BARRISTER SUHAIL

67

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


Gsky comment dinku ya bani dariya masu cewa cikin zeenah bana Suhail bane da masu cewa Allah yasa tayi miscarrage to duk ku biyo ni a cikin littafin dan kuji yadda zata kasance ina kaunar masoyana masu bibiyar littaffin Barrister suhail Allah ya hadamu a aljanna baki daya 

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----67

tana zaune a inda ya barta tana ganin sa ya shigo da plate mai dauke da shinkafa da miya sa sauri ta miƙe ta amsa 

kan kace mi ta saka spoon ta soma ci hannun Baka hannu ƙwarya idan zaka yadda take cin Abincin zaka rantse dui wunin yau ba Abinda ya shiga cikin ta 

Suhail ya jingina da ƙofar dakin yana kallon ta har ta cinye abincin tass

ta ajiye plate din Suhail ya ce"ko kina bukatar ƙari"

kai ta girgiza masa 

ya dauki plate din ya fita dashi

dakin sa ya koma yayi wanka yayi ya gabatar da sallar la'asar din da bai samu damar yin ta a jam'i ba 

bayan ya gama ya fito dinning ya ci abinci ya koma dakin Zeenah dake karɓar girkin ta yau 

tana zaune inda ya barta duk a'lamun rashin lafiya duk bayyana a fuskar ta Suhail ya zauna kusa da ita ya kalleta ido cikin ido ya ce"zeenah mike samun ki its seem like kamar baki da lafiya,kin chanza gaba daya"

rau-rau tayi da ido ta ce"nima ban sani ba suhail amman dai nasan bana jin dadin jikina ga wani irin craving dake damuna"

jinjina kai yayi ya ce"ki tashi kiyi wanka ki kwanta gobe sai mu je asibiti"

tashi tayi a hankali ta nufi bathroom

daren ranar yadda suka ga dare haka suka ga rana haka zeenah ta kwana tana Amai duk abinda taci a ranar gaba daya sai da ta dawo dashi 

hankalin Suhail ba ƙaramin tashi yayi ba,baya son Ganin mutun a halin Rashin lafiya ba kamar irin ta zeenah da dukkan a'lamun tana ji a jikin ta

Allah Allah yake gari ya waye su tafi asibiti dawowar sa daga masallaci kenan ya koma dakin ya tashe ta ta yi wanka ta dan jin kwarin jikin ta hakan yasa ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wata bakar Abaya 

yau ko damar kwalliyar ma bata samu ba Abinda zaiyi wuya ka gani babu Ranar da zaka kalli Zeenah ba tare da kwalliya a kan fuskar taba ko zata kwantar bacci sai tayi wannan make up din suhail ya sha yi mata magana amman bata daina wa

suna fito ya gamu da jennifer tana jera breakfast sai a lokacin ya tuna da iman da rabon sa da ita tun jiya da ya amsar wa zeenah Abinci

ya kalli jennifer ya ce"idan iman ta saukowa ki fada mata munje Asibiti"

risinawa tayi cike da ladabi ta ce"okay sir"

da kanshi ya buɗe mata kofa motar ta shiga Abinda ba kasafai ya saba yi mata ba kenan

bai tsaya ko ina da ita ba sai wani dan karamin clinic dake kan kusa da unguwar su 

koda yayi musu bayanin Abinda ya sami zeenah take aka dauki jinin ta zuwa dakin awo

batare da bata lokaci ba aka dawo da result likita na buɗe yayi murmushi ya kalli Suhail ya ce"congratulation sir You mr.zeenah  is six weeks pregnant"

Suhail jin maganar yake Tamkar a mafarki "zeenah is pregnant"

Suhail ya zuba wa likitan ido.

“Excuse me, Doctor… what did you just say?”

Likitan ya sake murmushi

“Mrs,Zeenah is six weeks pregnant.”

Na wasu daƙiƙu Suhail ya kasa magana Idanunsa suka koma kan Zeenah, zuciyarsa na bugawa da sauri 

idanunsa suka sauka kan zeenah 

ya rasa zuciyarsa mi take saƙa masa farin ciki ne ko aka sin haka abun ya zo masa ne babu zato babu tsanmani 

likitan ya ce"From her condition, everything looks stable for now Sai dai tana buƙatar kulawa sosai a wannan stage din Cravings, vomiting da gajiya duk alamu ne na pregnancy"

tana bukatar kulawa,har zuwa lokacin da zata fita daga wannan stage din 

Suhail ya juya ya kalli Zeenah

Ita kuma kanta a sunkuye yake
Bata ce komai ba

Ya lura hannayenta na rawa kaɗan

Likitan ya ci gaba da magana
duk lokacin da taji wani chanji zaku iya dawo domin duba lafiyar ta 

Kai kawai Suhail ya iya jinjinawa

Bayan sun fito daga office ɗin likitan…

Har yanzu shiru ne ya mamaye tsakaninsu

Ya buɗe mata ƙofar mota
Ta shiga

Shi ma ya shiga ya zauna a seat ɗin driver

Amma bai kunna motar ba
Ya jingina da seat yana kallon steering
Zeenah ce ta karya shirun 

“Yaya Suhail are You not happy for the pregnant,na zaci zakayi murna ne na baka Abinda matar ka ta kasa baka,ko kana baƙin ciki da ba matar ka bace ta samu cikin"

Suhail ya kalleta"zeenah why All this,ba wai bana farin ciki bane i'm just wondering "

"and let me give you a warning,ba ruwan ki da iman Itama i hope watarana zata samu nata in sha Allah"

"tsaki kawai taja tare da kai masa harara"

kuyi haƙuri da wannan na yi saboda jiya banyi masu tambayata Alhamdullilah ina lafiya 





like share and comment