"

murmushi tayi ta ce"ban hanaki ba ai"

Amatullah ta tashi zata bita Aunty Zarah ta mata tsawa ta koma

da sauri ta fita ganin har kusa fita daga gate rigar taja daga baya 

ya juyo cikin rauni ta ce"yaya Suhail yanzu tafiya zakayi ka barni"

"Eh,mana ai bansan abinda kuka tattauna da aunty Zarah ba har ta ce a barki ko dan haka duk sanda kika shirya kin dawo Nagode Allah da ba ke kaidai bace "

hawaye ya cika a Idanun ta ganin Suhail na ƙoƙarin dora mara laifin da bata yi ba ta kama hannun sa ta ce"Sweetheart wallahi bani nace ba kuma ma kazo mu koma sai a tambayeta kayi haƙuri"

murmushi yayi "oho ashe haka aka damu dani,naji zanyi haƙuri Amman sai kin rakani har mota"

tare suka fita Wajen gate sun jima a mota suna hira ganin dare ya soma tayi ta ce masa zata koma ciki kar Aunty Zarah taga ta jima

bakin ta da nasa ya hade waje guda ya soma kissing sai da sanye gaba daya jan liptick din da Amatullah ta shafa mata 

ganin ya kokari  cire mayafin dake jikin ta ta riƙe hannunsa ta ce"please yaya Suhail baka ganin ba a gida muke ba bar Aunty Zarah tayi tunanin wani abu"

da kyar ya sake ta ta flta da gudu ta koma ciki....


masu cewa ina typing kadan🥱 ai kune bakwa san comment sai na dage nayi typing amma sai dai kuce thanks amman duk da haka ina Godiya da likes amman ku gyara Please 

khadywrites🤟🏼