BARRISTER SUHAIL

68

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----68



Har ya yi niyyar ya yi mata magana, sai kuma ya tuna inda suke da kuma abin da ya kawo su wajen Hakan ya sa ya haɗiye maganar da ke bakinsa, ya kunna motarsa suka kama hanya.

Da suka isa gida, yana parking, Zeenah ta fito daga motar da sauri ta nufi ciki, tana ta zunɓuro baki

Suhail ya bi bayanta da kallo na ɗan lokaci, kafin shi ma ya shiga cikin gidan

Kai tsaye ɗakin Iman ya nufa

Ya tarar da ita zaune kan prayer mat Ta gama nafila kenan,tana karatun Alƙur’ani cikin nutsuwa

Da ya shiga, ta ɗago ta kalle shi

Ba ta yi masa magana ba

Shi ma ya tsaya yana kallonta

Sai da ta kammala shafin da take karantawa gaba ɗaya, ta rufe Alƙur’anin cikin girmamawa, ta ajiye shi a gefe

Idanuwansu suka haɗu

Na wasu daƙiƙu babu wanda ya furta komai

Daga ƙarshe, ita ce ta karya shirun ta hanyar ce wa 

“Yaya Suhail…”

Ya amsa da

“Na’am iman"

Cikin sanyin murya ta ce

“Jennifer ta ce kun je asibiti… Ya jikin Zeenah?”

“Da sauƙi, Alhamdulillah"

Sai ta ɗan yi shiru

Ta lura yadda fuskarsa take, tamkar akwai wani abu da yake son faɗa amma ya kasa

A karo na biyu ta sake tambaya cikin damuwa

“Yaya Suhail… me ya same ta?”

Suhail ya sauke ajiyar zuciya

Ya zauna a gefen kujerar da ke ɗakin, yana shafa goshinsa da tafin hannunsa

Sai ya ɗaga kansa ya kalleta tausayin ta ya cika zuciyar ta 

A hankali ya ce

“Likita ya tabbatar…”

Ya ɗan dakata ya ƙasa fito da maganar dake kan harshen sa

“Zeenah tana da ciki"

Kalaman suka faɗi cikin ɗakin kamar ƙararrawa

Iman ta zuba masa ido

Na wasu daƙiƙu, ba ta motsa ba 

Ba mamaki ya bayyana afuskar ta  kadai ba hadda tausayin kanta da ya mamaye zuciyatar ta

Ba ta baƙin ciki da ƙaruwar da zeenah ta samu ko ba komai dan mijin ta zata haifa

Sai dai wani iri abu da taji a Kasan zuciyar mai nauyi

Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci dan kawar da kwallar dake ƙoƙarin zubo wa

A hankali ta ce

“Alhamdulillahi masha Allah"

Suhail ya ɗago ya kalleta da mamaki

Bai yi tsammanin wannan ne martanin da iman zatayi ba

Ta sake kallonsa, murmushi mai cike da tawakkali ya bayyana a fuskarta 

“Allah Ya sa cikin ya bata lafiya Ya ba ta sauƙin haihuwa… Ya sanya albarka a Abinda zata haifa"

Suhail ya ci gaba da kallonta cikin mamaki

A zuciyarsa ya ce

“Lallai Iman ta bambanta da sauran mutane"

hakan yasa ya janye wa zuciyar sa duk wani damuwa

tun lokacin da likita ya tabbatar masa da cikin Zeenah babu wanda ya fado zuciyarsa banda iman

ita ke ta fafutukar son haihuwa amman da allah ya tashi sai ya ba Zeenah

badon baya son iman ba sai dan ya jarraba karfin imanin ta 

"Allah kaba ta ikon cinye wannan jarabawar"

ya fada a ransa 

a fili kuma ya ce"duk ranar da zeenah ta haihu zan dauko baby na baki shi ki cigaba da kula da shi tamkar naki"

murmushi tayi ta ce"yaya Suhail da ka gama min komai a duniya amman kana gani zeenah zata yarda"

"zata yarda mana tunda bata san wahala"

tashi tayi daga kan Prayer mat din ta ce"aiko yaya Suhail dani za'a reni cikin nan bari ma kaga na tashi na hada mata tea"

Suhail ya bi bayanta da kallo.
A hankali murmushi ya subuce masa.
“Wace irin mace ce wannan?” ya faɗa a ransa
A duk lokacin da yake tunanin ya gama gano kyawawan halayen Iman, sai ta sake nuna masa wani sabon abu da ya fi na baya

tana fita yayi kwanta a kan gadon bacci yayi awon gaba dashi sakamakon jiya ya kwana baiyi bacci ba

iman na shiga Kitchen ta daura ruwan ta buɗe cupboard ta dauko cup da tray 

bayan ta tafasa ta juye tea din ta nufi Dakin zeenah ta dade a baƙin kofa tana shawarar shiga rabon da Dakin tun Ranar da aka kawo zeenah

daga karshe ta yanke shawarar ta shiga zeenah na zaune a bakin gado Gama wayar kenan da mummy ta faɗa mata tana da ciki 

ko kunya bata jiba ta dauki son duniya ta ɗorawa cikin nan dan a ganin ta ta samu makamin da zata maido hankalin Suhail gare ta

iman ta shiga daƙin cike da fargaba dauke da sallama a bakin ta 

duk da zeenah bata amsa taba amman bata damu ba ta ƙarasa kusa da ita ta ajiye tray din a kan side bed 

ta ce"Zeenah ya jikin,Allah ya sauwake ya raba lafiya daman tea na kawo miki"

wata harara zeenah ta wurga mata iman ta sunkuyar da kanta 

zeenah ta miƙe tsaye "ni na faɗa maki ina buƙata,oj anji ina da ciki ko shine kika je kika zubo wani abu a ciki in sha cikina ya zube ko to ta Allah bata ki ba"

"ai sannu a hankali zan kwato mijina daga hannun juya tunda kin kasa bashi Abinda ni na bashi,baki da wani aiki sai dai kici kiyi kashi"

"kina ji kina gani wallahi zaman gidan sai ya gagare ki, tunda daman chan ƙwaƙwaba masa ke akayi ba wai dan yana sanki ba ni kam shi yagani ya ce yana so"


"dan haka ki tattara kayan ki bar min daki kije chan ki cigaba da fama da rashin haihuwar ki"


hawaye kesan zubo mata Zuciyar tayi nauyi amman a haka ta ɗan ne duk Abinda zake ji matukar tayi kuka gaban zeenah zata ƙara rena ta ne kawai 

ta dauki tray din ta fita dashi dakin ta ta koma ta shige bathroom ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciya


irin wannan ranar take tsoro a Rayuwar ta gashi yau a gaban anyi mata gorin haihuwa an ƙira ta da juya sannan an faɗa mata Suhail bashi ya ce yana son taba tabbas idan ba Suhail ya fada ma zeenah taya akayi ta sani

kuka take Tamkar ranta zai fita kukan tane ya tashi Suhail daga baccin da yake

a hankali yake jiyo sautin kukan ta a bathroom

A hankali sautin kukanta ya fara shiga kunnen Suhail

Kuka mai cike da ciwo

Da sauri ya miƙe daga kan gadon
“Iman…”
Shiru
Ya nufi ƙofar bathroom ɗin

ya shiga kiran sunanta amman 

Har yanzu babu amsa

Sai dai kukanta da ke ƙara tsananta

Gaban Suhail ya faɗi

“Iman, ki bude kofar "

Ta share hawaye da sauri


Ta san halinsa.
Matuƙar ya dage, ba zai bar wajen ba
A hankali ta buɗe ƙofar

Suhail ya tsaya cak

Idanunta sun kumbura sossai

Fuskarta ta jike da hawaye

Ba tare da ya yi wata-wata ba ya kamo hannunta ya fito da ita daga bathroom

Ya zaunar da ita bakin gado

“Wa ya ɓata miki rai?”

Kai ta girgiza

“Babu kowa"

“Iman…”

Ya kira sunanta cikin sanyin murya

“Ki daina ƙoƙarin ɓoye min komai"

Na san wannan ba kukan ba a banza kike yin sa ki faɗamin mike faruwa?

Hawayen da take dannewa suka sake zubo mata

ta janye hannun ta daga rikon da yayi mata "yaya Suhail dan Allah ka kyaleni"

Suhail ya kasa danne wa zuciyar sa 

"zeenah ce ko?"

bata kara ce masa komai ba 

Suhail ya yi shiru

Sai dai zuciyarsa ta fara tafarfasa

Ya san Zeenah sarai

Ya kuma san Iman ba irin macen da za ta yi kuka ba tare da wani ya taɓa zuciyarta ba dan duk Abinda zai sata kuka ba ƙaramin abu bane


A hankali ya miƙe tsaye

ya fita zuwa dakin zeenah


shin kuna ganin Suhail zai iya yiwa zeenah magana ko kuwa?


like 
share and comment