BARRISTER SUHAIL

71

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----71

ta jima tana kallon wayar kafin ta fara ƙoƙarin dubo lambar da tayi saving da yaya Suhail

bugo Daya cikin na biyu ya ɗaga

yana zaune a office yana duba wasu files kiran ya shigo

"yaya Suhail ina wuni"

"lafiya qlau iman"

"dama zan faɗa mata zamuje salon"

"okay,keda wa"

"Hafsat"kawai ta bashi amsa a taikace"

bata jira amsar saba ta kashe wayar 

Aunty Zaituna ta kalli hafsat ta ce"wai anya lafiyar ki kuwa sai dariya kike ke kadai ko dai akwai abinda kuke boƴewe"

dariya tayi ta ce"bakomai Aunty kawai dai Ammi ce tayi Abinda ya birgeni yanzu,kinga da haka imann zata fita ba tare da sanin mijin taba"

iman ta dago ta kalleta tare da zabgata mata harara 

tashi suka yi zasu tafi baba lami ta musu "Allah ya kiyaye"

har suka fita fita iman bata kula hafsat ba Napep suka tara Hafsat ce ta fada masa inda zai kasu

Napep ɗin ya tsaya a gaban wani babban salon mai kyau da tsari

koda zasu shiga iman ta ce"nifa ba wani lalle da zanyi kaina kawai zan wanke"

hafsat taja hannun ta ta ce"haba iman bikin yaya Mubarak fa ake dan Allah kar bani kunya ki barni ni zan zabar mana duk abinda zasu yi mana"

suka shiga ciki 

salon din cike yake da yan mata 

wasu ana gyara masu gashi yayi da wasu kuma ake masu ƙunshi

daya daga cikin ma'aikatan ta tarbe su tare da kawo masu littaffin shagon su zabi abinda suke ayi masu
Hafsat ce ta zabar masu 

dan danan aka fara yi masu Abinda suka zaba

Hafsat anayi mata calaba ta attachment iman kuwa normal kitso akayi mata 

dan Hafsat tasan ko ta zaba mata mai attachment ma bazata bari a yi mata ba

ana tsaka dayi mata kitson kiran Suhail ya shigo sai da kalli iman kafin ta daga

bayan sun gaisa ya tambaye ina iman ta ce"gatanan nan ana mata kitso"

Suhail ya ce"take care of her me"

murmushi tayi ta ce"in sha Allah"

tana katsewa wayar iman ta kalleta ta ce"dawa kike waya"

""wani ne"

bata sake tambayar taba 

sako ya shigo wayar Hafsat tana dubuwa taga kudi ne Suhail ya turo mata tare da text massage dake rubuce da "gashin ku biya kudin services idan akwai abinda kuke buƙata let me know"


ta mayar masa da sakon da "thank You yaya Suhail Allah ya ƙara budi"

ana gama masu suka nufi wajen kunshi ja baƙi gaba daya akayi musu 

basu bar salon din nan ba sai karfe biyar da kusan rabi 

duk yawan kuɗin da aka chaje su Hafsat ce ta biya 

suna fita daga salon din hafsat ta tambayi iman ina ta ta samu kudi masu yawa haka 

murmushi ta yi ta ce"wani bawan Allah ne ya Turo min"

jikinta kawai ya bata Suhail ne 

hafsat ta kalli iman ta ce"ki rakani shop din chan zan sayi veils please"

Iman ta girgiza kai

“Ni fa na gama abin da ya kawo ni"

“Don Allah Iman"

Ba tare da ta jira amsa ba ta ja hannunta suka shiga

Hafsat ta fara zaɓar kayan kwalliya da takalma sai mayafai 

Ita kuwa Iman tana tsaye gefe tana kallon shagon

wayar Hafsat ta sake ƙara Suhail ne ya kira ya tambaye ko sun gama salon din ta ce"eh suna wani shago kusa da saloon din"

Suhail ya ce"ta tura masa address din zai turo wanda zai maidasu gida"

ba ɓata lokaci tura masa bai fi minti biyar ba sabuwar lamba ta kirata 

bayan ta daga ya sheda mata cewa suhail ne ya turo sa yana kofar shagon 

basu ɓata lokacin ba suka fito 

yana ganin fitowar daga shagon ya nufi wajen wajen su 

"hajiya nine wanda sir Suhail ya turo"

iman ta kalli hafsat ta ce"ke kika faɗa masa munan ko,to ni bazan shiga ba zan tari Napep"

hafsat ta ce"haba iman miye haka,dan yaya Suhail ya damu da lafiyar ki laifi ne"

"hafsat nifa ma fada maki kawai bazan shiga ba"

ganin da gaske take ta ce"Iman nifa wannan abin ya fara isa ta kawai zan faɗa wa Ammi Abinda ke faruwa tsakanin ki da yaya Suhail"

direban dai yayi tsaye yana jiran umarni 

Iman ta kalli Hafsat ta ce"wannan shine ƙaron farko kuma na karshe da zai sake turo driver na bisa"


Hafsat ta ce"naji shiga mu tafi"

hafsat ta shiga gaba drivern ya buɗe wa iman seat din baya ya ta shiga

har suka ƙarasa gida babu wanda ya kara magana 

har ya kai su kofar gida ya sauke 

da kanshi ya buɗe masu kofa suka fito 

direban ya miƙawa wa iman wata karamar leda

ta kalli ledar ta ce"ta minene”

"sir Suhail ne ya ce na baki"

ta karɓa suka shiga ciki bayan hafsat tayi masa godiya

gidan ya fara cika da yan biki dangi na nesa da kusa sun fara cika gidan 

sakamakon gobe ake fara wunin biki 

dakin iman suka nufa nan kadai babu mutane cikin sa

suna shiga iman ta buɗe ledar kwallin chocolate ne da karamin envelope 

Ta buɗe envelope ɗin

Takarda ce guda ɗaya

Rubutun Suhail ne

“Ban san ta wace hanya zan nuna miki nadamata ba

Na san kalmar ‘sorry’ ba ta isa ta goge abin da na yi ba

Amma zan ci gaba da neman yafiyarki har ranar da zuciyarki za ta sake yarda da ni

— Suhail

Iman ta daɗe tana kallon takardar

sai dai wannan karin bata ji komai ba a zuciyatar kamar da da in yayi mata laifi take saurin yafe masa 

yanzu zuciyar ta ta ƙeƙashe a kansa

a hankali ta nade takardar

Hafsat kuwa tana tsaye daga gefe tana kallonta 

a zuciyarta addu'a take Allah ya daidaita tsakanin su amman tabbas suhail na san iman


comment dinku ne ya sa ni yi maku posting din nan idan kuna comment zaku rinƙa samun posting sosai 

sai dai idan baku samu na gobe ba kar kuyi ƙorafi🤣shine na turo muku

like.
share 
comment