BARRISTER SUHAIL

73

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----73

a hankali ta isa Kofar dakin 

ta jima a tsaye tana saita numfashi ta 

Sannan tayi sallama ta shiga dakin 

Suhail na zaune a kan carpet 

yayin da malam da Alhaji munnir ke zaune kan kujeru

babu Abinda ya fado mata a rai sai Ranar farko da Suhail yazo gidan su tare da mahaifin sa neman auren ta 

scene din ya rinƙa dawo mata sabo a ƙwaƙwalwar ta

tray din ta ajiye a gaban abba ta gaishe shi cike da ladabi 

ya amsa cike da sakin fuskar 

babu Abinda ke birge shi da iman sama da natsuwar sa da kuma hankalin ta wanda tun farkon ganin da yayi su suka dauki hankalinsa har yayi wa dan sa Suhail sha'awar ya aure ta 

dan duk inda ake neman mace ta gari iman ta kai 

Ko kallon Suhail ba ta yi ba.
Shi kuwa tun shigowarta idanunsa suna kanta.
Ash lace ɗin da ta saka ya fito da ƙyawunta fiye da yadda yake tunani
Sai dai babu walwala a fuskarta

Wani irin kasala ta ratsa zuciyarsa Ita ce matar da yake gani kullum, amma yau kallon ta yake tamkar sabon abu a gaban sa


ganin bata da niyyar gaishe da Suhail Malan ya ce"baki ga mijin ki bane"

ƙasa tayi da kai tana wasa da kasar hijabin ta ba tare da ta dago ta kalle sa ba ta ce"ina wuni"

"lafiya qlau" kawai ya amsa

Malan ya dube ta ya ce"bazaki miƙa masa ruwan ba" cikin zafi yadan yi maganar dan haushi ta bashi 

Abba yayi murmushi ya ce"haba malan ka bita a hankali mana ai zata bashi"

jikin ta har rawa yake ta zuba ruwa a cup ta miƙa masa hannunta da nashi suka haɗu waje guda da sauri ta janye hannun ta jin kamae an haɗa mata shocking

ta jima a zaune a wajen daga bisani ta tashi ta ce"zata je ta cigaba da aiki"

Malam ma ya fita ya basu waje dan suci Abinda aka kawo masu

Alhaji munnir ya dubi Suhail ya ce"Suhail ko akwai Matsala tsakanin ka da matar ka ne"

kai ya dan sosa ya ce"Abba nadanyi mata laifi ke kuma na bata haƙuri amman taƙi haƙura"

Abba ya jinjina ka tun shigowar da irin kallon da take ma Suhail yasan akwai matsala 


Abba ya ce"kayi kokarin gyara kuskure ka Suhail domin idan ka bari Khadija ta sibice maka ba baki nake naka ba amman zaiyi wuya ka samu mace mai hankali da natsuwa kuma ta fito daga gidan tarbiyya irin ta ba"

ƙasa yayi da murya ya ce"in sha Allah abba zanyi ƙoƙarin gyarawa"

"Allah bada iko,ya kamata mu tafi ko"

Suhail ya miƙe zasu fita kenan malan na shigo 

cikin mamaki yake kallan su"Alhaji har zaki wuce"

"Eh,malan Allah ya sanya Albarka ya bada zaman lafiya"

tare ya rako su har Kofar gida Suhail ya kira Hafsat tazo su gaisa kan ya wuce

bata ɓata lokaci ta fito cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji munnir Suhail ya buɗe masa mota ya shiga

ya dawo suka gaisa da Hafsat ya tambaye ya taro ta ce"Alhamdullilah"

tambayar ta yayi akan yaushe zasu je Kanon 

dan tunani tayi kafin ta ce"Malan ne ya hana shiyasa ma ka ji ban kiraki kaba ya ce baba lami kadai da Aunty zasu je"

kai ya jinjina dan hakan yayi masa dad'i daman baya so matar tana yawo daga wannan garin zuwa wannan 

sallama yayi mata ta shige ciki ya koma motar yaja sukayi gaba

har suka karasa gida abba nayi ma Suhail fada da kuma nasiha wanda duk bai wuce akan iman ba

Bayan kwana biyu 

yan biki kowa ya watse ya rage daga baba lami sai Aunty Zaituna dake shirin tafiya itama a yau dan ta baro mijin ta da bashi da lafiya 

Iman da hafsat na zaune tsakar gida suna cin Abinci 

Malan ya shigo ya fadawa iman ta same shi a daki bayan sallar magariba 

ta amsa da "to" 


haka ko akayi tana gama Sallar magariba ta nufi dakin malan yana zaune akan kujera ta shiga

waje ta samu gefen sa ta zauna ta gaishe ya amsa 

gyaran murya yayi ya ce"Dalilin da yasa na kiraki daman naji ki shiru baki ce ga ranar da zaki tafi ba  yaushe zaki koma dakin ki tunda an gama biki"

wani irin mummunan faduwar taji

ta dago ido ta kalli malan shima idon sa na kanta 

cikin raunin murya ta ce"Malan kayi hakuri amman bazan koma ba"

charbi da yake ja ya ajiye a gefe ya ce"kamar ya bazaki koma ba Suhail din sakin ki yayi"

kai ta girgiza masa 

ya ce"miye dalilin ki na cewa bazaki koma ba"

kuka ta tashe masa dashi Tamkar ranta zai fita Malan yayi mata tambayar duniya amman taƙi magana

ana haka Ammi ta shigo ganin iman na kuka hankali ya tashi ta soma tambayar Abinda ke faruwa

malan ya ce"wai cewa tayi bazata koma gidan ta ba"

Ammi ta ƙarasa kusa da ita ta janye hannun ta daga kan fuskar ta cikin sigar lallashi ta ce"iman ki min bayani miyasa baki zo ki koma"

cikin fushi malan ya ce"ta miki bayani,ai bata da wata hujja kuma matukar ba Suhail bane ya ce kar ta koma ba kuka ko zata mutu sai na kira shi ya zo ya dauke ta"

"shashar yarinya kawai ina miki kallon mai hankali ashe baki da shi"

kukan ta ya Karu fiye da ɗa karin Farko da malan ya daga Muryar sa a kan ta 

Ammi ta ce"haba malan ai kamata yayi mu lallaɓata ta gaya mana Dalilin ba wai a hau ta da faɗa ba da wanne zata ji"


Malan ya ce"ai daman duk wani Abu da yarinyar nan take a gidan nan ke ke goya mata baya banda haka kawai mijin ta bai sake taba ta ce wai bazata koma ba mi hakan yake nufi"


Ammi ta sunkuyar da kanta bata ƙara cewa komai ba ya dube su ya ce"ku tashi ku bani waje kuma ki shirya gobe goben nan zan kirashi yazo ku tafi"

da taimakon Ammi iman ta miƙe tsaye wani irin juwa take ji hatta idanunta basu gani sosai 

dakin ta, ta kaita ta kwantar da Ita kan gado ta kifa kanta cikin pillow tana kuka 

Ta yi ƙoƙarin hana kukanta fitowa da ƙarfi, amma zuciyarta ta gaza ɗaukar nauyin abin da take ɓoyewa"

baba lami dake zaune a falo ta tambayi Ammi Abinda ke faruwa bata boye mata komai ba na Abinda ya faru tsakanin iman da malan

baba lami ta miƙe ta ce"bari naje na samu audun ai kamata yayi ya zaunar da ita ya tambaye ta Dalilin ta na ƙi komawa bawai ya hau ta da faɗa ba"

Ammi ta ce"baba lami dan Allah har kije dan cewa zaiyi nice na Turo ki"

cike da gamsuwa da abinda Ammi ta ce ta koma ta zauna

daren ranar Iman bata kula kowa ba duk tambayar da Ammi keyi mata akan ta fada mata idan akwai Abinda ke faruwa tsakanin tabda suhail amman ta ƙi 

Hafsat kuwa tayi jigum ranta duk babu dad'i tasan dan Suhail da iman sun samu saɓani amman bazata ce ga Abinda ya ya haɗa su ba

ganin haka yasa ammi ta kira Mubarak a waya ta faɗa masa abinda ke faruwa ya kira iman din wataƙil shi ta buɗe baki tayi masa magana

ya ce"gobe in sha Allah zai shigo Kadunar da sassafe"


Ammi ta ce"Allah ya kaimu lafiya Mubarak ka gaishe da raihan"

"zataji in sha Allah"

Bayan ya ajiye wayar ya dubi Raihana dake gefen sa 

ya ce"gobe zan tafi Kaduna"

Raihana ta kallesa ta ce"honey lafiya dai "

ajiyar zuciya ya sauke ya ce"iman ce da mijinta ta kafe akan bazata koma ba kuma taƙi fadawa kowa dalili"

Raihana ta sauke ajiyar zuciya ta ce"honey zan bika,kaga ya kamata naje na gaida su Ammi"

kaii ya girgiza masa ya ce"ba yanzu ba tukun"

haƙuri tayi ba tare da tayi masa gardama ba

Raihana bata taɓa haduwa da dangin Mubarak ba sainda a waya banda malan da shima sai ranar daurin aure ta san shi

iman kuwa tuni take gano kamanin kullum Mubarak bashi da wani aiki sai na bata Labarin 

iman ta hardace komai nata hakan yasa take gano kamanin duk da basu taɓa haduwa ba 





anya ba da addu'a kuke bina ba irin wannan update da nake turowa ko dai kun samin hannun🥱🤒

like 
share and 
comment