BARRISTER SUHAIL

77

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️—–77

Suhail ya jima a tsaye

Ba maganar da Iman ta yi ce ke ba shi mamaki ba

Ta wani ɓangaren ma, abin da ta yi ya burge shi

A karon farko ya ga ta tsaya ta kare mutuncinta da kanta 

Sai dai abin da ya fi tsaya masa a rai 

Shi ne irin ciwon da ya gani a cikin idanunta

Ya san ba fushin fadan da sukayi da Zeenah kaɗai ne ke damunta ba

Akwai wani rauni da ya fi zurfi da yake hango wa a fuskar ta

Wani rauni ne ke damunta

A hankali ya nufi ƙofar ɗakinta

Ya ɗaga hannu zai yi knocking

Sai kuma ya sauke shi

Ya san idan ya matsa mata yanzu

Ba zai samu komai ba a Wajen ta ba 

Ya juya cikin sanyin jiki ya nufi ɗakinsa

A ɗaya ɓangaren kuwa

Iman na shiga ɗaki ta kulle ƙofa

ƙarfinta ya ƙare wani irin jiri ke dibar ta

Ta zube a bakin gado

Kukan da ta hana kanta yi a gaban Zeenah

Shi ne ya samu damar fita

Ta rungume filo tana kuka mai ciwo da tsuma zuciya

Ba don maganar talauci ba da Zeenah ta alaƙan tata dashi ba

Ba don gorin cikin datayi mata ba

Sai don yadda kalaman Zeenah suka dawo mata da duk abubuwan da take ƙoƙarin mantawa

“Ba ki ba mijinki abin da yake so…”

“Da ni ce ke, da na bar gidan nan…”

jin kalaman take tamkar Yanzu ake furta mata su

Ta dafe ƙirjinta

Wani irin zafi take ji kamar ana murɗa zuciyarta

A hankali ta furta

“Ya salam"

“ya Allah Ka bani ƙarfin jurewa"

“Idan wannan ƙaddarata ce"

“Ka sa ƙarshen ta ya zama mafi alkhairi a gare ni"

Hawaye suka ci gaba da gangaro mata

Ta runtse idanunta

A yau

Ba wai tana jin zafin abin da Zeenah ta faɗa kaɗai bane 

Ta fi jin zafin cewa

Ta fara yarda da waɗannan kalaman a cikin zuciyarta cewa ita juya ce wacece bata haihuwa

Suhail na dawowa daga sallar la'asar ya nufi dakin zeenah 

tana zaune a falo tana kallo tana cin soyayyen kwan da jennifer ta kawo mata 

da ganin Suhail ta soma gyara zaman rigar dake jikin ta 

tana murmushi shiko babu alamun walwala a fuskar sa 

ya ƙarasa gaban ta 

"zeenah nazo nayi maki gargadi this should be the first and the last warning da zan maki akan iman"

"ki fita harkar iman"

"kinga Abinda ya faru yau ki sani wata rana Abinda yafi haka zai faru matukar baki ƙiyaye ba"

tunda ya soma Magana ta dukar da kanta

Ba ta ko kuskura ta ɗago ta kalli fuskarsa ba

Suhail ya ci gaba da cewa,

“Na yi shiru a baya saboda bana son tashin hankali"

“Amma hakan ba yana nufin bana ganin abin da yake faruwa ba ne"

"kinyi mata gori,kici mutunci iyayen ta how do you think zata kyaleki har kina ƙoƙarin marin ta"

"a tunanin ki idan kin mareta bazata rama bane"

ganin bata da wani zabi daya wuci bada haƙuri dan Suhail a fusace yake ta riga ta sani ta rasa Suhail 

ta hadiƴe yawu da kyar

"kayi haƙuri Suhail abu makamancin haka ba zai sake faruwa ba"

"bani zanyi haƙuri ba zeenah kece zaki gyara halayen ki"

"ki daina shiga rayuwar iman"

"idan zakiyi mata magana fine idan ma bazakiyi mata ba kowa yayi harkar gaban sa"

"nagaji da tashin hankali da ake a gida na"

Shiru ya mamaye falon.

Zeenah ta ji zuciyarta na tafarfasa

Amma ta kasa cewa komai

Ta san wannan karon

Suhail ba wasa yake yi ba 

watannin suka ja a hankali a cikin watanni rayuwar gidan Suhail ta chanza,iman ta cigaba da kare kanta bata shiga harkar kowa a gidan duk da haka ba ta taɓa hana Suhail haƙƙinsa na aure ba Suhail kullum cikin nemo hanyar da zai dawo da murmushin yake,Amman abin ya gagara zeenah kuwa tun bayan kashen da Suhail yayi mata ta rage shiga harkar iman ,sai dai ƙiyayyar dake Zuciyar ta baza ta ragu ba

7 months later 

tuni zeenah ta shiga watan haihuwar ta  

kullum cikin siyayyar kayan haihuwa suke 

Ba ƙaramin kashe kuɗi Suhail yake yi ba wajen shirye-shiryen tarbar jaririn


babu abinda basu saya ba na tarbar jaririn kamar yadda aka sanar da zeenah tun a  awo namiji zata haifa

Duk lokacin da Suhail da Zeenah suka dawo daga siyayya, Jennifer da ma’aikata kan shiga da kwalayen kayan jariri cikin gida Iman kuwa idan ta ga haka, sai ta yi shiru ta koma ɗakinta Ba don tana yi wa Zeenah hassada ba…sai don duk wani ƙaramin kaya na jaririn yana tuna mata da burin da take da shi shekaru da dama a rayuwar ta 

yau ta kama labara tun daren jiya zeenah ke fada wani matsanan cin ciwon ciki 

har yau da ko motsa wa daga kan gado batayi ba 

jennifer ce ta shigo dakin riƙe da breakfast ganin zeenah a wannan yanayin ya tabbatar da tana labour 

ta saka hannun ta gaba ɗaya ta riƙe cikin ga wani kara da take yi lokaci zuwa lokaci

jennifer batayi wata-wata na ta nufi dakim Suhail tsaye yake a bakin mirror yana gyara zaman rigarsa

knocking tayi ya buɗe kofar 

cike da ruɗewa ta ce"Sir Hajiya is in labour"

da jin haka Suhail bai tsaya tambaya ba ya dauko key din motar sa 

tare suka koma dakin zeenah a lokacin tana a yadda jennifer ta barta 

Suhail ya ce ta chanza Mata rigar Bacci dake jikin ta ta saka mata  wata 

da taimakon shi suka fito da ita 

hayaniyar da suke ta farkar da iman daga baccin safen data koma

Ta hango Jennifer da Suhail suna riƙe da  Zeenah

Numfashi ta sauke
Ta fahimci abin da ke faruwa

a zuciyar ta take addu'a Allah ya sauke ta lafiya 

Bayan an saka Zeenah a mota…
Suhail ya ja motar cikin gaggawa suka nufi asibitin da zeenah ke awo

Da isarsu Asibitin 

Likitoci suka karɓi Zeenah cikin gaggawa

Aka shigar da ita ɗakin haihuwa

Suhail kuwa ya tsaya a corridor

Karo na farko cikin watanni ya kasa zama wuri ɗaya

Sai kai-komo yake yi

Lokaci-lokaci yana kallon ƙofar ɗakin

Yana addu’a "Allah ya sauki zeenah Lafiya"

tausayin ne fal a zuciyar sa ko ba'a fada ba kasan she is in pain duk da tana da juriya 

zeenah bata da raki

zeenah ta sha wahala sossai wajen haihuwar har likitici sun Fara tunanin yi mata Cs 

Bayan kusan awa ukku aka buɗe kofar dakin da zeenah ke ciki 


Likita ya fito yana murmushi

Suhail ya yi saurin ƙarasa
“Doctor ya jikin nata"

Likitan ya yi murmushi

“Congratulations Barrister Allah ya Azurtaku da da ɗa namiji"

Likitan ya ƙara da cewa

“Mother and baby are both fine"

Suhail ya lumshe idanunsa
Ya ɗaga hannayensa sama

yana godiya ga Allah 


Bayan wasu mintuna…

Aka ba shi izinin shiga ciki

Ya tarar da Zeenah kwance a gado

Jaririn yana gefenta cikin gadon yara 

jaririn fari tas an naɗe shi cikin  wami blue blanket na yan gayu a hankali ya sa hannun ya dauko sa babu Abinda yaron ya manto a kamanin zeenah Idanun sa ne kawai suka yi kama dana Suhail

Suhail ya matso a hankali
Ya kalli jaririn

A hankali ya shafa kansa yana murmushi 

“Alhamdulillah" ya furta

ya juya wajen zeenah ya ce"sannu zeenah ya jikin ki" 

"Alhamdullilah babe"

Mutun na farko da Suhail ya fara sanarwar haihuwar shine malan Wato mahaifin iman 

cikin farin ciki malan ya ce"Masha Allah,Allah ya raya cikin addinin musulunci"

addu'o'i sosai malan ya musu

bayan ya kashe wayar ya kira Abba ya sanar masa 

har iman da tun dazu take kiransa tana so taji lafiyar zeenah itama ya faɗa mata ta haihu an sami baby boy

a iya wayar ma kadai zaka san yadda take farin cikin samun karuwar da Suhail yayi 

ta masa addu'ar"Allah ya raya ya ba Zeenah lafiyar shayarwa"

Mami koda ya faɗa mata ,wani irin farin ciki ya lulluɓe ta duk da ciwon da take fama dashi a ƙafa hakan bai hanata miƙe wa zaune ta nuna farin cikin taba 

tana jin kaunar zeenah na ƙaruwa cikin zuciyarta ta tare da jinjirin data haifa

badon dan wai shine jiƙa na Farko da aka haifar mata ba sai dan Suhail ne ya haifesa

wuni guda suka yi a Asibitin bayan an tabbatar da zeenah da yaron suna cikin koshin lafiya

suka kama Hanyar gida jennifer na riƙe da jaririn a hannu

Bayan fitowarsu daga asibitin…

Kai tsaye gida suka nufa

Motar na shiga harabar gidan, Jennifer ta fara fitowa riƙe da jaririn

zeenah ma a hankali ta ke sauko daga cikin motar suka nufi ciki 

dakin ta suka nufa Suhail ya amshi jaririn daga hannun jennifer ya ce"kije ki kula da Zeenah"

dakin iman ya nufa tana zaune bakin gado tun tafiyar su ta rasa sukuni

Suhail ya shiga fuskar sa dauke da murmushi

ya ƙarasa bakin gadon yana miƙa mata jariri

da kamar bazata amshe saba 

Idanunta sun nuna alamun kuka

Amma duk da haka…

Ta yi ƙoƙarin ƙirƙiro murmushi

Cikin rawar hannu ta karɓi jaririn

ta rungume shi 

"yaya Suhail the baby so cute"

murmushi yayi ya ce"like you"

Sai ta ji tamkar wani ɓangaren zuciyarta da ya daɗe babu rai ya fara motsawa.

Jaririn ya buɗe idanunsa a hankali yana kallon ta 

Idanunsa masu kama da na Suhail suka tsaya a kanta

Ba tare da ta shirya ba taji

Hawayenta suka gangaro

Sai dai wannan karon ba hawayen ƙiyayya ba ne

Ba hawayen hassada ba ne

Hawayen bege ne

Ta shafa lausan kumatunsa 

Cikin sanyin murya ta ce

“Masha Allah…”

“Allah ya raya ka"

Allah ya sa ka zama sanyin idanun iyayenka.”

Suhail ya tsaya yana kallonta

Kalaman addu’ar da take yi wa ɗan Zeenah suna ƙara tabbatar masa da irin tsarkin zuciyar Iman.

Ya san…

Da ace wata ce daban

Da ko kallon jaririn ba za ta yi ba

A hankali ya ce,

“Na kawo miki shi ne dan kiyi masa addu'ar ya zama hafizin Alqur'ani kamar ki dan Na san babu wanda zai fara yi masa addu’a daga zuciya kamar ke.”

Iman ta ɗago ta kalle shi

Sannan ta yi murmushi mai cike da hawaye 

"in sha Allah he will even be morethan me"

Ta sake kallon jaririn

Jaririn ya buɗe idanunsa a hankali,
 tamkar yana nazartar fuskar da ta rungume shi"

har ranta take jin kaunar sa

Wasu hawaye biyu suka sauka kan blue blanket ɗin da aka naɗe shi da shi

Suhail na lura da hakan

Zuciyarsa ta kasa jurewa wa
 
a wannan karin 

Ya fahimci cewa ba kowace hawaye ake iya gogewa da kalmomi ba

Wasu hawaye

Lokaci ne kaɗai yake iya busar da su

Ya miƙa hannu a hankali ya karɓi jaririn

Kafin ya fita dan bata daman fitar da Abinda ke zuciyar ta 

tamkar tana jiran fitar sa ta fashe da kuka addu'a take 

ta rungume pillon dake gefen ta

“Ya Allah…”

“Ko sau ɗaya ne a rayuwata…”

Ka bani damar rungumar ɗana kamar yadda na rungumi wannan jaririn

like
share 
and comment


tsabagen typing hannu na har zafi yake🤒🥺