70
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
🅿️—70
Ba tare da ɓata lokaci ba, Suhail ya ɗauki hanyar Kaduna
Duk da gudun da yake yi, bai daina kiran layin Iman ba
Sai dai a wannan karon…
“The number you are calling is switched off…”
Wata irin faɗuwar gaba ya ji
Ya ƙara matse sitiyarin motar
“Ya Allah" kawai yake furtawa
Bai tsaya ko’ina ba har sai da ya isa Kaduna
Kai tsaye unguwar Malam Abdullahi ya nufa
Ya yi parking a gaban gidan
Unguwar ta yi tsit
Yara kaɗan ne ke wasa a bakin titi
A daidai wannan lokacin
Wata adaidaita sahu ta tsaya a gaban ƙofar gidan
Iman ta fito a hankali
Ta miƙa wa direban kuɗinsa
Ta sauko tana jan trolley ɗinta zuwa ƙofar gida
idanunta suka sauka kan baƙar motar da ke ajiye a bakin ƙofar gida
A hankali ta ɗaga kai
Suhail ne tsaye a gefen motar
Sai lokacin ya samu kwanciyar hankali ganin iman ta sauka
Ya nufo wajen ta
Bata yi tsammanin zai biyo ta har Kaduna ba
Ta ɗan runtse idanunta kafin ta buɗe su a kansa
“iman Miyasa kika taho a motar haya”
“Yaya Suhail ai na Saba hawa dan Haka shiga motar hanya ai ba saban Abu bane a wajena”
“Amman Miyasa Ina kiranki a waya ki ƙi picking"
"ban ga Dalili dagawa ba ,ya kamata ka tafi tun kafin wani abu ya sami matar ka"
"iman please ki saurare ni"
ganin tana ƙoƙarin shigewa ciki
Da sauri ya kama handle ɗin trolley ɗinta
Ita kuma ba tare da ta ce komai ba ta warce shi daga hannunsa ta ci gaba da tafiya.
dai-dai lokacin Hafsat na fitowa yayin da komai ya faru akan idanun ta
Suhail ya ja da baya
hafsat ta washe baki "yaya Suhail sannu da zuwa"
iman tabi ta bayan ta ta shige ciki
hafsat ta ƙaraso wajen sa bayan sun Gaisa ya tambaye ta ya school ta ce"Alhamdullilah yaya Suhail amman ya naga iman a haka ina fatan dai lafiya"
ajiyar zuciya ya sauke
ya dubi Hafsat ya ce"pray for me nayi mata lafi ne"
jinjina kai tayi ta ce"zan taya bata haƙuri, Matsalar kawai iman bata iya fushi bane but i will try my best in sha Allah"
godiya yayi mata ya saka hannu Aljihu ya dauko kudi masu yawa ya bata da farko kin amsa tayi dai daga baya kuma ta amsa
tayi masa godiya ya shiga motar sa yayi gaba
ko da iman ta shiga babu kowa a tsakar gidan dakin Ammi ta shiga
Ammi na zaune tare da baba lami yayar malan a falo
da sallama ta shiga ciki
baba lami ta fara tayar ta "a mutane habuja kune a tafe"
murmushi kawai tayi ta samu waje kan kujera ta zauna ta gaishe su daya bayan daya
Ammi na lura da iman dan baka ta saba zuwa ba ko da yaushe zata shigo da walwala akasin yau da kallo ɗaya zakayi kasan akwai Abin da ke damunta
suna zaune hafsat ta shigo
fuskar dauke da fara'a tana nuna wa su Ammi kudin da Suhail ya bata
Ammi ta kalli iman ta ce"au,daman tare kuke shine baki ce ya shigo ba"
yatsine fuska tayi ta ce"sauri fa yake Ammi"
Hafsat ta mata wani kallo
baba lami ta ce"Hafsatu nima ai sai ki bani nawa kason ko"
hafsat ta ce"chan baba lami ai sisi bazaki samu a kudin nan ba dama yanzu nake ta tunanin inda zan samo kudi na amso sauran dinkina sai gashi yanzu Allah ya kawo"
baba lami ta ce"au haka ma zaki ce kin kyauta amman jiya da kika rasa kudin adaidata a anan kika zo kina Allah Annabi na baki, wannan ai shine samu ka ƙi dangi"
Hafsat ta ce"kefa baba lami gori"
dubu guda ta zaro a cikin kudin ta miƙa mata ta ce"dama ai dari ukku na amsa ki rike dari bakwai din a riba"
baba lami ta ce"bakomai Allah yasa musu albarka"
duk Abinda suke iman da kallo kawai take binsu handbag din ta buɗe ta zaro dubu biyar ta mikawa baba lami ta ce"baba gashi na ƙara miki"
baki ta washe cike da jindadi ta ce"Nagode dije Allah yayi miki albarka ya kara miki zaman lafiya a gidan ki,ya kawo kazantar daki inje habuja inyi zaman ɗaki"
Ammi ta amsa da "Ammi" a ƙasar zuciyar ta
hafsat ta ce"oh waya ga baba lami a abuja Abincin yaya Suhail kam ya shiga ukku"
baba lami ta ce"dadin abin ma ba gidan ki nace zanje ba"
ganin dramar tasu bata karewa iman ta miƙe ta ce"Ammi zan shiga ciki kaina na ciwo"
kan Ammi tayi magana baba lami ta ce"Asha Allah ya baki lafiya"
hafsat murmushi kawai tayi "baba lami idon cin Naira"
pillon dake kan kujera ta dauko ta jefa mata da sauri ta kauce ta na dariya tabi bayan iman
baba lami ta ce"ai da kin tsaya shaƙiyar yarinya kawai"
iman na shiga daki ta kwanta kan gado ta rungume pillow
hafsat ce ta shigo ta zauna bakin gadon
ta jima tana kallon son isar da sakon Suhail take son yi amman ta rasa ta ina zata soma
"iman"
ɗago idanunta tayi ta kalleta
"dama yaya Suhail ne ya ce in baki hakuri aka abinda ya maki"
iman ta ce"haƙuri akan me fa"
nima dai ban sani ba"Amman koma minene kiyi haƙuri,yaya Suhail Suhail is so kind ba Kowane namiji bake ke laifi sannan ya gane kuskuren sa daga baya ba kiyi haƙuri ki yafe masa"
iman ta jima tana kallon Hafsat wanda bai wuce kalan mamaki ba "hafsat sai yanzu na gane dalilin daya sa ya baki kuɗi ya baki ne don kawai ki zo ki faɗamin kyawawan halayen sa ko"
murmushi hafsat tayi ta ce"ba haka ba ne,yaya Suhail ko ya bani kudi ko bai bani ba ya zama Dole na yafi kyakkyawan halayensa a ko ina yaya Suhail ya min abubuwa da yawa a Rayuwa ta bazan taɓa manta hallacin sa a gare ba"
"Tahirin rayuwa bazai taɓa manta wa dashi ba"
Iman ta miƙe zaune tana son sanin hallacin da Suhail yayi ma hafsat "Hafsat wani hallaci yayi maki da har kike tunanin bazaki manta dashi ba"
murmushi tayi ta ce"idan lokacin da zaki sani yayi zan fada maki waye Suhail dan ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba na fiki sanin sa"
jinjina kai iman tayi ta ce"bakomai idan tayi wari munji ai "
hafsat ta fita dan sama masu abinda zasu ci
bayan kwana Biyar
Duk Tsawon kwanakin nan iman bata Daga wayar Suhail sai dai idan zaiyi magana da ita ya kira ta lambar Hafsat duk nan din ma ba kullum take karba ba
ganin haka yasa Hafsat sai ta daidai ci suna tare da Ammi take kawo mata wayar
har Ammi ta gaji ta tambaye ta ko wayar ra samu Matsala ne
a iya yan kwanakin da iman tayi bata gidan jin gidan yaƙe tamkar kango
Gaba daya ya rasa natsuwar bai tabbatar san da yake wa iman ba ya kai wannan matakin kin sai yanzu da ya kwana biyar bai sata a idanun sa ba
ga azabtar da zuciyar sa da take ta hanyar kauracewa masa wanda yafi komai damun Zuciyar sa a halin zuwa
yau tun da safe iman da hafsat suka tashi,da wuri suka kammala aiki gidan dan zasu je saloon
Hafsat vta fara shirya bata fito falo Ammi da baba lami sai aunty Zaituna da tazo jiya sune zaune a falo suna tsara yadda Abincin bikin zai kasancewa da kuma duk abinda zasu buƙata kamar yadda Mubarak ya ce su rubuta duk abinda zasu amfani dashi yau zai taso daga kano zuwa Kaduna
Iman ta biyo bayan ta sanye take da doguwar riga ta material mai hula ta saka well-ironing hijabin har ƙasa ta dauko handbag din ta da wayar ta fito palorn
ta sami Ammi ta faɗa mata zasu je saloon
Ammi ta ce"kin fadawa mijin ki ne"
gaban taji ya fadi dan har ga Allah ta mantawa take da ita matar aure ce
kasa tayi da murya ta ce"Ammi ban faɗa masa ba kuma ma ai naga yasan biki nazo ai dole zan bita"
Ammi ta girgiza kaii ta ce"ban yadda ba idan kin fita ko nan da soro ne to da umarnin mijin ki"
ji tayi kamar ta fashe da kuka ko tama fasa fitar baƙi daya
Amman tana son zuwa bata da wani zaɓi da ya wuce ta kira sa din
kallon Hafsat dake gefe tayi itama ita take kallo
wani irin murmushi mugun ta tayi yau Ammi ta biyata ta birgeta
zata ga ta yadda iman zata fara kiran Suhail
tsaye tayi tana kallo
share
like
comment