65
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----65
bakin gadon ya nufo kallo ɗaya yayi wa fuskar ta ya tabbatar da kukan da tayi
zama yayi kusa da ita har suna iya jiyo numfashin junan su
"iman"
ɗago jajayen idanun ta tayi ta zuba su cikin nashi
"kukan me kikayi"
kai ta Girgiza
"ni ban yi kukah ba"
"iman yaushe kika fara min ƙarya"
Kunya da takaici suka haɗe mata
Ta sauke kanta ƙasa ba tare da ta sake cewa komai ba
fuskar ta ya ɗago da hannun sa
Har yanzu hawaye na maƙale a gefen gashin idanunta
Ya share ɗaya daga cikinsu da babban yatsansa
“Saboda abin da likita ta faɗa ne ko"
kai ta girgiza masa
"a kan sane mana iman, Shiyasa tun farko banso kika bi aunty Zarah Asibiti ba"
"ban faɗa bane saboda banaso tayi tunanin ko banyi appreciating kudirin ta akan mu ba"
"iman a ciki banga abin tada hankali zeenah ma bata haihu ba amman bata daga hankalin ta kamar yadda kikayi ba"
share hawayen fuskar ta tayi ta ce"yaya Suhail bana so wata rana kayi danasanin aure na tunda bana haihuwa ina karantawa a littattafai sannan ina kallo a fina finai duk macen da bata haihu ba mijin ta tsanar ta yake"
suhail ya ce"shine aka ce maki nima zan tsaneki,iman daidai da rana daya ban zan taba tsanar ki dan kawai Allah bai baki haihuwa ba"
"ban aureki dan kawai ki haifa min yara ba,na aure kine bisa umarnin mahaifina da ya zaba min Saboda wasu daga cikin kyawawan halayen ki,wanda kullum su ke kara kusanto zuciyata zuwa gare ki kuma har gobe ina ƙara godewa Abba da zafin da yayi min"
"i love You more words can ever explain my Father choose my My Qurratu Ayni Haƙiƙa ke haske ce a cikin zuciyata tunda kika shigo Rayuwa iman komai nawa ya zama daidai nake jin kamar kin zama wani ɓangare na jikina da bazan iya rayuwa babu ke ba"
"and i promise I will forever be suhail you councel you protector and You big supporter"
murmushi tayi jin sunan my councel daya kira
hannun ya kamo ya saka cikin nasa ya ce"kar ki taɓa tunanin dan baki haihu ba zan chanza maki babu wata mace da zata maye gurbin ki a zuciya ta koda kuwa dan gold ko diamond zata haifa min You are my peace, my safe place, and my home.
ta ƙasa dago ido ta kalle shi
kalaman Suhail na cigaba da yawo a cikin zuciyar ta
hawaye ke san zubo masa amman wannan karin na farin ciki ne
a hankali ta kai duban sa gare ta
"yaya Suhail"
"Nagode Allah daya bani kai a Matsayin miji ko a mafarki ban taɓa tunanin zan sami mutun mai irin halin ka ba ,yaya Suhail ka fita daban a cikin maza Allah ya bani ikon da zan faranta tare da bani ikon sauke nauyin dake kaina"
murmushi yayi ya ce"now promise me bazaki kara damuwa kan wannan issue din ba"
murmushi tayi ta ce"nayi maka"
ya mike tsaye ya ce"wipe those beatiful eyes"
ta share hawayen
a ranar sun zama tamkar damuwa bata taɓa samun ma zauni a zukatansu su ba
wannan daren ba kamar ko wani dare yake a wajen su ba
A wannan daren, ba su sake barin damuwa ta mamaye zukatansu ba Sun yanke shawarar rungumar ƙaddarar Allah da kyakkyawan zato, suna ƙarfafa junansu da kalaman bege da addu’a har dare ya yi musu riga
washe gari
tun da safe Suhail ya fara shirin tafiya kaduna duk bai sanar da iman ba
ta gama gyaran gidan kenan ta nufi Kitchen taji fitowar sa
sanye yake da wani light blue din yadi yayi matukar karbar jikin sa cike da natsuwa ya kara kofar Kitchen iman ta kallesa
"yaya Suhail ina kuma zaka je da safe nan"
"i'm sorry na manta ban faɗa maki ba mami ce bata da lafiya zanje in dubata sai daga nan kuma in dauko zeenah"
kai ta jinjina tare da cewa "Allah ya bata lafiya"
ya amsa da "amin"
"Amman,ai da ka bari ko breakfast ma kayi kafin ka tafi"
"Nagode,idan naje chan nayi"
har bakin gate tayi masa rakiya tare da addu'ar dawowa lafiya tana kallon motarsa har ta ɓacewa kallon ta kafin ta koma ciki"
tea kawai da bread ta hada ma kanta dan shi kadai zata iya ci
ƙarfe goma ya iso garin kaduna
ya doshi hanyar gidan su a kofar gida yayi parking motar sa yayi knocking baba haladu ya buɗe masa kofa
fuskarsa dauke da annuri ya bashi hannu suka gaisa "Mutan habuja sannu da zuwa"
murmushi Suhail yayi ya ce"sannu baba haladu ya aiki"
"Mun gode wa Allah ya aka baro iyalan"
"duk sunan nan lafiya qlau"
suhail bai jira baba haladu ya kara magana ba ya shige ciki
part din mami ya nufa babu kowa a falon ƙasa ya nufi upstair
mami ce zaune a kan carpet ƙafarta naɗe da bandage tun daga gwiwar ta har zuwa ƙafrin ta duka a naɗe yake da sauri Suhail ya karasa ganin mahaifiyar sa cikin wannan yanayin bai taɓa tunanin ciwon nata ya kai haka ba
koda yayi sallama bata ɗago ta kallesa har ya ƙarasa gaban ta
"Mami ina wuni ya saukin jikin"
"jiki da sauki Suhail ,sai yau matar taka ta baka umarnin kazo ka dubani ko kuma sai yau ta baka izinin tuna kana da uwa"
da mamakin ya kalleta "haba mami har akwai macen da zata shiga tsakani da ke"
"Akwai mana Suhail tun last week na kiraka akan banda lafiya Amman la kasa zuwa sai kudi ka tura min sai kace an ce maka talauci ya dame ni"
ƙasa yayi da murya ya ce"kiyi haƙuri Mami bansan ciwon naki ya kai haka ba"
Mami ta ce"haka dai kullum ayi haƙuri ayi haƙuri kuma ka kasa chanza halin ka"
shiru ya ratsa tsakanin su kafin Suhail ya ce"Mami mi zai hana a fita kasar waje a nake ganin kamar zama anan babu wani progress da ake samu"
kai ta girgiza masa
"babu inda zanje Suhail, wannan ciwon sugar nawa gado nayi a wajen mahaifiyata babu kasar da bata je neman magani ba amman daga ƙarshe sai da ta rasa kafaffun ta duka biyu to ka barni anan nima zuwa yadda Allah zaiyi"
"Allah baki lafiya yasa kaffara ne"
"Amin"
"ka duba dining akwai Abinci in zaka ci"
murmushi a ransa ya ce
mami kenan Abu daya da yafi birgesa da ita duk halin ta tana matuƙar kaunar yaran ta
batason wani abu ya same su ta yadda ita tayi musu duk abinda yaga dama amman matukar aka taɓa mata su sai inda karfin ta ya kare ,gashi har gobe kallon yara take masu musamman suhail da take jin son da take mashi yafi na sauren linƙuwa
musamman da idan akayi la'akari da duk cikin yaranta yafi kowa kyautata mata
shine tsaye a kan lafiyar ta bai damu da sai ya jira mahaifinsa yayi ba da kudin shi da jikin sa yake fafutukar nema mata lafiya
har ya tashi zai fita ya ce"Mami zeenah ta zo ne"
"tazo jiya,tama jima sossai ai ita ta damu da lafiya ta"
bai kara magana ba ya fita dan ya gane point mami ke san zuwa
bayan ya gama cin Abinci ya nufi part din Abba yana zaune a falo yana kallo news a tv sun jima suna hira har Abba ke tambayar sa dalilin daya sa baizo da iman ta duba mami ba ya ce jiya suka dawo daga Asibiti ma bata da lafiya
Abba ya ce"subuhanallahi,Allah bata lafiya "
ana yake tambayar Abba aunty Fauziya ya ce"taje gida yayanta ke aurar da ƴar sa "
a ranar haka ya wuni yana yawo cikin Kaduna gidan Sameer ya fara zuwa bayan ya biya wani shopping mall yayi siyyayya ya hado ma Nasreen chocolate kala-kala masu tsada ya kaii mata
Maryam ta ce "ai na dauka tare zaku zo da iman"
ya ce"bata da lafiya"
sameer ya ce"aiko ya kamata muje mu dubata dama bamu taɓa zuwa ba"
Suhail ya ce"ya dai kamata kam"
har la'asar yana gidan Sameer dan anan ma yaci Abincin rana
yana fitowa ya kama Hanyar gidan malan cikin Sa'a ya same shi kadai a kofar gida duk yadda malan yaso su shiga gidan Suhail ya ce sauri yake zai koma Abuja
kudi maau yawan gaske Suhail ya ajiye a gaban Malan ya ce"Malam gashi wannan an ƙara a hidimar biki"
ido malan ya girgiza kai ya ce"Allah ya sauwake shi bazai amsa ba yaji da hidimar da yake dasu kadai ta isa"
Suhail ya karya murya ya ce"haba Malan ashe baka dauke ni a Matsayin ɗa ba indai har baka amshi kudin nan ba zanyi tunanin kana min kallon siriki ne kawai"
"Malan,ko babu abinda ya hadani da kai zan iya yi maka abinda yafi haka na roƙe ka da Allah ka amsa,ko ke faɗa mana cewar shedan ne kadai ke maida hannun kyauta baya"
jin haka yasa ya amsa wasu kudin daban da basu kai na malan ba ya bashi gashi wannan kuma aba Ammi
malan ya ce"Kuma,kai dai baka gajiya"
bayan ya tashi zai tafi ya sami yara ya daga boot din motar sa suka fito da tullin kayan Abincin da ya siyo suka shiga dasu ciki
malan tsabagen Mamaki har ya kasa magana
Suhail bai koma wajen saba ya shiga motar sa yayi gaba
ya nufi gidan su Zeenah
like
share and comment