64
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----64
Bayan Suhail ya fita daga gidan, Aunty Zarah ta jima tsaye tana kallon ƙofar da ya bi
Ta gode Allah da ya bata suhail a matsayin ƙani Suhail yana da zuciya mai kya tabbas iman tayi dacen miji na gari
ta juya ta nufi Dakin Amatullah Iman na kwace gefe guda, idanun ta abude ta zuba su kan p.o.p din dakin
Da alama tunanin da ke kanta ya hana ta ko lumshe ido
Aunty Zarah ta zauna kusa da ita
Ta shafa kanta cikin tausayawa
“Iman baki samu baccin fa kena"
murmushi tayi ta ce"nayi Aunty Zarah yanzu na tashi ma"
"yayi kyau,suhail ya ce sai da yamma zai dawo daukar ki"
kallon ta tayi ta ce"aunty yazo ne"
"eh, yanzu ma ya tafi ai"
ajiyar zuciya ta sauke
Amatullah ce ta shigo dakin hannun ta riƙe da school din ta da sauri ta nufo iman ta rungume ta tare da kai mata kiss a forehead "Aunty iman i'm back"
murmushi tayi ta ce"sannu da zuwa Amatullah ya school"
taɓe baki tayi ta ce"fine amman fa na gaji"
Aunty Zarah ta ce"to parrot faɗi ba'a tambayeka ba tashi kije ki cire uniform din"
haɗe fuska tayi ta tashi tacire uniform ta saka wasu jajayen pajamas riga da wando
da dare Suhail ya dawo ɗaukar iman Amatullah ta sa rigima wai ita sai da ta bisu
Aunty Zarah ta ce"Makarantar fa Amatullah"
"ni,momy sai na bisu Uncle zai kaini daga daga chan"
duk lallashin duniya babu wanda ba'ayi mata ba amman bata jiba Suhail ya dube ta ya ce"kiyi haƙuri idan aka yi hutu da kaina zan zo na dauke ki"
share hawayen ta tayi ta ce"promise me Uncle"
murmushi yayi ya ce"i promise You dear"
Amatullah ta ce"to nayi haƙuri"
Aunty Zarah ta girgiza kai ta ce"Amatullah ban san ranar da za kiyi hankali ba kina nine years old amman yanzu haka junaid ya fiki hankali"
suhail ya ce"Aunty Zarah allow my girl to rest"
Iman da ke tsaye gefe tana kallonsu ta kasa hana kanta murmushi A karo na farko tun bayan fitowarsu daga asibiti, ta ji zuciyarta ta ɗan yi haske
har baƙin bakin gate su aunty Zarah suka tafi
har suka isa gida babu wanda ya ce da kowa komi lokaci zuwa lokaci iman ke satar kallon fuskar Suhail babu wani chanji a tattare da shi
sai natsuwar sa da kullum zaka samshe cikin ta
a haka har suka ƙarasa gidan
koda suka shiga falon Suhail ya zauna kan kujera ya dubi iman ya ce ta hado masa tea yunwa yake ji
mayafin kawai ta ajiye ta nufi Kitchen cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa masa indomie da chocolate tea ta doro a tray ta kawo masa ta haura sama
gidan yayi shiru ko giccin jennifer bata gani ba a zaton ta ko sun fita unguwa tare da Zeenah
dakin ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel rigar bacci ta zura ta gabatar da Sallar isha'i wayar ta ta dauko tayi dialing Number Malan Abdullah mahaifinta
har ta katse baay daga ba sai bayan ta kira ne ta tuna da Yanzu yana kofar gida tare da ɗaliban sa
lambar Hafsat ta ƙira Ringing biyu ta daga
"iman,ya kike kwana biyu"
"lafiya qlau Hafsat,kwana biyu ko nema na ma bakya yi"
murmushi tayi daga nata ɓangarem ta ce"Iman kinsan mun fara exams din second semester to gaba daya hankali na kan karatu"
jinjina kai iman tayi ta ce"Allah ya bada sa'a,our future nurse,ina Aunty Zaituna"
"ta raƙa abba asibiti,kinsan ƙwanan nan jikin nasa sai a hankali"
Iman ta ce"Subuhanallahi Allah ya bashi lafiya"
Hafsat ta ce"Amin ya Allah,ina yaya Suhail"
"yana nan lafiya"
"ki gaida shi"
iman ta ce"Zai ji in sha Allah ki gaishe Abba da jiki"
tana kashe wayar kiran Malan na shigo wayar
dauka tayi suka gaisa Mallan ya ce"Khadija ya mai gidan naki"
"Alhamdullilah Abba"
a yadda tayi maganar malan ya fuskanci kamar tana cikin damuwa
"Khadija ko wani abu na damunki ne"
ajiyar Zuciya ta sauke bata da wanda ya dace ta fadawa damuwarta fiye da iyayen musamman malan ko zai taya ta da addu'a
nan ta soma bashi Labarin duk abinda ya faru a Asibitin da kuma ciwon da ake hasashen tana da shi
cikin kuka take masa bayani har ta kai karshe malan ya rasa ma ta ina zai fara
babu Abinda yake furtawa a ƙasar zuciyar sai
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…”
Ba don ya ɗauka abin ya fi ƙarfinsu ba, sai don ya tuna cewa kowace jarabawa daga Allah take.
A hankali ya ce,
“Khadija…”
Ta share hawayenta
“Na’am Abba"
Ya ce cikin nutsuwa
“Da farko ki daina zubar da hawaye Ba likita ba ne yake bayar da haihuwa, Allah ne,Likita yana gano matsala ne kawai, amma magani da waraka duk daga Allah suke"
Shiru ta yi tana saurarensa
Ya ci gaba da cewa
“Kin tuna labarin Annabi Zakariyya (A.S)? Ya yi shekaru masu yawa yana roƙon Allah kafin aka ba shi Yahya Haka kuma akwai mata da yawa da likitoci suka ce ba za su haihu ba, amma Allah Ya ba su zuri’a mai yawa"
“Saboda haka ki ci gaba da magani, kada ki bar addu’a ki yawaita istigfari ki yawaita karanta Suratul Maryam da Suratul Al-Anbiya Kuma ki yarda da ƙaddarar Allah tunda koda ya hallicce bai yi ba kowa Alƙawarin haihu ba kamar yadda baiwa kowa Alƙawarin arziki dan haka ko kin samu kanki a cikin su kar yi tunanin kamar Allah baya tare dake ki zama mai yawan godiya a garesa kila yayi miki wani babban tanadin ne a gaba"
Sai da ya ɗan yi shiru kafin ya tambaye ta "shi Suhail din ya ce wani abu"
kai ta Girgiza tamkar tana gabansa ta ce"bai ce komai ba"
"to Alhamdullilah Allah yayi muku albarka khadija na yaba da halin mijinki kuma tun da kika zo Duniya,miji irin Suhail nake fatan Allah ya baki kuma Allah ya amshi addu'a ta kina zaune a gidan mijin ki lafiya qlau"
Hawayen Iman suka sake zubo, amma wannan karon ba na baƙin ciki ba ne
Na jin cewa har yanzu akwai mutanen da suke tare da ita
sai ya tabbatar ta kwantar da hankalin ta ya ce"Maryama ta faɗa miki an gama haɗa kayan lefen Mubarak ko"
"a'a Abba ina ganin ta manta ne,ya kamata idan kin samu lokaci mijin ki ya kawo ki , ki gani dan cikin satin nan za'a kai su kano chan gidan su yarinyar "
"to,Abba Allah ya tabbatar da Alkairi ya kaimu Lokacin lafiya"
"Amin ya Allah"
Malan ya katse wayar
tana zaune bakin gado taji an turo kofar dakin
ido biyu suka haɗa Suhail
like
comment and share
wallahi inajin daɗin yadda kuke bibiyar littaffin nan ina godiya matuka