63
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----63
Shiru ya mamaye office ɗin
Kalmar da Dr. Nadia ta faɗa ta tsaya cak a kunnen Iman
“Endometriosis…”
Ta ji kamar ba ita ake magana da ita ba
A hankali ta ɗago idanunta ta kalli Dr. Nadia
ita kuma tata ƙaddara rayuwar a haka tazo mata ta yarda da cewa duk Abinda ka fiye so a duniya Allah yakan jarabbace dashi
"Allah ya bani ikon cinye wannan jarabawar"
Aunty Zarah ta dago ta kalli dr nadia ta ce"yanzu kina nufin bazata haihu ba kenan"
nadia ta Girgiza kai ta ce"Zarah ba haka nake nufi ba"
ta matso da kujerar gaba ta ce"ina so ku fahimta mata da yawa masu suna samun kici da endometriosis musamman na iman da yake a mataƙi na biyu wato stage two (mild)bai riƙa yayi karfi a jikin ta ba
hatta wanda suke a stage four a endometriosis suna samun haihu wasu idan anyi mata treatment wasu kuma a iya kan magani kadai ake dora su"
"kuma ita ma in sha Allah zamu dora ta akan magani"
wani nauyayyen lumfashin mai wuyar fita Aunty Zarah ke yi
Dr nadia na lura da yanayin su har iman dake zubar da hawaye
dr nadia tayi gyaran murya ta ce"Endometriosis wata cuta ce da ke faruwa idan wani nama mai fitowa a cikin mahaifa (endometrium) ya fara girma a wajen mahaifa, kamar a ovaries, fallopian tubes, ko wasu sassan ƙashin ƙugu"
ta ce"wannan ba wani serious issue bane Da zaku daga hankali mata da yawa suna fama dashi ba tare ma da sun sani ba kuma su haihu lafiya qlau"
wannan ciwon ba'a san takamaiman Abinda ke kawo shi ba amman bisa binciken wasu daga cikin likitoci sun ta'allaka akan ana iya gadon sa daga mahaifiya,da muna wani ɓangare na jinin al'ada dake shiga kugu wato(retrograde mesturation) ,matsalar garkuwar jiki,hormones musamman estrogens
wasu daga cikin alamomin ta kuma su ne mentural pain,jin zabi yayin saduwa,jin ciwo yayin bayan gida ko fitsari,wahalar samun ciki
kuma a yadda binciken ya nuna ciwon kamar ya daɗe a jikin ta tun kafin ma ayi auren su shiyasa gwaji lokacin aure yake da matukar amfani da tun lokaci ya nuna da anyi mata maganin sa kuma ma Zarah a yadda family din ku keda educative ya akayi hakan ya faru
Aunty Zarah ta ce"Auren yazo a ƙurarren lokaci"
jingina kai tayi ta ce"ya kamata shima Suhail din idan ya samu lokacin yazo a duba sa dagan sai a san maganin da za'a dorata akai
prescription Form ta dauko ta rubata drugs ta mika wa Zarah tashi suka yi zasu tafi har baƙin kofa dr nadia ta raƙo su zata koma aunty Zarah ta daga jaka ta ciro kudi masu yawa taba nadia ta ce"gashi ki kaiwa mama"
sosai nadia taji daɗin kudin ta ce"thank so much Zarah mama na godiya"
Zarah tayi murmushi ta ce"bakomai yiwa kaine"
suna fita daga office din aunty Zarah taba iman key din motar taje ta jirata achan zata shiga pharmacy ta amso drugs din
amsa tayi ta fice daga wajen tana tafiya Tamkar wanda iska ke shirin kadawa
ba jima ta dawo da ledar magunguna ta shiga suka kama Hanyar gida kiran Suhail ya shigo wayar aunty Zarah ta daga "Aunty ya Asibitin"
"Alhamdullilah suhail gamu nan ma a hanya zamu koma gida"
"okay,ko zaki ba iman wayar tuk dazu nake kiran wayar ta"
Aunty Zarah ta miƙawa iman dake zaune a front seat wayar ta ce"gashi Suhail zai yi magana dake"
amsa tayi ta kara wayar a kunne
"hello iman shine kina ganin kirana kika ƙi dauka i hope everthing is going well"
ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce"ƙayi haƙuri,na bar waya a mota Shiyasa"
"okay, ya naji Muryar ki so bored ko jikin"
Aunty Zarah ta amshe wayar daga kunnen ta ta ce"Suhail idan ka tashi daga office ina son ganinka"
"Aunty lafiya dai ko"
"Suhail koma minene idan kazo ai zaka ji"
ta katse wayar ta kalli iman data jinginar da kanta jikin kujera
a zahiri idanunta na kan titi amman a zuciyar ta tuni ta nisa cikin tunani da koma son nema wa kanta mafita
a haka har suka ƙarasa gidan iman ta dubi Aunty Zarah ta ce"zata je ɗaki ta kwanta kan ta na mata ciwo"
"okay,kije ki kwanta idan kin tashi zan kawo maki magani"
Dakin Amatullah taje ta kwanta Aunty Zarah tabi bayan ta da kallo jin Iman take tamkar ƙanwar da suka fito uwa ɗaya uba ɗaya ta tausaya mata halin da take ciki Allah kadai yasan yadda take ji a ranta a hankali ta furta "ya Allah ga baiwarka nan Allah ya kawo mata mafita"
mai aiki ta kira ta kawo junaid ta bashi mama ta maida mata shi ta shiga Kitchen ɗora abincin Rana
Bata jima ba taji sallamar Suhail ta fito da fara’ar Suhail har ka iso kenan
murmushi yayi ya ce"Aunty ba dole ba tunda kin riƙe min mata"
"kai suhail ko kunya ta ma baka ji, tunda haka ne sai tayi sati guda zata koma"
"tab Aunty Zarah kenan Ashe ko nima zan tattaro kayana gaba daya na dawo gidan"
pillow ta wurga masa ya kauce
ya haɗe hannayen sa waje guda ya ce"ayi haƙuri big Sister gani nazo"
gyara zaman tayi ta kallesa ido cikin ido ta soma baki labarin duk abinda ya faru a asibiti da mamakin ta sai ta ga ko damuwa ma baiyi ba
ya ce"Aunty amman dai bata jin ciwon komai"
kai ta Girgiza ta ce"baya mata ciwo,hasalima ai batasan tana dashi ba sai da muka je asibitin"
ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Aunty ba damuwa Allah ya bata lafiya iman Ko da Allah bai ƙaddara mana haihuwa ba, zan ci gaba da zama da ita daman ƙila tun farko Allah ya tsara hakan sai mu cigaba da addu'a kawai Allah yayi mana zaɓi na Abinda yafi zama Alkhairi a rayuwar mu"
Aunty Zarah ta ce"Amin"
ta jima tana kallon s dan batayi tunanin zai amshi Maganar da wasa ba amman ba abin mamaki bane Suhail mutun ne tawakkali da amsar ƙaddara a duk yadda tazo masa
a karo na biyu ta kai dubanta gare sa ta ce"Suhail ina so Maganar nan ta tsaya a tsakanin mu banaso ko mami ta san da wannan maganar"
murmushi yayi ya ce"ai nasan ko wacece mami bazan taba tunkarar da maganar in sha Allah”
"ai kafi kowa sheda halin ta,jiya ma munyi waya da Naima take faɗamin mami ta kira ta wai jikinta ya tashi tana so ta koma Asibiti"
suhail ya ce"nima ta kirani nama tura mata kudi sai zuwa weekend zan shiga"
Aunty Zarah ta ce"ka kyauta kam nima zan sami Abinda na tura mata kasan idan Mamii ta fiye jajajen ciwo kudi take so"
dariya sossai Suhail yayi ya tashi zai tafi
ta ce"Suhail ka jira kaci Abinci mana na kusa ƙarasawa"
"bana jin yunwa,idan iman ta tashi ki faɗa mata da magariba zanzo in dauke ta"
"to shikenan,sai ka dawo”
Idan kunyi comment da yawa da yiyuwar ku Samu update da dare🥹😩