76
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----76
Suhail bai sake matsa mata ba
Ya san idan ya ƙara magana a wannan lokacin, wataƙila zai ƙara dagula mata zuciya ne kawai
Motar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa
Sai ƙarar tayoyin motar da kuma sautin AC ne kaɗai suke tashi
Lokaci zuwa lokaci Suhail kan sace kallonta
Har yanzu kanta na sunkuye
Hawayen da take sharewa a ɓoye ba su daina zuba ba
Bayan kusan awa guda suka shiga cikin garin Abuja
Kai tsaye gida ya nufa
motar na tsaya a harabar gidan, Iman ba ta jira ya buɗe mata ƙofa ba
Da kanta ta buɗe
Ta fito
Ta nufi cikin gidan ba tare da ta waiwayi inda yake ba
Suhail ya fito daga motar ya zaro trolley ɗinta daga boot
A hankali ya bi bayanta
ko da ta shiga falon babu kowa dakin yayi shiru
ta nufi nata dakin da shigar ta ,ta maido kofar ta saka key
koda ya karaso kofar dakin da mamaki yaji kofar a bude
hannunsa ya dora kan handle
"Iman"
jin shiru ya sake kira amman
taƙi ta amsa
"Iman na san kina fushi,na san na miki laifi amman hukuncin ya isa haka bana so ki fara hukunta kanki sabo dani"
koda taji Muryar sa wasu sabbin hawayen suka soma zuba
ganin bazata buɗe ba ya juyo ya ajiye trolley din ya tafi
ya soma jin haushin Abinda take masa
saida ta tabbatar da ya tafi ta buɗe kofar
ta dauko trolley din ta
ko kallon ledar Abincin batayi ta koma gado ta kwanta
bayan kwana biyu
tunda Ranar idanun Suhail dana iman basu kara haduwa ba
ya zama tsakanin sa da ita sai wasan ɓuya
bata fitowa daga daki sai ta tabbatar daya tafi wajen aiki
haka da zarar ya dawo take shiga daki ta kulle kanta
sossai abu ke damun Suhail shi kansa cikin kwanakin har wata rama yayi
yau ma kamar kullum Suhail ya tafi office iman ta fito daga dakin ta nufi Kitchen dan sama wa kanta abinda zata ci
tea ta haɗa ta soya kwai guda biyu ta doro akan plate ta fito
tun daga nesa ta hangi zeenah zaune kan kujera tana bare ledar cingum da cin sa har ya zame mata dabi'a
tun daga nesa take kare ma iman kallo wanda ba komai a cikinsa face raini
har tazo taza wuce zeenah ta ce"Hmmm,haka dai aka iya kullum ci Wallahi da nice ke da tuni na jima da barin gidan nan tunda na ƙasa ba mijina Abinda yake so miji baya ta taka amman ka nace ko dan ba laifin ki bane ki na tsoron komawa cikin tuwo da miyar kuka da aka baro"
iman ta yi gaba ba tare da ta kula ta
"juya kawai"
kamar Daga sama iman taji zeenah ta kirata da juya duk har ranta taji zafin Maganar amman ta shanye
Karo na farko idanunta suka sauka cikin na Zeenah
murmushi tayi mai ciwo ta ce"ni bazan kula mutun marar tarbiya irin ki ba zeenah"
dandan nan fauskar zeenah ta chanza
iman ta nuna kanta ta ce"Ni Allah bai bani haihu Amman ya bani tarbiyya"
ta nuna zeenah ta ce"ke kuma sai ya baki cikin da kike taƙama dashi kuma ya hanaki tarbiyya iya zama da mutane"
a fusace zeenah ta ce"mi kike nufi"
Iman ta ce"Mutum mai tarbiyya ba ya shiga gidan wani yana neman ya raba shi da matarsa"
“Mutum mai tarbiyya ba ya yiwa mutane gori da abin da ba ita ta halitta kanta da shi ba"
“Mutum mai tarbiyya ya san cewa haihuwa Allah ke bayarwa"
Ta ɗan yi shiru
Sannan ta ce cikin ƙarfi murya ta ce"tarbiyya iyayen ke badawa amman saida kash banga Alamar sun baki ba,ko da sun baki batayi aiki akan ki"
zeenah ta zaro idanun
"Ke yar talaka ce, ko za'a hada Ku duka danginku ba za ku kai matsayin iyayena ba, Mutun cin mahaifina yafi kam matsiyata irinku kina da bakin magana"
"Arziki daga Allah yake, tarbiyya kuma daga iyaye Na fi alfahari da tarbiyyata fiye da dukiyar da zasu mallaka"
iman ta ce"niko nake da bakin magana Saboda kin tsallake iyaka"
"ki jini kuma ki sani ba tsoranki nake ji ba"
"duk abinda,kike min a baya ina shanyewa bana kulaki saboda kwanciyar hankali mijin mu,amman ki sani tura ta kai bango anzo gaɓar da bazan iya jura rashin hankalin ki ba"
"Ba kuma zan ƙara bari ki raina ni ba"
“Idan kina son zaman lafiya, ki bar ni da mutuncina"
“Idan kuma kina son tashin hankali…”
Ta kalli Zeenah ido cikin ido
“To ki sani ni ba yarinyar da za ki ci zarafinta ba ce ta kyaleki tunda naga alamar duk kara da nake miki baki gani ba shasha kawai wanda har yanzu hankali bai gama ratsa ki ba"
Zeenah ta ɗaga hannu cikin fushi zata mare ta
dai-dai lokacin Suhail na shigo wa
"zeenah" ya kira sunan ta da karfi
iman ta kama hannun ta da karfi ta wurga
ta nuna ta da yatsa"wannan shine babban kuskuren da zaki aikata duk Ranar da wannan kazamin hannun naki yayi ƙoƙarin rabar jikina a Ranar zaki ga real color din na"
"Ki gyara halayenki kafin ki zo kina raina mutane"
ko ta kan tea da egg din bata bi ba ta koma daki
“Suhail ya tsaya cak Karon farko tun da ya auri Iman, ya ga wannan ɓangaren nata Ba iya fushin ya ba shi mamaki ba… sai yadda ta kare mutuncinta cikin ƙarfin hali "
Suhail ya nuna zeenah da yatsa ya ce"kinga Abinda kika jawa kanki ko,tun Yarinyar tana baki girman ki har ta daina"
zeenah ta ce"haka ma zaka ce"
Suhail ya ce"ai iya gaskiyar kenan"
kwafa tayi ta shige daki
Mutanen iman fa anyi baki🥺🤪
da alama fa kamar aikin malan na soro ya fara karyewa wallahi da kyar nake muku typing🥱😭
dan Allah ku kara komawa wajen wani
Comment ɗinku zai nuna min ko Iman ta yi daidai ko kuma ta yi tsauri😂❤️”
share
like
and comment