BARRISTER SUHAIL

75

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----75 

Mubarak na tafiya a kan titi, amma hankalinsa gaba ɗaya yana kan Iman

Kalaman ƙanwarsa suna ta dawo masa cikin kunne

”…idan kuma so kuke a kawo gawata ku matsamin sai na koma gidan sa…”

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi
Ya san ya yi iya ƙoƙarinsa, amma ya kasa canja ra’ayin Malam

A lokaci guda kuma

Malam ya lalubo wayarsa
Lambar Suhail ya nemo ya danna kira

Ringing biyu kacal aka ɗauka

“Assalamu alaikum, Malam"

Cikin girmamawa Suhail ya gaishe shi

Malam bai ɓata lokaci ba ya ce,

“Suhail, duk abin da kake yi ka bar shi. Ka zo ka ɗauki matarka. Ba zan yarda ta ci gaba da zama a gidan ubanta ba"

Wani irin bugun zuciya Suhail ya ji

Da ƙyar ya iya cewa

“In shaa Allah, Malam. Gani nan zuwa.”

Bayan ya ajiye wayar, ya daɗe zaune yana kallonta wayar"

Bai san ko farin ciki yake ji ba ko kuma tsoro

ya jima yana kallon rufin dakin 

Bai taɓa tsammanin Iman za ta dawo rayuwarsa da wuri haka ba

Amma tambaya ɗaya ce ta mamaye zuciyarsa

Ta yaya za su zauna ƙarƙashin rufi ɗaya alhali ta daina ko kulasa bata yi masa maga

Ko yanzu ma abin da ya sa yake ƙoƙarin nisanta kansa da ita shi ne tsoron kada ta ƙara jin haushi idan ya matsa mata

a hankali ya soma tattare takardun dake gaban sa ya maidasu gefe guda ya shiga bathroom a gaggauce ya fito ya shirya cikin wani milk yard an yi mishi dinkin Captain ya feshe jikin sa da perfumes masu tsada 

ya dauki key din motar sa ya fito

zeenah na zaune a falo tana sha fruit

gaban ta yazo ya ce mata zan tafi kaduna

ajiye kankanar dake hannun tayi "Kaduna kuma Suhail,jiya fa ka dawo babe mi kuma zaka je kayi"

"zan dawo da iman"

wani irin faduwar gaba taji ta ƙasa daurewa ta ce"babe ai na dauka bazata dawo ba"

wani Irin kallo yayi mata "“A wani dalili ne ba za ta dawo ba? Ko na taɓa gaya miki cewa na sake ta?”

Bai ƙara cewa komai ya juya ya fita

har ya kai bakin ƙofa zeenah ta ce"babe ka dawo da wuri please kaga banda lafiya"

bai kula taba ya buɗe kofar ya fita

yana fita zeenah ta zube akan kujera 

wani Irin tashin hankali ya mamaye zuciyar ta 

dawowar iman ba karamin abu bane zata rasa duk wata kulawa da take samu a wajen suhail

hannu biyu ta sa ta dafe kanta 

"a'a ba zan bari ba"

a hankali ta furta cikin muryar da babu mai jin ta 

gudu sosai Suhail yake a cikin mota hakan yasa shi isa kaduna cikin awa ɗaya da rabi

ya jima zaune cikin mota a Kofar gidan malan

Ya jingina da seat yana kallon kofar gidan

Karo na farko cikin kwanaki masu yawa ya ji tsoro

Ba tsoron ganin Iman ba

Sai dai tsoron yadda za ta karɓe shi

Ya tuna ranar da ta bar gidan ba tare dako waiwaya ba

Ya runtse idanunsa ya ambaton Allah

“Ya Allah"

Ya furta a hankali

“Ka gyara min abin da na lalata"

Daga bisani ya fita daga cikin motar zuwa kofar gidan

A gidan Malam kuwa…

Tun bayan fitar Mubarak, Iman ba ta sake fitowa daga ɗakinta ba.

Ammi ta kai mata abin karin kumallo

Amma ko kallon Abincin  batayi ba bare ta taɓa 

Malan na zaune a dakin sa yaji sallamar Suhail yayi masa iso daya shigo

bayan sun Gaisa malan ya ƙara yi masa nasiha tare da nuna masa cewa haihuwa ta Allah ce da yake bawa bayin sa wanda yaso 

Suhail bai kawo komai a ransa duk zaton sa malan nasihar sa ya saba masa ce yau ma yayi 

anan malan ya barsa ya shiga cikin gida

hafsat na Zaune kan tabarma tare da baba lami suna kallo a waya

Malan ya ce"ta faɗa iman ta fito su tafi mijin ta yazo"

ita kanta sai  da zuciyar ta karye da kyar ta miƙe a sanyaye ta shiga daƙin

bazata iya tunkarar Iman da wannan maganar ba hakan ya sa tabi ta kan Ammi 

tare suka shiga dakin Iman na zaune bakin gado fitowar daga wanka kenan tana shafa mai

Ammi ta shigo ta ce tayi sauri ta shirya mijinta yazo yana jiran ta 

da kyar ta ida shafa mai ta saka atamfa dinkin doguwar riga da hijabin ta

da taimakon hafsat ta haɗa mata kayan a trolley suka fito 

babu wanda ta tanka daga Ammi har baba lami ta fita waje 

daidai lokacin malan na raƙo Suhail 

Suhail ya amshi trolley din daga hannun Hafsat ya saka a boot ya buɗe mata front ta shiga ta zauna na tare da ta kalle shi ba 

duk a kan idon malan 

Suhail ya dawo yayi masa sallama suka kama hanyar 

tunda ta shiga ta sunkuyar da kanta banda kuka babu Abinda take

Hafsat ma ganin Iman ta tafi tana kuka ta ƙasa daure Zuciyar itama ta fasa kukan ta shiga koma ciki 

baba lami ta buɗe baki ta ce"oh ni lami jikar mutun hudu yau naga Abinda yafi karfina"

ita wancan ta fita rai a hade ko sallama bata min ba ko dan kar ta bani kudin ban kwana ne oho

"ke kuma kin shigo wii wii kinawa mutane kuka"

"idan ba kisan ku rabu ki fiddo miji mana kema a aurar dake Shekara Ashirin da ɗaya ga kinan idan a kauye ne ai Yanzu ki ajiye yara ukku ko hudu"

"Amman kin biye wa boko kega alhuda-huda sarkin karatu"

Hafsat ta hadiƴe kukan da take ta kalli baba lami ta murguda mata baki ta ce"Eh,anyi din"

ta tashi ta amshe wayar ta ta koma daki

baba lami ta ce"idan bakiyi bama ai baki cika Sunan ki ba,haka hafsatun kauyen mu take duk tabi ta ishi yan garin da masifar tsiya da baƙin hali"


duk maganar da take Hafsat bata kula taba ganin haka 

baba lami ta ce"Hafsatu kiyi wa Allah ki dawo ki ƙara sa samin kallon nan"

hafsat daga cikin dakin ta ce"bazan kun na ba kije wanda ba masiffafe ba ya kunna maki"

baba lami ta ce"kar Allah yasa ki kunna bari na tashi na gaida Ubangiji na"

Hafsat ta ce"da dai ya fi maki dan kabari kusa kike" 

"to yar baƙin ciki in sha Allah ba Yanzu zan mutu ba sai dai Zaituna ce kabarin ta yake kusa"


duk da halin da Ammi take ciki bai hanata yin dariya ba tsamar Hafsat da baba lami bata kare wa dui fadan da suke hakan bazai hana anjima ka gansu zaune waje guda ba 


tunda Suhail ya bar Kofar gidan malan 

daga Suhail har iman babu wanda ya kula wani 

Suhail ya kan dan saci kallon ta 

har Yanzu bata daina zubar da hawaye ba wanda ke nuna ciwon zuciyar ta 

Ajiyar zuciya Suhail ya sauke

ya buɗe baki ya kira sunan ta 

"Iman"

bata ko Amsa ba bare yayi tunanin zata juyo ta kallesa 

shiru ya ratsa

sai karar motocin dake wucewa

koda ya fahimci bashi da lokacin 

ya cigaba da tuƙi 

Bayan tafiyar kusa awa guda

Ya tsaya a wani babban restaurant da ke gefen hanya

ya juyo ya kalleta tare da tambayar ta Abinda zata ci 

"bana jin yunwa"

ta faɗa a takaice

sanin ba lalle ta faɗa ba ya fita ya bai jima ba ya dawo da ledojin Abinci da lemu

ya saka a seat din baya yaja sukayi Gaba

like 
share 
and comment 

comment dinku na kara min kwarin gwiwa Nagode da kauna