66
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
🅿️—66
Da isarsa, security suka buɗe masa gate ɗin gidan Ya shiga har zuwa babban falon
A ciki ya tarar da Mommy mahaifiyar Zeenah, zaune kan kujera yayin da mai aikinta ke rubuta mata jerin kayan da za a saya a kasuwa
Da sallama ya shiga
Cikin fara’a Mommy ta ɗago kai ta ce
“Suhail… kai ne a tafe?”
Murmushi ya yi
“Mommy, ina wuni?”
“Lafiya lau Ya matar taka? Fatan tana lafiya?”
“Alhamdulillah"
Ta miƙe tsaye
“Bari na kira maka Zeenah"
Bai jima da zama ba…
Aka turo ƙofar falon
Zeenah ce ta fito
Sanye take cikin wata farar elegant abaya da ta matuƙar karɓi fatar jikinta
Ƙamshin turarenta ya mamaye falon tun kafin ta iso gabansa
Suhail ya ɗaga kansa
Idanuwansu suka haɗu
Na wasu sakanni ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta
Kwana biyun da suka yi ba tare da ya ganta ba, sai ya lura ta canza
Ta ƙara ƙiba kaɗan
Fuskarta ta ƙara wani irin haske da walwala…
Tamkar ba ita ce Zeenah ɗin da ya sani ba fuskar dauke da annuri
Ta ja kujera kusa da shi ta zauna, tana taunar cingam cike da kasaita
Da ya lura ba ta da niyyar ko gaishe shi, sai ya ce" Zeenah gaisuwar ma sai na roka"
hade rai tayi "kai yaya Suhail komai sai kayi ƙorafi"
bai ƙara magana ba ya tashi"idan kin gama ina waje"
ya fita ya koma cikin mota ba jimawa jennifer ta soma fito masu da kayan su
zeenah ta shiga daƙin momy yi mata sallama anan ma sai da tayi mata faɗa duk ta lura a wannan zuwan zeenah kamar ta rage rawar kai
karfe takwas na dare suka shiga garin Abuja
zeenah ta ce"su biya ya siya mata gas fish"
da mamaki yake kallo ta a iya sanin sa zeenah bata cin kifi har ya kasa Daurewa ya ce"zeenah yaushe kika fara cin kifi"
kwabe fuska tayi ta ce"jiya aka siyo ma momy naga ya birge kuma inaso inci"
Suhail ya hade gira ,tun iya sanin da zeenah yasan ko kamshin kifi bata son ji amman miya chanza ta haka
kai ya gyada ya ce"okay"
wajen masu siyayyar da gas fish yayi parking ya leda ukku ya sa ayi masa koda ya dawo ya mika mata leda biyu ya ajiye gudar a seat din baya hararsa tayi sanin iman ce ya siya ma gudar
ta watsa ma jennifer dake baya ledojin ta riƙe mata
basu ƙara tsayawa ko ina ba sai gida da kanshi ya fito ya buɗe gate din ya shiga da motar ta
yana parking zeenah ta buɗe mota ta fita jennifer ce ta shigar masu da kayan ciki
iman na tsaye a dinning area tana jera kulolin abincin zeenah ta fara shigowa
kamshin girkin dake tashi a wajen ya sata dakatawa tana kare wa warmers kallo tare da san sanin Abinda ke ciki
cikin babu wanda ya kula wani duk chan magana bawai ta cika hadasu bane.
zeenah taji duk duniya sai taci Abincin nan ne kawaii hankalin zai kwanta ga wani tashin zuciya da take fama dashi
haka ta kama Hanyar dakin ta, jennifer ta biyo bayan ta ta ajiye kayan zata koma dakin ta
zeenah ta kirata"jennifer kinsan Iman ke girkawa"
kai ta girgiza ta ce"ban sani ba hajiya ko naje na tambayeta ne"
"a'a ki barshi idan Suhail ya shigo zan sashi ya amso min"
sallamar Suhail ta katsewa iman tunanin da take akan chanjin data gani tattare da zeenah
ya shigo falon yana cire agogon dake hannunsa
ido biyu suka haɗa da iman ya sakar mata waki cool smile ya ce"my busy wife"
itama murmushi ta mayar masa tare da yi masa Barka da dawowa
"yaya Suhail,ya jikin mami"
"jikinta da sauki"
"Allah ya bata lafiya"
"Amim" ya miƙa ledar gas fish ta masa tayi masa godiya
zai nufi Dakin kenan jennifer ta ce masa "hajiya na Magana"
kallon ta yayi ya ce"me zan mata kuma bayan tare muka dawo"
"nima ban sani ta ce"idan ta shigo na faɗa maka"
tsaki yaja ya nufi dakin ta bai manta da yadda ta wurga ledar kifin da ya siya mata ba Kamar ma batayi appreciating ba kuma hakan baida nasaba da siyawa iman da yayi
a tsakar daki ya iske ta sai safa da marwa take ta ƙasa tsugum da ranta
da sauri ta sha gaban sa ta ce"yau wa Suhail dan Allah ka amso min Abincin cin chan na wajen iman wallahi yunwa nake ji"
"yunwa ,kuma keda ma ba girkin ta kike ciba ko kin manta ranar data fara girka Abinci ta baƙi kika ce bazaki ci Ƙazantaba ko kin manta order kikayi Yanzu ma ai sai kiran su su kawo maki nikam bazan je ba"
ya juya zai fita ta riƙe hannunsa ta ce"Dan girman Allah ka amso min wallahi Suhail idan banci ba komai zai iya faru wa"
janye hannunsa yayi ya buɗe kofar ya fita
har ya nufi dakin sa sai yaji ya ƙasa daurewa ya koma wajen Iman dan baisan miya samu Zeenah ba ta fara fito da wasu sabbin halaye da da bata dasu
Suhail ya sauke numfashi a hankali
“Iman… Zeenah tana son ta ci girkin ki.”
Iman ta ɗago tana murmushi.
“Ai ba sai ta tambaya ba. Ta zo mu ci tare mana.”
Murmushi ya bayyana a fuskar Suhail.
“That’s why I admire you, Iman.”
Ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa,
“Please… ki zuba mata. Bana jin za ta iya fitowa ta ci a nan saboda kunya.”
Iman ta jinjina kai.
“Ba damuwa.”
Ta buɗe warmer ɗin, ƙamshin miyar ya sake bazuwa a falon.
Ta zuba abincin cikin plate tare da haɗa mata ruwa.
Ta miƙa masa.
“Ga shi.”
Ya karɓa yana kallonta na wasu daƙiƙu.
“Thank you, my kind-hearted wife.”
Murmushi kawai ta yi tana kallonsa har ya juya ya nufi ɗakin Zeenah
like
share and comment
khadywrites taku ce