BARRISTER SUHAIL

69

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----69


har ya kai kofar dakin sai kuma ya fasa wani tunani yazo masa Yanzu zeenah kula take buƙata ba maganar tashin hankali ba 

hakan yasa ya koma Dakin sa ba tare da yayi mata magana ba 

wunin ranar haka kowa ya wuni a nasa dakin iman har yanzu kuka take anzo gabar da ta kasa bai wa kanta hakuri 

kalaman zeenah ke cigaba da mata yawo a kai

"ta kirata da juya"

Sannan tayi mata gorin ba Suhail bane yana son ta

sai da tayi kukan ta mai isar ta ta tashi ta nufi bathroom ta wanke  fuskar ta 

kiran Ammi ya shigo wayar ta

ƙoƙarin kawar da damuwar kan fauskar ta tayi tare da saisaita Muryar ta ,ta yadda kar Ammi ta gane tayi kuka 


"Assalamu alaikum ammi ina wuni"

"lafiya qlau Iman ya gidan da fatan kowa na lafiya"

"Alhamdullilah Ammi"

"dama na kira na tambayeki ranar da zaki zo kinga biki sai gaba towa yake duka duka baifi sati biyu ba"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Ammi in sha Allah sati mai zuwa zan taho"

"to Allah ya kawo ki lafiya,ki gaida Suhail din"

Tana ajiye wayar ta bita da kallo ji take kamar ta janyo satin ma yazo tayi tafiyar kaduna 

ba karamin  buri ta azawa bikin yaya Mubarak ba yana ɗaya daga cikin bukukuwan da take fatan gani tun tana karama 
daga nashi sai na Hafsat 

ganin bata da wani aiki yasa ta tashi ta haɗa kayan tsab a trolley ta ajiye a gefe har zuwa ranar tafiya

sai da Suhail ya kwana biyu a dakin zeenah ya koma dakin iman 

a daren ranar zeenah kwana tayi kiransa a waya wai yazo bata da lafiya ya, yazo ya kula da ita 

tun yana kashe wayar idan ta kira har sai da ya tashi ya kalli iman dake kwance a gefen sa 

cikin sanɗa ya fita daga ɗakin 


sai dai baiyi tunanin idanunta biyu ba tashi tayi zaune ta kunna gajeren haske tabi Kofar da kallo

kuka take san yi amman ta danne zuciyar ta ta ƙasa jurewa abinda Suhail yayi mata 

ko a baya da yake tsanin nuna mata kulawa bata taba barin ya kwana a dakin ta  ranar girkin zeenah 

gudun kar Allah ya kama su da laifin tauye mata hakki 

amman ta lura zeenah bata tashi matsa masa sai ta lura da ranar dake da girki 

hannun ta ta daga sama ta ce"ya Allah kar ka kama yaya Suhail da laifin daya aikata min a yau na yafe masa duk wani abu da yayi min dama wanda zaiyi min anan gaba"

kwanciya tayi amman Bacci ya gagare ta 

tun kwana biyun da suka wuce baccin ma neman sa take ra rasa haka take kwana sallah da karatun Alqur'ani 

yau din ma haka ne saukowa tayi daga kan gado ta nufi bathroom tayi alwala ta fito ta jira jalbab din kan rigar bacci jikin ta ta fara sallah 

sai gab da sallar Asubah bacci yayi awon gaba da ita

Kiran sallar Asubah ne ya farkar da Suhail

Da sauri ya buɗe idanunsa

Ya kalli Zeenah

Tuni ta koma bacci bayan amai da ciwon da ya dame ta cikin dare

Ya sauke numfashi

A hankali ya tashi ya nufi alwala

Bayan ya idar da sallah a masallaci, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa 

koda ya dawo Kai tsaye ɗakin Iman ya nufa

Ya tura ƙofar a hankali

Abin da ya gani ya tsaya masa a zuciya

Iman na kwance a kan Prayer mat

Alƙur’ani yana buɗe a gabanta

Tasbaha kuma tana riƙe a hannunta tana ja

Da alama bacci ne ya ɗauke ta tana ibada

Suhail ya tsaya yana kallonta

Wani irin tausayinta ya mamaye zuciyarsa


A hankali ya ƙarasa

Ya ɗauki Alƙur’anin ya rufe 

Ya ɗora shi kan shelf 

ya zare tasbaha kenan iman na bude idanun ta 

koda ta ganshi a kanta tayi saurin tashi zaune

ganin ranar haske ranar da ya shigo ta window ta tashi da sauri

tayo Alwala ta gabatar da Sallar Asuba

duka Suhail na zaune ya tsura mata ido 

har ta kammalawa ta kallesa cikin girmamawa ta ce"yaya Suhail ina kwana"

"lafiya qlau"

ganin bata bata chanza masa ba ya shashi shiga cikin kunya  a hankali ya buɗe baƙi ya ce"iman i'm sorry da Abinda ya faru jiya"

murmushi yaƙe tayi ta ce"bakomai yaya Suhail ai tafi bukatar kulawa yanzu"

Wannan amsar tata ta sake karya zuciyar Suhail.

Ya rasa kalmar da zai ce

A dai-dai wannan lokacin…

Jennifer ta buga ƙofar ɗakin

“Sir…”

“Na’am"

“Hajiya tana ta amai sosai Ta ce ku zo"

Suhail ya lumshe idanunsa

Ya kalli Iman

ganin hankalin baya wajen ya ce "gani nan zuwa"

har ya fita ya juyo ya kalleta "basai kin daura breakfast ba zan fita na siyo mana"

kai kawai ta gyada masa


a haka aka shafe sati guda duk sanda Suhail ke dakin iman zeenah sai ta san abinda ta haɗa ya dawo wajen ta 

Suhail har gaji da bawa iman hakuri

ita kuma ganin haka yasa ta janye jikinta daga gare shi ta cire ranta a kanshi

idan ya shigo dakin ta kansa idan ma bai shigowa bata damuwa

tunda daman chan ta sawa ranta zuwan wannan ranar

yau ta kama Litinin kuma a yau ne iman ke shirin tafiya kaduna kamar yadda ra tsara 

tun safe ta tashi ta fara shirin ta cikin riga da siket na Atamfa ta saka  hijabin har ƙasa 

dakin Suhail ta nufa kamar yadda yace idan ta gama shirin ta faɗa masa dan shine zai kaita

Da sallama ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin.

“Yaya Suhail…”

Muryarta ta katse tunanin da yake yi.

Ya ɗago kai ya kalleta.

Na wasu daƙiƙu idanunsa suka kasa kaucewa kanta.

Tun bayan cikin Zeenah…

Wannan shi ne karo na farko da ya ga Iman ta shirya tsaf

Atamfa mai launin ruwan kasa da gold da ta saka ta ƙara fito da natsuwarta

Hijabinta ya rufe Gaba ɗaya jikin ta ta fito a Asalin ta na yar malan Abdallah

“Na gama ,ta faɗa cikin ladabi

"okay gani nan fitowa" 

dakin ta koma ta dauko jakar kayan ta da handbag dinta ta fito

tana zaune a falo,zeenah ta sauko hannun ta riƙe da cup ganin iman a zaune cikin shirinta fita tasan tabbas Suhail take jira 

da sauri ta chanza hanya zuwan dakin sa hannun ta riƙe da cikin ta 

tana yarfe hannu Suhail na saka kayan sa ta shiga 

duƙewa tayi a tsakiyar dakin "wayyo Allah Suhail cikina"

da sauri ya nufo bta hankalin a tashe ya ce"Zeenah miya same ki "

"cikina ke ciwo ka taimaka min"

ajiyar zuciya ya sauke 

ya kamo ta ya ce"muje ki shirya mu tafi asibiti"

tashi tayi da kyar ta koma dakim ta suhail ya fito gaba daya ya manta da iman dake zaman jiran sa

kusa da ita ya karasa ya zauna

ya jima yana tunanin abinda zai ce mata 

so yake ya faɗa mata ta fasa tafiyar yau ta bari sai gobe

ganin baida niyyar tashi ya sa ta cewa"yaya Suhail mu tafi ko"

kansa ya dan sosa ya ce"iman kiyi haƙuri ki bar tafiyar nan zuwa gobe,zan kai zeenah Asibiti kuma idan nace sai ka dawo kinga dare yayi"

murmushin yaƙe tayi ta mike ta ce"ka barshi kawai zan hau mota na tafi"

kan yayi magana har ta ja jakar ta ta fita 

kamar wanda aka ɗasa ya kasa binta yana kallon  ta fita 

ta jima tsaye bakin gate ta ma rasa ta inda zata Fara

shekarar biyu a garin Abuja amman bata taɓa bin motar kasuwa zuwa Kaduna ba 

hakan yasa inda zata dosa

tana jan trolley dinta har ta ƙara sa bakin titi 

taxi ta tara ta faɗa masa ya kaita inda zata shiga motar kaduna

bata damu da kudin da ya ambata mata ba ita dai burin bai wuce ta ganta a motar kaduna ba 

wata tasha mai nisa ya kaita ta bashi kudin sa 

ta shiga cikin cikin Sa'a ya rage saura mutun biyu mota ta cika hakan yasa bata yi wani jira ba 

mota ta cika suka kama hanya 

Suhail na zaune kamar wanda aka tsikara ya miƙe 

dakin zeenah ya shiga da mamaki ya ganta wance kan gado tana dan na wayar ta

ransa a matuƙar bace ya ce"zeenah kika ce baki da lafiya"

Zeenah ta ɗan yi dariya

"ai naji sauki"

Ya runtse idanunsa yana jin wani irin nadama na ratsa zuciyarsa

"innalillahi "kawai ya iya furta

da sauri ya bi bayan iman 

amman ina komai kama da ita bai gani ba 

zeenah kuwa ta fashe da dariyar mugunta 

A hankali ta ce a ranta

“Ko ma me zan yi… ba zan bari Iman ta sake samun matsayi a zuciyar ka ba You will remain mine forever"

Suhail ya fara ƙoƙarin kiran iman a waya

Wayarta ya kira 

tana zaune a mota taji karar wayar ta 

ta duba taga Suhail

ta lumshe Idanun ta

hawaye suka cika mata ido

ta ƙasa daga kiransa

kusan kira ukku yayi mata a jere bata dauka ba 

Ya ji gabansa ya faɗi.

A karon farko tun bayan aurensa

Ya ji tsoron rasa Iman

baida wani option daya wuce yabi bayan ta

a rude ya shiga motarsa yabi bayan ta amman duk tashar da ya sani ya je amman bai same ta ba 

yanke shawarar yayi ya bita kaduna