62
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----62
ta jima tsaye a balcony tana gyara Kayan ta gudun kar su fahimci Wani Abu ya Faru tsakanin ta da Suhail
Kowa yana zaune a Inda ta barsu Amatullah a hankalli ta karaso shigo wa kamar mai tsoron Wani Abu
Amatullah ta kalleta ganin babu lipstick data Shafa mata ta zaro ido”laa aunty kema Shanye lipstick din kika yi ba kyau fa “
Ji tayi ruwa gaba daya ya cinye ta ta kalli aunty Zarah ta gefen ido ganin hankalin ta baya wajen su ta sauke ajiyar zuciya
Ta kama hannun Amatullah suka Koma ciki gudun kar ta sake ɓallo mata wani ruwan
Aunty zarah ta bisu da kallo bata taba ganin mutun mai kunyar iman ba
Washe Gari
Aunty Zarah da wuri ta tashi ta shirya Amatullah drivern ta ya kaita school
Sai da ta gama hada breakfast ta tashi iman tayi wanka ta shirya cikin wata bakar abaya mai launin cream
Aunty Zarah na dining Tana serving din Sadeeq anan take faɗa masa zasu je Asibiti a duba iman
kai ya ya daga dan tun ajiya ta fara faɗa masa
ta kaiwa iman nata breakfast din daki tea ne sai soyyayan kwai da omlette da fruits ta ajiye mata a gaban ta
karfe tara daidai suka fito sadeeq na zaune a falo yana dan na wayar sa gefen sa kuma junaid yana wasa iman ta duƙa har ƙasa ta gaishe shi
ya amsa cike da sakin fuska Aunty Zarah ta ce zasu tafi kudin dake ajiye a gefen sa ya miƙa mata ya ce"gashi koda za'a bukaci wani abu"
Godiya suka yi masa Aunty Zarah ce tayi driving din su har suka isa wannan babban private hospital dake tsakiyar Birnin Abuja
tun daga bakin Asibitin zaka sheda haduwar sa tamkar kana a ƙasar waje bayan masu gadi sun gama screening din motar su ta ajiye motar a parking space suka shiga cikin harabar asibitin a bakin reception suka nufa
ko ina sai kamshin disinfectant yake nurse na bakin reception suna kula da masu shiga da fita
daga gefe Guda kuwa wasu ƴan tsirarun patient ne zaune kan waiting chairs dan da wuya ka iske layi a sibitin ba kowa ke zuwa ba duk da kwarewar su a wajen aiki amman mutane na koka a kan yadda tsadar abubuwa suke ke amman duk hakan mutane tafe suke
daya daga cikin nurse din ta tare su "welcome ma'am how i can help you"
Aunty Zarah ta ce"zamu bude card ne za mu gaga Dr nadia"
"okay ma'am did you have an appointement with her"
"no,but tell her it's Zarah munnir Mahmud"
nurse ta dauko telephone dake ajiye a reception din ta kira office dr nadia ta ce"dr you have a visitor Miss Zarah munnir Mahmud"
ban samu damar jin abinda dr nadia ta ce ba nurse ta kashe wayar
ta kallli Zarah ta ce"private card ne ko Family"
Dan tunani tayi ta ce"family card"
file ta dauko ta fara cikewa "name of the spouse"
"Br Suhail munnir Mahmud"
bayan ta rubuta ta tambayi shekaru sa shima ta rubuta
ta ce" the wife name"
sai lokaci iman tayi magana "Khadija iman Abdullah"
duka ta rubuta aka tura su dakin biyan kudi da kuma na ganin likita suka biyan kudin kati da consultation suka nufi bakin office din da dr nadia ke ciki har sai da layi yazo kan suka shiga
dr nadia na ganin Zarah da murmushi ta tashi ta rungume ta Zarah dama kina nan
"eh,ba gashi kin gan niba"
bayan sun zauna Zarah ta dubi nadia ta ce"long time tun muna turai rabo na dake sai daga bayan nake samun labarin kinyi aure"
nadia ta ce"aiko dai nima ban jima da dawowa Abuja ba from lagos na samu transfer zuwa nan,but nayi mamaki yadda akayi ƙi kasan ina nan"
Zarah ta ce"jiya na kira dr hafiza akan zanzo sai ta ce ta samu transfer tana Lagos amman zata haɗa ni da nadia tunda ta faɗa nasan kece"
murmushi tayi ta ce"hmmm,Zarah har yanzu intelligence naki na nan dan ma kin ƙi aiki kin barmu muna ta shan wahala"
"Nadia aiki ai yana da amfani,nima da Abban Amatullah ya barni ba abinda zai hana ni aiki"
Nadia ta ce"ina Suhail yayi aure kuwa and You sister na'ima"
murmushi tayi ta ce"yayi aure ga matar sa nan ita ce na kawo"
"na'ima kuma tayi aure tana dutse"
murmushi tayi ta ce"wow masha Allah Amman Suhail ya iya zabe irin wannan kyakkyawar mata haka"
iman ma sai sa tayi murmushi
dr nadia ta ce"miya same ta"
Aunty Zarah ta kalli Iman ta ce"kiyi mata bayani"
da farko taji nauyi tunawa da tayi tazo dan neman lafiyarta hakan yasa ta ajiye duk wani nauyi da kunya a gefe ta fara yi ma Dr nadia bayani
cikin sanyin murya ta ce"munyi aure shekara biyu Amman har yanzu ban taɓa samun ciki ba"
dr nadia ta gyada kai cikin fahimta ta ce"kin taɓa miscarrage"
kai ta girgiza
"da kina budurwa an taɓa yi maki aiki ko kinyi amfani da family planning"
"a'a"
dr nadia tayi wasu rubuce-rubuce ta dago ta kalli Zarah ta ce"
Da farko ina so ki sani cewa rashin samun ciki cikin shekara ɗaya ko biyu ba yana nufin akwai babbar matsala ba"
“Amma dole mu yi bincike akan lafiyar ta duk da Binciken ba ma mace bane ita kadai,Amman zamu fara da ita idan akwai yiyuwar zuwan nasa zamu kirasa"
"bakomai nadia kiyi duk Abinda ya dace"
lab form ta dauko ta rubuta test kamar haka blood test,hormonal profile,pelvic scan and MRI bayan ta gama rubutawa ta kira nurse tsation a turo sister guda ta bata test din ta raka iman zuwa lab ta faɗa masu patient dinta ce tana bukatar result da wuri
"okay ma'am"
dr nadia ta dubi iman ta ce"ta bita"
suna fita ya rage daga dr nadia sai aunty Zarah suna hira nadia ke cewa ina ta bar yaran "Amatullah na makaranta,junaid kuma na wajen babansa"
"Masha Allah,Allah ya raya su"
"Amin, ina Mashkur ko yana makaranta don ko lokacin da suka yi karatu a ture nadia nada aure"
nadia ta girgiza kai tayi murmushi ta ce"yana wajen mahaifinsa tun bayan rabuwar mu ya taƙura akan lallai sai na bashi yaron sa"
ido Aunty Zarah ta zaro "nadia kun rabu fa kika ce"
kai ta jinjina ta ce"tun da na samu aiki ya matsa min akan na zaba ko shi ko aikina ni kuma na zabi aikina dan ya fiye min komai Zarah kin fi kowa sanin iyayena basu da karfi da aikin nan nake daukar gaba daya responsibities na parent dina hatta karatun ƙannena ni saboda haka nace kawai ya sauwake min "
Aunty Zarah ta jima tana mamaki miyasa maza suke haka basa kaunar rufin Asirin matayen su da sunga Wata dama tazo musu sai su fara musu ƙyashi da hassada dan a labarin data bata yanzu babu komai facce hassada da take damun mijin nata
ta bude baki ta ce"Allah yayi miki zabi mafi Alkairi"
ta amsa da "Amin"
sun jima suna hira kafin su iman suka dawo tare da result dakw liƙe a leda nurse ta miƙa wa nadiya ta fita
Iman ta rasa gane kanta tun fitar su zuwa lab taje jin faduwar gaba wanda a yanzu tafi tsananta fiye da ɗa
a hankali Dr nadia ta soma duba gwaje-gwajen ɗaya bayan ɗaya har ta kammala a iya mood din fuskar ta zaka gane akwai Matsala
Aunty Zarah ta ce"nadia explain to me"
zare glass din fuskar da tayi ta ce"i'm sorry to said Sakamakon scan da sauran gwaje-gwajen ya nuna alamun endometriosis"
comment
like
share