BARRISTER SUHAIL

78

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

🅿️—78

Suhail na fita daga ɗakin Iman ya miƙa jaririn ga Jennifer sannan ya nufi ɗakinsa domin ya sauya kaya

Zeenah na fito daga wanka

Jennifer ta haɗa mata tea mai kauri kamar yadda likita ya umarta ta riƙa sha

Bayan ta gama shan tea ɗin
Ta shafa mai

Ta saka wata atamfa ɗinkin riga da siket mai kyau

Da wanda bai san ta ba ya ganta

Zai rantse ba ita ba ce ta haihu sa’o’i kaɗan da suka gabata ba


Jaririn da Jennifer ke riƙe da shi kuwa a falo

Ya fara tsotsar yatsansa

Alamar yunwa ce ƙarara

Da sauri Jennifer ta ɗauke shi ta nufi ɗakin Zeenah

A lokacin tana waya da mahaifiyarta

“…Eh Mommy, Alhamdullilah da sauki" shine Abinda ta fada da alamar barka ce take mata

Jennifer na tsaye a bakin ƙofa tana jira har ta gama wayar

ko da ta kashe wayar cikin girmamawa jennifer ta ce"

“Hajiya… Baby yana neman nono"

Zeenah ta ɗaga kai ta kalle ta

Ta sauke numfashi cikin gajiya

“Jennifer… bana ce ina son hutu wa ba?”

Jennifer ta sunkuyar da kai

“I’m sorry Hajiya… amma  zai fara kuka "

Ta miƙa mata jaririn

sai dai zeenah bata karɓe saba ta kalli Madarar,da ke kan dressing mirror

Ta ce

“Ba ga madarar da aka masa chanza da za'a basa"

Jennifer ta ɗan yi mamaki 

“Hajiya… amma likita ya ce ya fi kyau ki fara ba shi nono"

Zeenah ta ɗan haɗe Fuskar.

“Please Jennifer… bana son gardama kije kiyi Abinda nace maki"

“Idan ba za ki iya kula da shi yadda nake so ba"


“zan nemo masa nanny tun da wuri ta kula dashi"

Jennifer ta yi shiru 

Ta rungume jaririn da har ya soma kuka

A zuciyarta ta ce

“Allah Ya shirya zeenah"

mi amfanin ka haifi yaro kaƙi shayar dashi

jennifer ta kwashi formula din da abinda zata haɗa masa ta koma palor

ruwan zafi ta dauko ta haɗa masa ta zauna zata fara bashi kenan Suhail na fito daga ɗaki sanye dake da jallabiya ash color har ƙasa 

ganin abinda jennifer ke ƙoƙarin yi ya ƙara so da sauri ya kamshi abun feeding din 

"jennifer What are You try to do jaririn daga haihuwar  sa yau zaki fara bashi madara baki da hankali ne"

jikin ta har karkarwa yake ta ce"kayi haƙuri sir hajiya ce da kan ta ta ce na basa nayi kokarin fahimtar da ita this is not what he want tace naje na basa"

Suhail ya dauki jaririn dake kan cinyar ta ya nufi dakin zeenah 

ransa a bace tun daga Kofar dakin ya soma kiran sunan sunanta ta 

har ya ƙarasa cikin dakin

"zeenah dan Allah yaushe zakiyi hankali daga haihuwar yaron yau zaki sa a fara bashi formula"

"me kike a matsayin ki na mahaifiyar sa da bazaki bashi nono ba,ina ga tun dawowar mu daga asibiti baki bari yaron nan ya rabi jikin ki ba"

"me kike nufi idan har bazaki iya rainon saba zan dauka na ba iman tunda ita zata iya bashi kulawar da tafi taki"

Ko da ba za ta iya shayar da shi ba, na san ba za ta taɓa ƙin kula dashi ba

wani irin kallo tayi ma Suhail 
"ita ta haifar min yaron da zaka dauka ka kai mata ,ko ita tayi min wahalar cikin mi zai hana ita ta haifi nata sai ta kula dashi kuma nono ni gaskiya bazan iya bashi ba Gaskiya ina tsoron su fadi"

Suhail  ya tsaya cak A wannan karon Suhail ya tabbatar ba son jariri ne ya fi cika zuciyar Zeenah ba… son kanta ne 

ya lura faɗa bazai mata ba dole ya soma aikin lallashi da kyar ta Amince ta basa duk ba wata cikakkiyar shayarwa ya samu 

amman yaji dadin cikin sa dandanan bacin wahala yayi gaba dashi

Suhail ya amshe shi daga hannun ya kwantar dashi kan baby bed


Ya kalli jaririn cikin tausayi A ransa ya ce"daga zuwan shi duniya yau,ya soma shan wahalar da bai san dalilin taba"

Wataƙila wannan ce ƙaddarar da Allah Ya rubuta masa… ya fara fuskantar jarabawarsa tun ranar da ya zo duniya

Suhail bai samu damar zuwa jam'i ba hakan yasa ya koma dakin sa yayi sallar 

iman ce zaune kan Prayer mat ta gama sallah tana azkar din yamma kenan ta fita dakin zeenah danyi mata barka 

tasan war haka ta huta

sai tayi knocking aka bata izinin shiga

zeenah ma kwance kan gado tana dan na wayar iman ta shiga

cikin tafiyar ta mai kama da ta ƴan koya

bakin gadon ta zauna ta ce"sannu zeenah ya jikin"

"da sauki" ta faɗa a takaice

"Allah ya kara sauki ya raya shi"

zeenah ta ce"Amin idan da gaske kike,dan bazan taɓa yarda kina mana fatan Alkairi ba"

murmushi iman tayo ta miƙe zsta fita daidai lokacin Suhail na shigo daki
ba tare data kallesa tabi ta bayan sa ta wuce

shi kuma ya ƙarasa cikin dakin 

bayan ya zauna ya kalli zeenah ya ce"inaso zan saka masa sunan amman kafin nan ya kamata muyi shawara a matsayin ki na mahaifiyar sa na yanke shawara zan saka masa sunan Abba dan tun kafin a haifesa na zaba masa

Zeenah ta ajiye wayar ta dube sa ta ce"wani Abban"

Suhail ya ce"Akwia wani Abba daya wuce mahaifina"

zeenah ta ce"Abinda bazai yiyu bane,nima ai ina da mahaifin dan haka matukar bazaka saka sunan mahaifina na ba sai a saka masa wani sunan"

Suhail ya ce"badamuwa,i name him Ibrahim Khalil Allah ya raya"

zeenah ta ce"Hakan ya fi dai "

bayan kwana biyar da haihuwar khaleel 

Suhail bai koma aiki ba a waɗannan kwanakin, ya fi mayar da hankalinsa kan kula da Zeenah da Ibrahim Khalil

Abinda ya lura dashi 

Duk lokacin da jaririn ya yi kuka

Jennifer ce ke ɗaukarsa

Ko kuma shi da kansa

Zeenah kuwa

Sai idan ta ga dama take karɓarsa


A ranar da aka yi kwana shida da haihuwar Ibrahim Khalil, Mami ta haɗo kaya masu yawa ta aiko Naima da Meerah su kai wa Zeenah


Da misalin karfe goma ta faka a harabar gidan

Naima da meerah ke fito daga ciki tare da tullin kayan da suka zo dasu 

da makon driver da kuma jennifer suka shigar da kayan ciki 

akwatuna ukku ne Kowane shake fam da kayan

Daga baby clothes, diapers, baby blankets, towels, pampers, baby bath set, stroller, har zuwa kayan wasa na jariri

Ba wannan kaɗai ba

Akwai kuma manyan ledoji cike da atamfofi, laces, turare, takalma da sauran kayan jego da Mami ta aiko wa Zeenah

sai kayan suka kusa cika falon zeenah

koda Naima da meerah suka isa cikin

tun daga karar tarbar da zeenah tayi musu gwiwowin su suka yi sanyi

bayan sun gaishe sunyi mara barka naima ta ce"Mami ce tace akawo maki wannan kuma tanayi maki barka"

zeenah ta dan yatsine fuskar ta ce"an gode"

jennifer ta ƙaraso kusa da ita ta ce"Hajiya a shiga da kayan ciki"

zeenah ta ce"da alama kayan are not expensive so ki kaisu dakin ki already mun sayi duk wani abu da zamu yi amfani da shi"

Jennifer ta tsaya cak

Ta kalli Naima da Meerah, sannan ta kalli Zeenah.

Ta rasa abin cewa.

Naima ta yi murmushi mai ɗaci, sannan ta ce,

“Zeenah… Mami fa ce ta bada kayan nan.”

Zeenah ta ɗaga gira.

“And so? Kina nufin sai na shiga da su ɗakina ne saboda ita ce ta bayar?”

Shiru ya mamaye falon.

Jennifer ta sunkuyar da kai.

Meerah ma ta kasa cewa komai.


Naima ta lumshe idanunta.

A karon farko ta ji maganar Zeenah ta tsaya mata a rai

Allah kaɗai Ya san irin wahalar da Mami ta sha kafin ta haɗa waɗannan kaya

Amma ga shi…

Wadda aka kawo wa kayan ko godiya ba ta nuna ba.

A hankali Naima ta haɗiye abin da ke bakinta.

Ba ta so ta yi maganar da za ta ɓata al’amari

takun Suhail suka jiyo dake shigo wa 

idanunsa suka sauka kan naima da meerah 

“Kun iso kenan?”

Naima ta jinjina kai

Suhail ya lura da kayan dake jibge a falon

ya kalli Naima ya ce"wannan fa"

"mami ce ta bada a kawo"

Suhail ya ce"ita da bata da lafiya ai da bata wahalar da kanta ba, anjima zan kirata nayi mata godiya"

yana lura da mood din naima 

"Naima lafiya kuwa"

murmushi tayi ta ce"lafiya qlau yaya"

da kunya ta faɗa masa Abinda zeenah tayi musu

Zeenah kuwa ba ta ma sake kallonsu ba

Ta maida hankalinta kan wayarta tamkar babu kowa a falon

Suhail ya fita ya barsu

a falon babu mai cewa kowa komai bare su fara tunanin zasu sami Abinda zasu ci ko su sha

zeenah ta miƙe tsaye ta kalli jennifer dake packing kayan 

ta ce"idan sun gama zaman ki kaisu boys quarters"


share
like 
and comment