72
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----72
ajiye takardar tayi
Hafsat ta ce"bazaki karanta sakon ba"
iman ta Girgiza kai
"na karanta abinda nake bukatar karantawa"
ta linke takardar ta maida cikin envelope chocolate din ma ta maida cikin ledar
ta saka cikin drower
bata ƙara cewa komai ba ta fita daga dakin
a kofar dakin malan ta hangi baba lami tana gyara kayan miya ta nufi wajen ta
kan tabarmar ta zauna gefen baba lami
"Dije an dawo kenan"
murmushi tayi ta ce"na dawo baba dije ai da na shigo ban gan ki ba"
"ƙila na shiga ɗakin audu ne"
baba lami ta kalli lallen dake hannun ta ta ce"kinga ko yadda kunshin nan yayi kyau anya sirrikin nan nawa ba kudin sadaki zai sake biya ba kuwa"
murmushi ima tayi wanda iyakar sa kan fuskar ta ta ce"baba lami kenan idan kina so kema sai in kaiki a miki irin shi"
baƙi baba lami ta buɗe ta ce"wayyo waya ga tsohuwa da budurwa zuciya ai wannan sai ku ƴan mata ni nayi wannan zane zanen ai har mutane sun kirani da tsohuwar banza"
"ga lalle na chan na jika an jima Hafsatu zata kun samin lalle idan ta ga dama kinsan ita din ce ba'a abin arziki da ita"
dariya iman tayi ta ce"baba lami ai kun fi kusa da ita"
"au haka ma zaki ce"
"Eh,mana ai tare na ganku"
wuƙa ta dauko ta taya ta da gyaran Albasa a haka Hafsat ta fito ta same su
Suhail ne zaune a falon sa yana kallon hotunan iman
wanda Hafsat ce ta turo masa su lokacin da ake yi mata kitso da lalle ba tare da ma tasan ta dauka ba
fuskar ta babu walwala amman duk da hakan bai hana nutsuwar ta fito wa ba
ya jima yana kallon hotunan zeenah ce ta shigo hannun ta rike da cup din juice tana sha
kallon sa tayi ta ce"Suhail jennifer ta ce baka ci abinci ba"
"bana jin yunwa" kawai ya fada a takaice
ta rasa gane kansa tun ranar da iman ta sa ƙafa ta bar gidan tamkar ta tafi da walwalal sa ko office baya zuwa sosai
kullum yana gida kuma ko wani lokaci zaka same hannunsa riƙe da waya
sun jima a haka babu wanda ya ce wani abu
har daga ƙarshe Suhail ya tashi ya bar zeenah a nan
da kallo ta bisa har ya shige dakin sa, zuciyarta cike take fal da tsanar iman wanda a ganin ta ta rushe mata duk wani gini da kuma yadda ta tsaro Rayuwar ta Suhail tun kafin auren su
amman shigowar ta cikin rayuwar su ta rusa komai
ta lura da ba ƙaramin mahimmanci take dashi a cikin rayuwar sa ba wanda har kasan yasa baya ganin kowa a Rayuwar sa face ita
duk duniya bata da wani maƙiyi da ya wuce iman kuma ta sha alwashi matukar tana raye a duniya duk yadda zatayi ,zatayi dan ganin zaman iman da Suhail ya zo karshe
daga nan kuma sai tayi kokarin cusa kanta a zuciyar Suhail
ko wannan kulawar da yake nuna mata a yanzu tasan baya wuce albarkacin cikin shi dake jikin ta
kuma da wannan zata samu damar mallakar Zuciyar ta har abada
duk da a baya ba wai tana son haihuwar bane dan ba haka ta tsarin Rayuwar ta ba ,tun kafin auren su da Suhail bata auresa dan ta haihuwa ba a cewar bata so ta tsufa da wuri
kuma har ga Allah bazata iya wahalar reno ɗa ba amman tunda wannan ne Burin Suhail yasa ta haƙura da nata burin
ta shirya haifa masa yaran
tunda iman bata da lafiyar da zata cika masa wannan burin
haka ta karaci zaman tq anan ta tashi ta tafi
washegari....
tun karfe tara na safe gidan malan Abdallah ya cika da baƙi
yau Alhamis yau ne ake yinin biki
iman da hafsat kuwa tun da safe suke ta kai kawo
Ammi sai sa masu albarka take yadda suke kula da komai Tamkar ita ce tsaye a wajen
aunty Zaituna da sauren dangin ke kula da abincin baki
a dai-dai lokacin motar Mubarak tayi parking a kofar gidan
ya shigo ciki tuni gidan ya ƙaure da buɗa ganin ango sanye yake da farar shadda manyan dinki sunyi matuƙar yi masa kyau
yaya Mubarak yayi ƙiba sossai yayi haske tamkar ba shi ba
kudi sun zauna dan ba ƙaramin aiki ya samu a kano ba wanda jajircewar sa da Amanar dake nuna masu ya kaishi wannan matakin
hakan yasa Ubangidan sabya haɗa auren shi da aure da ƴar sa
hatta motar da yake hawa shine ya bashi da kuma gidan da zasu zauna a kano saboda baya son yayi nisa da aikin sa
yaya Mubarak ya gaishe da kowa cikin ladabi
matan nan sai fatan Alkairi suke masa tare da fatan zaman lafiya mai dorewa
Ammi ce ta fito sanye take da atamfa holland anyi mata ɗinkin riga da zani
Mubarak ya Rungume ta cikin so da kaunar mahaifiyar tasa
ji tayi Zuciyar ta kare idanunta ya kawo ƙwalla ko wata kuwa tana Burin taga ta aurad da yaran ta
Alhamdullilah ta godewa Allah daya kawo mata wannan Ranar ta aurad da Dukkanin yaran ta biyu da Allah ya bata
da sauri ta saka tafin hannun ta ta share hawayen
iman ma ta ƙara so wajen sa Cike da fara'a "yaya Mubarak sannu da zuwa"
kallo ɗaya yayi mata yaga ta rame sosai ba kamar ganin da yayi mata karshe ba
ya lura da murmushi da take bai kar har zuciya ba
ta dan haɗe gira
a zuciyar sa yake tunanin lalle akwai abinda ke damun ta
ya yanke shawarar idan ya samu dama zai zauna da ita yaji abinda ke damunta
tun ranar da Suhail ya ƙara aure har yanzu bai samu kwanciyar hankali ba
kullum gani yake tamkar matsa ma ƙanwar sa ake a gidan
yau ta kama jumma'ah a yau ne duba bin mutane ke sheda daurin auren Mubarak Abdullahi tare da Amaryar Raihana Aliyu wanda aka daura a Babba masallacin Isiyaku Rabiu dake garin kano bayan sallar juma'a
bikin ya samu hallartar manyan baƙi daga garuruwa daban daban ciki hadda suhail da mahaifin sa wato Alhaji munnir Mahmud
mutane da yawa ma daga Kaduna sun samu zuwa
tarba ta musamman su malan Abdullah bda mutanen suka samu a wajen Alhaji Aliyu mahaifi Amarya
babu wanda bai ci ya sha a wajen nan ba tabbas babu abinda Malan Abdallah zai ce da sirrikin sai san Barka ba shakka Mubarak ya auro yar babban gida
sai bayan sallar la'asar mutane suka soma juyawa kaduna ciki hadda shi kansa Mubarak
dan ba wani event da zasuyi kuma sai gobe Amarya zata tare hakan yasa shima ya koma cikin danginsa ya gudanar da nasa bikin
chan Kaduna ma sai hidima ake gida ya dinke tab da baƙi
Hafsat bda iman sukayi anko cikin wani ash din lace mai ratsin milk komai a ranar anko sukayi hatta mayafan su ma zaka rantse ƴan biyu ne
Bayan an dawo daga daurin aure Suhail da mahaifin suka biyo malan a dakin su ya sauke su
ya shiga cikin gidan ya sami Ammi ta kira Iman ta kawo abun sha dakin sa Suhail ne yazo da mahaifin sa
suna zaune a ɗaki tare da hafsat ammi ta kira ta ce"tazo ta kaiwa mijin ta da surukin ta abin sha suna dakin malan"
wata irin faduwar gaba taji ta marairace ta ce"Ammi dan Allah kiba hafsat ta kai masu"
baki Ammi ta kama ta ce"ke bazaki je ba kenan to bari in fadawa malan cewa kin ce bazaki je ba"
ganin Ammi da gaske take ta sha gabanta ta ce"Ammi kiyi haƙuri, kawo na kai musu"
hararar Ammi tayi iman tabkoma ta dauko doguwar hijabin ta har ƙasa ammi ta bata plate din ta nufi Dakin malan
to ga Suhail ga Alhaji munnir ga kuma hajiya iman
mi kuke tunanin zai faru🤗
ina jin daɗin comment dinku Shiyasa nake rikitaku da update akai akai a cigaba da gashi
i love You guys
like
share
comment